ABDUL JALAL (2020)

288 24 0
                                    

    _ABDUL  JALAL_
           (2020)

      _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
    (Daddy's girl)

               PAGE-  12

PART 1

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Is a free book

Ina yinku AbdulJalal novel fans irin💯💯💯 da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all ❤❤❤

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢
Your comments give me courage

    Takabbalallahu minna wa minkum eid el Mubarak alaina wa alaikum
Allah ya karbi ibadunmu yasamu a Wanda yYafewa a wannan kwanaki goma na dhul hajj

         -my first Novel-

Numfasawa yayi ganin yadda yaran gaba daya suke durkushe a gabansa ga maryam da take ta kuka

Ko ba komai Aliyu yaron kirki ne tun tasowarsa ba taba dakko masa magana ba dukda fadansa da shige shigensa baya dakko magana
Kuma ya duba misalin da inna mairo tai masa Suma yadda sukazo basu San kowa ba malam shehu ya daukesu kaman yayansa Dan haka ya numfasa

"To shikenan na amince Allah ya tabbatar mana da Alkhairi yayi muku albarka gaba daya"
Marry ta dago da sauri

"Baba dagaske ka yadda in auri Aliyu"

Ya gyada mata kai
Da gudu marry ta tafi gurin Inna mairo ta rungume ta

"Mama bani da bakin godiya mama kiyimin godiaya gurin baba, kun gama min komai a rayuwa da kuka karbeni nagode sosai.

" ba komai maryam nima nayi diya dama bani da ya mace"
Inna mairo tayi maganar tana sharewa marry hawaye

Aliyu da Dan uwansa haka suka dinga yiwa mahaifinsu godiya tare da adduo'i
Usman yaji dadin yadda baba ya amince ko ba komai shima Dan uwansa ya samu farin ciki

Bayan malam imam ya koma daki ya kira Aliyu yayi masa nasiha  ya ja kunnensa game da rike amana da yi masa gargadin zama jakada nagari na addinin musulinci da kuma kabilar hausawa
   Haka marry ta karbi musulinci  ta koma maryam Amma aliyu yake kiranta da noorat saboda sunan mahaifiyarsa ne
Abubuwa sunzo mata da sauki saboda tasan addinnin musulinci se Dan abinda ba a rasa ba.
Itakuwa Maman Jawwad tunda taga abunda yafaru gashi kuma mutanen gidan sun karbi maryam.ta fara jin haushi, yadda inna mairo take kula da maryam kamar yarta amma ita dasukayi kusan shekara shida da ita bata wani shiga sabgarta,
Dan haka ta shiga yayatawa a anguwa kanin mijinta Aliyu ze auri kirista dukda tasan ta musulinta, hakanan se yan unguwa su shigo dan aga matar da Aliyu ze aura.

Duk surutun da ake a gari Aliyu da yan gidansu suka toshe kunnensu, dama ba a tunkarar Aliyu da maganar Dan ansan masifaffe ne
Sedai ayiwa Usman ko magulmata in sun shigo suyiwa inna mairo
Aka ware musu bangarensu a cikin gidan, dukda kasancewar maryam kabila kuma wadda tayi girma a gidan sarauta amma tana da matukar biyayya da girmama manya ba ruwanta da hayaniya, mamansu Aliyu ana kiranta inna mairo amma ita se dai tace mata mama

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now