ABDUL JALAL

1K 29 1
                                    

.🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 6️⃣0️⃣114

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

     

              _MY FIRST NOVEL _

Turus Mummy tayi tana kallon tarkace da Ilham ta zazzage a gurin, cikin zare ido da masifa Ilham taci gaba da maganganu

"Wannan shine dalilin tafiyar da nayi, kinmin Alkawarin auren danki amma saboda rashin sanin mahimmancin Alkawari kika kasa cika abunda kika ce, wallahi dukda haka bazan kyaleki ba seke ma kin dandani abunda Uwata ta dandana"

Jalila kam har Jalal ya sata a mota zasu tafi ta bude motar ta fito, Jalal ya lura gaba daya a birkice take, ya fito yana fadin

"Jalila mene kuma? Ina zakije?"

Fuskar ta a hade tace

"Nifa jakata tana can, zuwa zan in dakko"

Jalal ya sassauta murya yace

"Haba wife, zauna a mota in dakko miki, bana son ranki ya kuma baci a banza saboda ni"

"Nika kyaleni dakkowa kawai zanyi ni bazan kuma kulata ba"

Jalal yace "Shikenan muje se in rakaki"

Bata tsaya jiransa ba tai gaba abunta ya biyo bayan ta ba tareda ya rufe motar ba, dan ya lura gaba daya idon ta ya rufe a fusace take.

Jalila na shiga dakin ta tarar da Maama da sauran 'yan uwansu sunyi zugum baki bude suna kallon Ilham, Ilham din ta kalla taga tarkacen layu manya da kanana a gaban ta, ga wasu kayan gashi da wasu kayan tsubbu se wari suke, Ilham kam idon ta ya rufe masifa kawai take, dan ba ta san Jalila ta shigo ba

"tsawon shekaru Ashirin da biyu da Jalal yayi yana shaye2 Ummana ce tai masa Asiri aka kulle zuciyar sa, akasashi a hanyar shaye2, duk abunda mutane suke gani daidai ne to shi akasin ta yake kallo daidai"

Da kyar Maman Ilham ta motsa bakinta ta fara magana dukda ba'a ganewa sosai amma idan mutum yayi shiru ze gane me take fada

"Khadija ke anaki haukan da kina tunanin zan kyaleki ne? Kimin cin amana mafi muni sannaan in kyaleki kinci bulus, ko yanzu na mutu na rage radadin abunda kikayi min, ni naiwa Jalal Asiri a cikin turare yai Amfani da shi aka juyamin tunanin sa, kabiru ne ya dau nauyin a lalata rayuwar Jalal da shaye2 dan ya dau fansa, wallahi khadija ba dan Jalila ba da se an kashe Jalal koya rayu a prison saboda shaye da neman mata, kuma da Ilham ta auri Jalal kokuma ya kwanta da ita da duk wata dukiya da kuka tarar ta dawo mallaki na, dan keda Jalal sedai kallo, dana sani daya nakeyi kuma nasan Alhakinsa ne ya kamani, Jalal bemin komai ba na dau Alhakin sa, yasan ina masa Asiri amma yayi shiru be fada ba, amma koma me ya sameshi kece sila Khadija, mugun kwadayin ki da son abun duniya, cin amana da wulakanta dan adam dinki ne ya ja miki, shiyasa na rama akan Jalal, na saka aka cusa masa kiyayyarki, wallahi ko yau na tashi akan kafufuwa na bazan barki ba sena ga bayanki"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now