ABDUL JALAL (2020)

349 18 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

    _ABDUL  JALAL_

      _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
    (Daddy's girl)

               PAGE-  6

PART 1

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

I want comments not stickers😢😢😢😢
Comments dinku  shine kwarin gwiwata

       _My first novel_

"Gobe ma in kikaga Jalal kikuma zaginsa useless creature kawai"

Yayi tafiyarsa ya barta a gurin tana ta mimmikewa tana fama da numfashi ta galabaita har a tafara fita hayyacinta.

  Mummy ce tafito daga sashen daddy zata shiga kitchen ta dinga jin kakari da nishi, dawowa tayi da baya a Dan tsorace, tana duba meke wannan nishin,
Jalila tagani a zube a gurin tafita hayyacinta numfashinta nata fita da sauri

(Lallai JALILA ta sha hayaki)

" subhanallah ke Jalila meyafaru meke damunki??"
Tazo tana taba ta
"Ohh ni khadija meke damun ta kodama tanada athma ne

" Ilham!,  Ilham!!,  Ilham!!!,"

Tashiga kwala mata kira

"Ke Ilham kifito da sauri"

    Itakam Nana gajiya tayi da jiran Jalila Dan haka kawai tayi tafiyarta ta shige Gida,kai tsaye taje dakin mummy
"Mummy mun dawo "
"To sannunku ina Jalilan?"
"Wayarta ta manta ta koma dakkowa shine na taho"

Kai inkuma Yaya Jalal ne yamata wani abunfa tai wannan tunanin a ranta
da sauri tafito ta nufi gidansu Jalal

   Shikuwa Jalal gurin Jawwad yatafi abunsa, kaman be aikata komai ba hankalinsa kwance
Amma lokaci2 in ya tuna maganganun Jalila se ransa yabaci .

Da gudu Ilham tafito
"Mummy lafiya kuwa?

" zo kiga Ilham dama tanada asthma ne ko wani cutan?"
Ilham ta Dan zaro ido

"Mummy ya za ayi in Sani"?

" maza jeki gidansu kifada suzo akaita Asibiti kar ta mace min a Gida"
"To bari in je"
Mayafi Ilaham ta dauka ta fito da sauri a bakin gate taci karo da Nana
" yawwa Nana Jalila dama tanada asthma ne kowani cutan?"

A firgice Nana ta kalleta
"Asthma kuma? Bata da wani asthma, me yasameta?"
"Zo muje kyagani"

Ilham tafada tana janyo hannunta zuwa cikin gidan

"Subhanallah Jalila meya sameki?"

Nana tafada tana jijjiga Jalila amma Jalila bata San me akeba tafita hayyacinta
Da gudu Nana ta tafi gida domin sanar dasu abinda yake faruwa,
tana shiga gida a harabar gidan ta ci karo da su Jawwad

"Ke Nana lafiyarki kike gudu haka? sekace wata karamar yarinya mene haka"
Jawwad ne yayi maganar a Dan fusace

"Yaya Jalila CE"
"Me yafaru da ita?"
Yafada hankalinsa a tashe

Nima bansaniba  yaya tana gidansu Yaya Jalal yanzu muke tare da ita takoma dakko wayarta yanzu kuma  ta suma bata iya numfashi sosai
"Suma kuma"
  Ai bejira tagama bayanin ba yayi hanyar waje da sauri

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now