ABDUL JALAL (2020)

284 19 1
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

    _ABDUL  JALAL_
           (2020)

      _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
    (Daddy's girl)

               PAGE- 34

PART 1
Share please

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
ABDUL JALAL NOVEL FANS
Love u all guys ❤❤❤❤❤

          -MY FIRST NOVEL-

Ja da baya ta dingayi yana Binta, har seda ta kai karshen bango sannan ta tsaya tana zazzare ido
"Kingama gudun?"
Saboda karfin hali irin na Jalila ta dubeshi
"Wallahi kasake ka karaso inda nake sena maka Illa, akan me baza a fadi gaskiya ba, ai duk abunda nake fada ba karya nayimaka ba haka kake"
Daka mata tsawa yayi, Wanda yasa taji hanjin cikinta sun nannade guri daya
"Shut up, akwai wata illa dazakiyimn Wanda yafi miyagun maganganun da kikeyimin, ke badan darajar Jawwad ba da tuni na dade da kakkaryaki na karya banza"
Dagowa Jalila tayi da sauri ta kalleshi,
"Eh in karya banza mana, in ban mantaba a wancan karon nagaya miki ba ruwanki dani kifita a sabgata kome nake aikatawa babu ruwanki, meyasa kike da taurin kai da shishshigi,?
Dakamata tsawa ya kumayi ba tambayarki nakeba
Banza tai masa ta dauke kanta
" kaga ni ban guri in wuce"
Ba musu yabata hanya, ta sa kai zata wuce cikin zafin nama yasa hannunsa yakamo hannunta guda daya, yai masa wata muguwar murdawa, Wanda in yakuma murdawa ze iya ballata
Bata San lokacin datayi wani uban zilloba ta fasa kara
Ya kalleta "da zafine?"
Kasa magana tayi se wani uban fitsari dataji ya matsota, gashi ko kwakwakwaran motsi takasa balle ta kwace hannunta
Be saketa ba, da daya hannun nasa yasaka yakamo kunnenta, cike da mugunta ya murda iya karfinsa, wannan karon batayi ihunba sedai taji kaman fitsarin yafara fitowa, Allah ya temaketa hawaye yafara zubowa daga idonta, yana daf da ita sosai Dan suna iya jin numfashin juna, ya Dan tsura mata ido sannan yace
"Nikike cewa makakke ko? Kuma Useless and hopeless creature ko, ke gaki wadda ta haifowa duniya rashin kunya, daga yau in kinga Jalal, kikuma kallon ko inda nake sena yi maganinki
Hada cewa kinfi karfin makakke irina, ke meye abunso a gurinki,, yana ina wata mummuna dake, banda rashin mutunci da rashin kunya  baki iya komaiba"
Motsa baki take, tanaso tayi magana amma takasa
Har yanzu be saketa ba, yadan kalleta
"Ko kinada maganane"?
Girgiza kai tayi, fuskarta tayi jajawur, se ruwan hawaye dayake zuba wani nabin wani,"
Da kyar ta tattaro kalaman dazata fada
"N..Ni kasakeni, zan karye fa"
Yadda tayi maganar cikin kuka da kuma shagwaba, seyaji jikinsa yayi wani iri
"Au bakinki be mutu bako" yafara a hankali
Yasa kafarsa ya take mata yatsun kafarta
"Wayyo Allah Ummi, ze kasheni, Allah ka temakeni"
Yadda taketa kuka gwanin ban tausayi, Dan zuwa yanzu ji take kamar hannunta ya karye, sannan ta saddakar ya cire mata kunne, ga yatsun kafafuwanta dake wani zugi, kunenta yafara saki sannan yacika mata hannunta
Daya hannun tasaka ta rike hannun dayayiwa muguntar danji take kamar ya karye,
Dan kallonta yayi kamar yayi dariya amma ya dake
"Gobema kikuma sena tabbatar miki ni makakke ne, da giya naso nabaki kisha senaga bake yakamata in bawaba Jawwad zan bawa, in yasha kaman kinsha ne, stupid girl, tafi kibani guri"
Dukda haka be ishi Jalal ba Dan Sam be huce ba akan abubuwan data keyi masa, seda yamata kyakyawan rankwashi a tsakiyar kanta, aikuwa nan take ta tsuguna kasa ta fashe da kuka,
Shikuma yakoma kan kujerar da yataso yai zamansa yacigaba da abunda yake,
Kuka take sosai saboda batason atabamata kai ko kitso bata sonyi setace zafi yake mata, balle wannan katon ya rankwasheta, kuka take sosai hada sheshsheka
"Idan baki tashi kinbar dakin nan ba nazo gurin nan, sena danneki na baki giya, and I mean it"
Bashiri ta mike ta nufi hanyar fita, tana Jan kafa seda ta bude kofar, ta waigo ta kalleshi,
"Allah yasakamin wallahi, mugu kawai, kuma wallahi niba mummuna baceba,"
Shiru yayi mata, "bazata iya yin shiruba, bakinta baze mutu ba"
Tsayawa tayi ta share hawayenta daga waje Dan gujewa tambayoyim Nana, tana daf da shiga cikin gida Jawwad suka karaso shida doctor salis
"Munzo a dai² Jawwad waccan ba mutuniyar bace?"
Doctor salis yai maganar yana nunawa Jawwad Jalila"
Banza Jawwad yai masa yanemi guri yayi parking, Jalila tana kallonsu amma bata tsayaba tayi cikin gida, Allah ya temaketa bakowa a parlour tashiga dakinsu ta tarar halima tana ninkewa Nana kayan sawarta
"Halima ina Nana"?
" hajiyace ta kirata,afiya kuwa"
"Lafiya kalau"
Jalila ta shige toilet Dan kar halima ta dameta kunnenta yayi Ja ga hannunta da ya sage ji take kamar banata ba
Gaskiya Jalal azzalumine, ya iya salon mugunta, babban abunda ya dameta wannan rankwashi da yayi mata Dan tunda yayi mata take jin Jiri har yanzu, kanta har yafara ciwo, lallabawa tayi ta watsa ruwa, ta wanke fuskarta tayi alwala Dan magariba ta gabato sannan ta fito ta canza kaya, bata iya amfani sosai da hannun da Jalal ya murda mata, guri daya takoma ta dunkule lokaci² tana share hawaye
Nana tazo ta sameta a haka
"Lafiya kuwa?, daga zuwa duba Yaya Jawwad kinzauna"
"Naje baya nan yanzun nan ya dawo"
Jalila tabata amsa a takaice
"Wai meya sameki naga yanayinki ya canza?"
"Kainane yake ciwo"
"Eyyah sannu inada paracetamol inkinyi salla seki sha"
Jalila ta gyada mata kai, Nana kuma tayi waje
"Azzalumin banza wainice mummuna makaryaci kawai, wallahi ko makaho yasan niba mummuna bace"
Jalila taita mita tana kunkuni,

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now