ABDUL JALAL (2020) 10

338 26 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_
(2020)

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 10

PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Is a free book

Ina yinku AbdulJalal novel fans irin💯💯💯 da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all ❤❤❤

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢
Your comments give me courage

Haka suka cigaba da tafiya sunayi suna hira jefi² har suka shiga garin Kaduna
Karfe 4 dai² suka iso kofar gidan su Jalila, suna parking Jalila ta fito bata tsaya bi takan JAWWAD ba balle trolley dinta, ta sakko ta ruga da gudu cikin Gida,
Ummi tana tsakar gida ta idar da salla Jalila ta shigo da gudu ta fada jikinta tana murna
"I really miss you ummina"

"To karyani ki huta sarkin fitina ga yanda kika shigo da gudu kaman an koroki,"

"Bikiyi missing dina ba ko ni duk na damu saboda rashinki a kusa dani amma daga zuwana kin faramin fada"
Ana haka JAWWAD ya shigo da trolley din Jalila,

"Au shi kikabari da dakon kayannaki? Kekam se a hankali"
Ummi tafada tana ture Jalila daga Jikinta

"Ba komai Ummi naga ta kagu ta ganki ne yasa ta manta da trolley"
Yafada yana murmushi

Murmushi Ummi tayi
Har kasa ya tsuguna ya gaida Ummi ya zauna
Ta amsa fuskata cike da fara'a haka ya zauna sukayi ta hira da ummi,
Ummi tana kaunar Jalal kodan yadda yake son diyarta dakuma yadda mahaifinsa yake tsaye akan lamuransu ita da yarta
Bayan haka kuma JAWWAD yarone me matukar biyayya da hakuri

Sallar la'asar yayi, be wani dade ba yace tafiya zeyi,
"Jawwad tun yanzu"
"Ummi bana son tafiyar dare ne"
"Hakane kam bata da dadi"

To Dan jirani ina zuwa daki ta shiga ta dakko wani turare me kyau tabawa JAWWAD yayi godiya sosai

Yayiwa Jalila alama da ido ta tashi tarakoshi waje
"Sisyna zanyi missing dinki zuwan nan naki yayi min dadi gashi kin dawo kin barmu"

"Allah sarki yayana nima banji dadin rabuwa daku ba "

"Sisyna kiyi karatu kinji nasan ke mutuniyar kirki ce, banda kula kawayen dabasu zuwa makaranta
Banda tsokana da shagwaba"
Ya karasa maganar da sigar tsokana

"Insha Allah yayana"
"Good very good sister, insha Allah very soon zan dawo mukoma"
Dan turo baki tayi batace komai ba

Mortar ya bude ya dakko wani jaka yabawa Jalila
"Thank u very much my brother"
"Shhhhh don't mentioned dear"

"Wish u safe trip brother thank u very much ka gaida min da Nana ta"
"Zan gayamata and karki manta dayiwa yayanki addu a"

"Addu a mekakeso in maka"?
"No bani ba Jalila yayanki Jalal"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now