ABDUL JALAL 95

384 25 3
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 4️⃣2️⃣95

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

_MY FIRST NOVEL _

Cikide fusata Maama ke fadin

"ni zakayiwa haka? Ka watsamin kasa a ido, a kai kudin Auren yarinyar mugama gayawa duniya za'ayi biki sannan kazo min da wata maganar banza, wallahi baze yuwu ba Jawwad bashida matar data wuce Naja
Abba yace

"Shikenan tunda ke zaki daura masa auren ai seki aura masa Najar in gani"
Ya juya ze fice tace

"Kuma wallahi bazata bar gidan nan ba, in dai Naja zata bar gidan nan to Jalila ma seta bar gidan nan"

Cak Abba ya tsaya ya juyo yace
"gida nawane, duk wanda yake ciki a karkashin ikona yake, idan yarinyar nan ta kai magariba a gidan nan to Wallahi zaku tafi tarene, ta tattara tabarmin gida nagaya miki, Jalila nan gidan sune , nine mahaifin Jalila, Jalila bata da uwa ba uba seni, ita kuma wannan tanada iyaye dan haka ta koma gidansu, kowa ya zauna a gidansu" yana gama fadin haka ya juya ya fice.

Jawwad yana zuwa ya canza kaya, ya nufi gidansu Jalal amma yatarar baya nan, dan haka ya koma gida ya samu guri ya kwanta dan ya huta

A fusace Jalila ta kalli Jalal tace

"Wallahi bazani club ba, ka tsaya in sauka in yaso kaje inda yafi club be dameni ba"

Shiru yamata ya cigaba da tukinsa, yana satar kallon yadda ta rintse ido tana masifa, ganin yaki kulata yasa a fusace tace

"Magana fa nake maka, wai meye haka?"

Fitooo yafara yi mata yana murmushi, Jalila ta kai karshe a kuluwa, ya dan kalleta yace

"meye kuma na tashin hankali bafa cewa nayi zamuje Kisha giya ba rakiya kawai zakiyi insha mutafi"

Ta fuskanci so yake ya raina mata hankali, dan haka tayi shiru taga gudun ruwansa, ta dauke kanta zuwa ga kallon window tana share kwalla lokaci zuwa lokaci gani tayi tafiyar taki karewa dan haka takara fashewa da kuka me sauti Da sauri Jalal yace

"Ke meye haka kuma? Nifa ba Jawwad bane da zakimin shagwaba"

Ido duk hawaye tace "Eh aida Yaya Jawwad ne yasan inada test bazemin haka ba, kuma Allah ya kiyaye in maka shagwaba in maka shagwaba ince nayiwa wa?" tai maganar tana harararsa da kumburarrun idanunta
Dan hade rai yayi yacigaba da tukin ba tareda yace komai ba itakuma tana hawaye.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Où les histoires vivent. Découvrez maintenant