ABDUL JALAL 60

394 21 4
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE7️⃣ 60_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

_MY FIRST NOVEL _

Jalila da kyar take fizgo numfashi, nufota Jalal yacigaba dayi, yana zuwa seya wuceta yatafi gurin socket dake kusa da Tv yanata shan tabarsa, yaje yasaka wayarsa a caji, Jalila kuwa se binsa take da kallo, yagama sa cajin ya taso yakuma dawowa harya wuceta ya dawo ya zauna a gabanta ya kura mata ido, dauke nata idon tayi,

"naga kina son kallona ne shiyasa na zauna kigama karemin kallo" ya faɗa tareda busamata hayakin sigari a fuskarta, da sauri ta dago tareda toshe hanci, ta dan fara tari,

Cikin tsiwa tace

"wai meye haka, Allah ya sawwake inzauna ina kallonka, kato da kai kazomana gida ma tube sekace dakinka"

"dakin Jawwad dakina ne, dan haka ko tsirara naga dama zanyi yawo"

yunkurawa tayi zata mike, yasa hannu ya janyo ta ya maida ita kan kujerar ya kafeta da ido, yasa kafarsa daya a gefenta, ta kalli inda yasa kafarsa aranta tace kalli jikinsa duk gashi kaman wani dan biri, lighter ya jefomata yasa wata sigari a bakinsa, yaimata alama ta kunna masa, wani mugun kallo tayi masa ta dauke kanta

"Allah ya kiyaye ya rufamin asiri, nikabani hanya in wuce, kalleka dan Allah"

hannunta daya yakama cikin mugunta ya murde mata yatsu, ihu tayi saboda zafi, take tafara zufa cikin tsawa yace

"Kunnamin ko tarihi ya maimaita kansa, inkuma duramiki sigari yanzun nan"
jiki na bari ta kunna lighter ta mika hannunta ta kunna masa,

"dan Allah ka sakarmin hannuna, yatsuna zasu cire"

a hankali yasakar mata hannu, idonta har yayi ja, yacigaba da busa mata hayaki, gashi ya tareta da kafa bazata iya guduwa ba, hannu ta kai zata toshe hancinta, "wallahi kika toshe hancinki sena wanka miki mari, sena baki mamaki da hannunki zaki shata"

bashiri ta ajiye hannunta yana busa mata hayaki, se tari takeyi tana dauke numfashi

"gaskiya Jalal dan iskane bashida mutunci, yanzu inna matsa da rashin kunya ze iyayimin akuya" seda ya shanye tabarsa tsaf sannan yadubeta yace

"nine Namiji mara daraja ko? Ni Jalal nikike zagi ko?"

shiru tayi tana kallonsa, daka mata tsawa yayi

"ba dake nake ba kike wani kallona mara kunya" cikin dakewa tace

"karya nayi, aiba karyanayi ba namiji me daraja baze abunda kake ba"

"hakane Amma kin bar kari tun ran tubani, kinyi sake namiji mara daraja yamiki Illa, wadda bazaki ganetaba a yanzu, idonki kawai ya nuna a tsorace kike kar in miki wani abu, ba abunda zan miki a yanzu, amma kisani bana yafiya, bana mantuwa, sena hukunta ki akan cin mutuncin dakikemin bazan kyaleki ba, sena gwada miki abunda nakeji idan kika ci zarafina, kidena shishshigi akan abunda baki saniba" Yayi ajiyar zuciya

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now