ABDUL JALAL 68

332 23 3
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 1️⃣5️⃣ 68_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com


_MY FIRST NOVEL _

A razane Ilham ta cewa Jalila

" Ubanwa ya gayamiki wani abu na zuba a ciki? ke bayan munafunci hada sharri a lamarin naki, ai na dade da gano sonshi kikeyi, kalleki a haka kaman ta Allah amma tsabar rashin tsoron Allah da idona na ganki kina rungume Jalal, se anyi magana kice aike basanshi kike ba, in ba sonshi kike ba uban me ya kaiki jikinsa, meye naki nasamun ido iyee? munafuka kawai"

Jalila tai murmushi tace
"inkika daga murya kanki zaki tonawa Asiri baniba, danni ba ruwana, sannan dan na rungume Jalal, damace nasamu kema kije ya rungumeki mana in kin cika mace" Jalila takarasa maganar tana dariya, tacigaba da cewa

"Ilham tsabar mugun abunkine yasa kullum idonki yake ganemiki abunda ze hanaki sukuni tsakanina da dan uwanki, amma ko makamancin so na wancan abun babu araina fatan kin gane, for now Jalal beci wannan tsafin ba sekije kiyi wani shirin kuma" tana gama fadin haka bata jira me Ilham zatace ba ta juya zata fita, Ilham tasa hannu ta janyota, ta waigo sukayi ido hudu, Ilham kaman ta fashe da kuka tace

"wannan karon kinyi Nasara, amma ki saurari abunda ze biyo baya nan gaba"
"Idan har Allah shine abun dogaron mutum to a koda yaushe nasara tasace, dan haka inaji ranki, sannan kisani bani kadai yakamata kiga baya ba, Hanna ma tana nan tana target akanki, sekin kara tunani kin rarraba hankalinki, dan hanna bazata barki ba,"

Jalila ta fizge hannunta tai gaba abunta. Ilham taji wasu hawaye na bacin rai suna bin idonta Allah yahadata da Jaraba, mezatayiwa Jalila ta huce ne? Gani take da za'abata wuka seta kasheta, ita hannah ba barazanace a gurinta ba Jalila tafi tsayamata a rai, da Jalal yaci abun nan da yanzu anmawo karshen komai, amma Jalila ta wargaza komai, ajiyar zuciya Ilham tayi

"dole in sanar da umma abunda ke faruwa, na dauka zan iya shawo kan lamarin nan amma abun yafi karfina"

Jalila kam takuma silalewa ta fice ba tareda kowa ya ganta ba ta tafi gida. Koda Jalila takoma gida, sabgoginta ta shigayi, amma takan tuna nasihar da Jalal yaimata dazu, babban abunda yabata mamaki yace jikinsa yana bashi ummi tana raye fatanta Allah yasa hakane ummi tana raye, har akayi sallar isha'i sannan Nana ta dawo gida, da fara'arta ta tafi gurin Jalila ta zauna, Jalila ta kalleta

"se yanzu kika dawoko? Dan kinga Abba bayanan"

"Aiko yana nan baze hananiba, Allah sarki Yaya Jalal se murna yake yaga yan uwansa"
"Hmm Nana ai dan uwa dadi ne dashi, sedai abun tausayin naga yan uwannasa duk nutsatsu amma banda shi"
"ya akayi kika gansu bayan kina gida?"

"naje naga palourn a cike bazan iya wucewa ba dan haka na dawo"

Nana ta dan girgigiza kai

"bari kawai Jalila, Jalal abun tausayi ne, Allah ya kyauta kawai" daga nan Nana bata kuma cewa komai ba ta tashi, ta bar dakin.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now