ABDUL JALAL

361 18 2
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

              _ABDUL JALAL (2020)_

       _Story and written by_
      AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
        
   PART 2        
                          _PAGE  5️⃣/58_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Or Facebook on real humaira

              _MY FIRST NOVEL _

Ransa a hade ya tunkarosu, yana zuwa ya kalli Jalal yai murmushi, seda hakoransa suka bayyana, Jalal be fiye fara'a ba seda dalili dan kullum fuskarsa a hade, hakan ya tabbatatwa da Jalila, Jalal yana cikin farinciki
"Kasan wani abu Jawwad?" Jawwad yace "A a seka fada mutumina" Jalal se ya juya harshe yaiwa Jawwad magana da wani yare wanda Jalila bata iya fuskanta, dan zare ido Jawwad yayi tareda yin murmushi "dagaske kake?"
"kwarai dagaske nake, daddy ze dawo gobe Insha Allah, amma kasan meyafi sani farinciki"? "A'a seka fada"
"daddy ya tabbatar min da cewa 'yan maiduguri zasu kawo mana ziyara, zasuzo kano Jawwad, kaga hakan na nuna komai ya wuce" yakarasa maganar da kwalla a idonsa mikewa tsaye Jawwad yayi, "Dagaske zasuzo Jalal" "hakane daddy ne ya gayamin, zasu kawomana ziyar" "Alhamdilillah Jalal nafika murnar hakan, naji dadi, Allah ya kaimu suzo, hakan na nuna komai ya wuce a gurin su"
"Hakane gobe insha Allah zamuje dakko daddy karfe hudu ze dawo" "to Allah ya kaimu" ita dai Jalila ba tace komaiba sema wata cakwakiyar tunanin dasuka kuma sata, dama Jalal yanada yan uwa a maiduguri amma basa zuwa, ita bata taba ganin baki sunzo gidansu bama, se abokan kasuwancin Mummy dakuma wasu tsirari daga danginta, dan ko a gurin birthday din Jalal wadanda tagani, sunfi kama da Mummy, Jawwad ya kalleta yace "sarkin tunani, mekuma kike tunawa? Zamu wuce nida Jalal zamu fita"
"Hmm sekun dawo" Jawwad yai murmushi suka fita shida Jalal.
Yaya mairo ce take korawa Maama jawabi
"Zainab yakamata mu karfafa zumuncinmu ta hanyar hada auratayya a tsakanin yaranmu, kinga yaron gurina Nura tun Nana tana yarinya yakesonta, yakamata kubashi Nana, sannan Jawwad mu hadashi aure da Naja, kinga haulat kuma dan gidan baba habu Dini shize aureta, tunda Nana kanwar Nura ce kinga duk se a hada su koya kikagani?" seda Maama tai Jimmm, dan gara batun hada auren Jawwad da Naja akan auren Nana da Nura, dan tasan Nana bazata yadda ba, balle Abba tasan baze mata auren dole ba, dan sam Nana ta tsani Nura basa jituwa balle data girma gashi duk wanda yasan Nura yasan ba mutumin kirki bane, dan zuwansa prison sau uku
"Yanaga kinyi shiru ne? Ko baki yadda bane?" tab tasan a yanzu idan ta nuna mata rashin amincewarta zasu samu sabanine dan haka tace
"gaskiya Yaya mairo, wannan tunanine me kyau Allah ya tabbatar mana da Alkhairi saura kuma amincewar yaran"
"to meye inma basu yaddaba ai dole subi umarninmu" "A'a Yaya mairo in har basu amince ba Abbansu baze yadda ba, har gara Jawwad amma kinga Nana kinsanta da taurin kai"
"Ki barni dasu kawai, kinga Jawwad in aka hada shi da Naja kinga zamu dauke hankalinsa daga kan wannan makirar yarinyar, bari Nanan ta dawo" Maama dai ta amsamata ne amma badan ta yaddda da abunba har cikin zuciyarta.
Jalila tana nan inda su Jawwad suka barta halima tazo ta zauna sukai ta hira, har la'asar, Jalila na shirin komawa cikin gidane manu direba ya kawo Nana gida daga school, ta gaji sosai
Ta kalli Jalila "sarkin gudun makaranta kin gudunne tun azahar"
"wayagaya miki, mungama lectures ne da wuri kawai, sannu"
"Yawwa, au halima kindawo ashe" "eh na dawo" "yayi kyau"
Suka dunguma zuwa cikin gida, suna zuwa suka tarar su Mama duk suna palour, Jalila tai wucewarta dakinsu, tanaji Yaya mairo tanawa Maama mita
"Zainab ashe har yanzu baki janye yaranki daga jikin wannan kinibabbiyar yarinyar ba ko, saboda munafunci data dawo seta koma waje ta zauna, amma Nana tana dawowa kinga tabiyota ta dawo"
Sa'ada tace "hmm kema dai kyafada, muna funci a gurin kabilu bama dai ita tana wa mutane gadara sekace a gidan ubanta" dogon tsaki Nana tayi, ta wuce dakinsu
Binta sukayi da kallo, Naja tace "Tabdijan zama da madaukin kanwa, Ace kina magana Nana tayi miki tsaki, lallai abun ya girmama"
Nana tana shiga daki ta tarar da dakinsu kaca2, kan gadonsu hada kwanukan abinci "Jalila meye haka? Yanaga dakinmu a haka, sekace makwanci mahaukata, dakin dayake tas amma hada kwano akan gado"
"Ke karki saukemin gajiyar makarantarki, ni kin taba ganin ina cin abinci akan gado, kuma in tashi in bar kwano, nima haka na dawo naga dakin, bakinku ne sukayi masa haka"
"Kutmelesi, waisu Naja aikuwa sena musu rashin mutunci sun dauka kowa kazamine irinsu, suna abu kaman sakarkaru" fuuu Nana tai waje tana zuwa palour tafar zazzaga masifa "Ke sa'ada akanme zaku shigar mana daki kuci abinci akan gado, wannan wane irin shirme ne? Muda a haka muka bar dakin zakuyi marmarin shigane," Maama ta daka mata tsawa "Nana meye haka? Sa ada ba gaba take da keba? Kuma ya akayi kikasan sune sukayi hakan? " cikin shagwaba kaman zatayi kuka tace
"Maama dan tana gaba dani sesuyi  mana haka a daki, kuma koba a gayamin ba ai nasan Jalila tafini gyara dakin nan tunda bata son kazanta bata tabcin abinci a guri ta barshi ba, amma daga zuwansu zasu bata mana daki, wallahi karku kara shigar mana daki, tunda baku da hankali, kazamai kawai" bude baki sukayi da mamaki Naja zatayi magana Yaya mairo ta hanata tace "rabu dasu yi hakuri bazasu karaba, sannan inason in kin samu lokaci kije gida kisameni ina son ganinki" seda Nana ta yamutsa fuska, sekuma tayi shiru  takoma daki tana kunkuni tana mita, seda tafara gyara gurin sannan ta shiga wanka, dan Jalila tace wallahi kartin banza bazasu bata daki ta gyara ba. Koda Nana ta wuce daki Yaya Mairo tace "kingani ko zainab yaranki na neman sufi karfinki ace har kina fada tana mayarwa saboda waccan yar karuwar, kinsansu arna ba ruwansu yayansune suke juyasu shiyasa take so ta mayar miki dasu irinta ki tashi tsayefa wallahi aikine babba agabanki"
Koda su Yaya mairo suka tashi tafiya seda aka bude store aka jido musu kayan abinci, banda wanda Abba yakesawa a diba a basu, banda kudi da take bawa yaya mairo, se anbi kayan abincinsa na gida bada saninsa ba anbasu banda sitira da sauran kayan more rayuwa, dayake Yaya mairo akwai mugun sonn abun duniya, duk an kwashi kaya an kai boot Manu direba ze maidasu gida. Nana ta fito daga wanka zata shafa turare, amma ta lura babu wasu abubuwan akan mirror dinnasu, tsaki tayi "Allah ya kyauta wannan masifar, Jalila kallifa hada kayan mu suka sata, wallahi senaje se sun bamu" da sauri Jalila ta dakatar da ita "bari Nana ai yan uwankune inkikayi haka kaman kin tozartasune, ai arzikine sekinada abun sata za a sata, bakomai semu sayi wasu" haka Jalila ta lallabata ta hakura badan tasoba. Jin alamun fitarsu daga palourn yasa Jalila ta fito palour, hakan yai dai2 da dawowar
sa ada zata dauki wasu kaya data bari a palour wanda na Nana ne da Jalila ta dauka bada izininsuba, hada kayan man shafe2 da turaruka da Nana take mita, Jalila ta kalleta tai murmushi "Allah sarki bariki batayi rana ba, ace duk iskancin da ake a bariki ba a tara abunda za a rike tsofaffi ba se an hada da maula a dangi, bayan haka kuma se an hada dana sata to Allah ya kyauta" a fusace ta kalli Jalila ta nunata da yatsa "Karki kara dangantani da bariki" "Ke sauke yatsanki karki kuma nunani  karki rainamin hankali mana nasan komai kallonku kawai nake daga ke har mahaifiyarku, kuma wallahi kigayamata ta kiyayeni inasane da abunda takemin da cin mutuncin uwata datakeyi, idan na tashi yimata rashin mutunci se tagane bata da wayo, har yanzu ban taba gwada muku wace Jalila ba, ta kiyayi haduwata da ita" Jalila tai gaba tabar sa ada da bude bakin mamaki. Bayan tafiyar su Naja da daddare Nana se mita take "nikome yaya mairo zata gayamin wani wai senaje gidanta, Allah yasa wani abun Arzikin nanba rainamin hankali zatayiba, nibana son zuwa gidanta saboda wannan Jarabar tata"
"To ai hakuri zakiyi, maybe abunda take son gayamikin yanada mahimmanci ne"
"Anya Jalila bana tunanin hakan amma bansaniba"
"Yawwa Nana dan Allah in tambayeki mana?"
"to Allah yasa nasani" "dama Jalal suna da wani yarene naji sunayi shida Yaya Jawwad" murmushi Nana tayi tace "Eh sunadashi, ta bangaren daddynsa, kakanin Jalal kanuri ne" Jalila ta gyada kai tace "Amma ya akayi Yaya Jawwad ya iya"
"Lallai Jalila har yanzu kina daukar amintarsu da wasa, tare suke kwana su tashifa, yanzune suka dena kwana guri daya, saboda Yaya Jalal yana fita yawonsa, da har maiduguri suke zuwa suyi kwanaki" jinjina kai Jalila tayi tace "lallai kam dole ya iya yaren" daga nan suka bar wannan zancen, Jalila ta kwanta bacci Nana kuma tafara waya da saurayinta.
    Yau lecturer su Jalila ya kudiri aniyar yimusu test, unexpected saboda ya hukunta Jalila sir Hafiz kenan, matashin mutum me matukar izza da jin kansa, bashi da mutnci kokadan, kayadda dalibai a course dinsa shiyafi komai sauki a gurinsa, ga kwauron maki shiyafara korar Jalila daga class, sau biyu yana korarta daga class, na farko yana lectures tana tunani na biyu kuma kullum ya shigo class yamata tambaya bata sani ba, gashi ya lura seta gadama take attending class ya fuskanci dakikiya ce amma tana da izza da jin kanta dan haka, bayan anfito daga lectures karfe biyu, unexpected ya kira captain dinsu yace, ze musu test bayan sallar azahar, students din sun shiga damuwa saboda basu shirya ba, kowa yakama littafin sa, zahra ma ba abarta abayaba ta dage tanata dudduba littafinta, yayinda hajiya Jalila bayan ta idar da salla, ta janyo abincinta tanaci tana chatting da yaya Jawwad yana dariya , zahra ta kalleta "Jalila ke bazakiyi karatun ba? Test fa zeyi kuma ance yanada kwauran maki" "don't mind me, yi karatunki kawai, ni yunwa ce ta dameni" "to amma ai gara...." "shhh ya shiru kicigaba da karatunki kar haddarki ta zube" zahra ba karamin mamaki Jalila take bataba, ga dukkan alamu dai ba wani ja take ba saboda ba ataba tambaya ta bada amsaba amma za ayi test ko a jikinta, se tsabar iya tsiwa fal cikinta,
Karfe biyu da rabi suka shiga test din nan, wadda duration din test din 30minutes ne kawai, ga tsaro a hall din dan duk ya rarrabasu, bame iya ko kyakykyawan motsi, sannan Jalila ita kadai aka ajiye agaba bakowa a kusa da ita bayanta ko gefenta, gashi ya dakko wasu malaman department din su tayashi invigilation, Jalila ta lura yasamata ido sosai, ya dinga safa da marwa yana kallonta, kowa ya dukufa amma ita tana zaune tana kalle kallenta karewa ma ta tafi tunanin abunda yake gabanta na rayuwar Jalal, sir hafiz yazo kanta ya duba paper dinta ammma empty, ya kalleta yai kasa da muryarsa ya dan sunkuyo da fuskarsa yace "dakikiya kawai ba abunda kika rubuta, dama ba kyaja se tsabar iya shege ko? Rashin mutunci kawai shine a kwakwalwarki, bakomai se shirme, sokuwa kawai barikiji in gayamiki wannan shine last chance dinki idankika fadi test din nan kin fadi exams dina" wani irin kasaitaccen murmushi Jalila tayi masa alamar sam bataji zafin maganganunsa ba ta dauke kanta, seda yayi gaba ta bude paper dinta ta amsa tambayoyin, nanma itace karshen bayarwa, yauma batajira manu ba ta tafi gida.
Tana tsaye tana jiran mota, amma bata samuba dan haka ta yanke shawarar fara trecking, tana cikin tafiya taga wata katuwar mota range rover baka wuluk se sheki take, ga wasu mota biyu gaba da bayan motar, range rover tazo ta tsaya agabanta, kokari take ta wuce motar, amma se kokarin rufemata hanya me motar yake, "wai wani tsabar wulakanci ne haka? Bana son wulakanci fa. Wasu yan sanda ne biyu, suka fito daga motar " Yan mata kinsan waye a cikin motar nan kuwa, ki iya bakinki fa, kinsan matsayinsa kuwa? yanzu dai yace yana son magana dake kishiga motar semu ajiyeki" cewar daya daga cikin yansandan, wani mugun kallon banza Jalila tayiwa yan sandan, "ai mutum ne a motar ba aljan bako, to duk matsayinsa ace masa bazanzoba, malam bani hanya zan wuce" kuma shan gabanta sukayi "Ke waime kike takama dashi haka kike mana wulakanci kinsan suwaye mu, kinsan dawa muke tare?" "matsalarkuce koku suwaye kodawa kuke tare ba damuwata bace, kuban hanya kawai in wuce tunkafin in taramana jama'a" motar aka bude, wani hamshakin mutum ne yafito daganinsa yaci ya koshi, sanye yake da kakin yan sanda, nan suka dinga sara masa, babban mutum ne ba yaro bane, dan ze haifi Jalila, gabanta yazo ya tsaya "Am sorry mun tsareki a hanya, kizo mu saukeki a gida kinga da rana sosai" Jalila da rashin kunya taso tayi masa amma ganin babban mutum yasa tafasa "A a bakomai nagode, inada kudin mota, amma kace subani hanya in tafi" "zasu baki hanyane, amma kitemakeni da lambarki inaso zamuyi magana" dan zare ido Jalila tayi "laifin menayi maka?"
'laifine babba kam tsakaninki da hukuma , amma tsakaninki da hukumar zuciyata"a ranta tace "ji tsohon kawai, tab wallahi wrong number zanbashi"
"yakikayi shiru, kitemakamin mana"
"kawo abu inrubuta maka" ya mikomata galleliyar wayarsa, dazata samasa wrong number kawai wata zuciyar tahanata "ze iya zama garkuwa gareki daga sharrin su Jeje" ajiyar zuciya tayi tasaka masa lambarta
"Nagode sosai beauty, muryarki kawai ta isa sani bacci cikin nishadi, bankiba muyita tsayuwa anan kinamin magana, gayamin sunanki"
"Kaga ni nagaji, tafiya zanyi rana ta dameni" "hmm se anjamin aji kenan, to shikenan tunda bazaki bari inkaiki gidaba i will call you Insha Allah" bata kuma cewa komai ba ta wuce.
Tana zuwa gida tai wanka tai salla taci Abinci, Mummy takira Maama awaya tace dan Allah ta turamata Jalila ko Nana,su karbi sakon Ilham tana bacci, Dayake Nana bata dawo ba seta tura Jalila, wani tea flask ne me kyau a kwali Mummy tabawa Jalila tace ta kaiwa Maama, wata coustomer zata siya, ta karba ta fito, Jalila na fitowa harabar gidan motarsu Jawwad ta shigo sun dakko Daddy daga airport, tsayawa Jalila tayi daddy ya fito daga motar dauke da brief case dinsa, kana kallonsa kaga mahaifin Jalal, amma yafi Jalal kyau, sedai wannan dogon hancin Jalal ya dakkoshi, shaye2 ne yabata Jalal amma yana da kyau irinnasa, har kasa Jalila ta zube tana gaisheshi, da fara'a ya amsamata
"Takwarar Jalal, ashe kina kanon har yanzu ya kike ya karatu" cikin tsantsan ladabi Jalila tace "Karatu Alhamdilillah daddy" "Masha Allah, Allah ya temaka yayiwa rayuwarku albarka" "Ameen daddy" Jawwad ya dakko trolley da traveling bag na daddy sukayi gaba yayinda Jalal ya tsaya rufe mota, ta taka ta karasa gurin Jalal yana juyowa yaci karo da ita hade fuska yayi kaaman yaga kashi, dan da yaganta yake tuno cin mutuncin datayi masa, seyaji kaman yaimata shakar da seta kusa zuwa lahira
"Kalleka a haka sewani zumudi kake wai kai kafi son mahaifinka, sekace gaske, abunda inka ga dama shima daga masa murya kake, kokagaya masa maganar daka gadama, kana nuna kana sonsa amma baka hakan a aikace, ka girmamashi, tausasa lafazi a gareshi, in gari ya waye kaje ka gaisheshi, in yana maka fada ka nutsu ka danne zuciyarka, kayi hakuri dashi a duk lokacin daya bukaci taimakonka ko alfarmarka zama taredashi da gudun bacin ransa wanda hakan zesa yaji dadi yayi alfahari dayana da ďa me kaunarsa, duk fa bazaka iya wannan ba, ta yaya zaka nunawa duniya cewa kana son mahaifinka, hmmm bazaka iyaba banda zafin zuciya da raina iyaye baka iya komai ba kodayake ba abun mamaki bane no need to expect anything good from you, giya ba karya bace, a canza hali abokin Yaya.
Ta danyi murmushi tai gaba, tana addu'ar Allah yasa abunda tafada yai tasiri a zuciyar Jalal, Jalal karasa rufe motar yai ya nufi cikin gida jikinsa a sanyaye, Jalila tazame masa karfen kafa ta uzzuramasa dayawa, gashi har yanzu yakasa samun mafita akanta. Cikin gida yanufa jikinsa a sanyaye yana zuwa ya tarar dasu a palour a zazzaune, daddy ya kalli Jalal yace "Ya dai naganka a haka? Meya faru" dan girgigiza kai yayi "bakomai daddy" haka dai akayi hira sama2 aka watse domin bawa daddy damar ya huta.
      Hannah ta na kwance juyi kawai takeyi, zuciyarta fal tunani da damuwa, dagaske son Jalal ne yake damunta, gashi har yanzu takasa samawa kanta wata mafita sam Babu alamar Jalal ze amince ya aureta, a da aikin datakewa Jeje na son Jalal ya amince da ita, sudinga shedanci hakan ya gagara, amma ita yanzu babban burinta ya aureta in har ya aureta tagama karuwanci har abada, to amma tayaya? Yazata samo kan Jalal ya yadda da ita ya karbeta ya aureta, abaya tasan ta taka rawa gurin kara ingiza shi akan shaye2 amma yanzu tayi nadama, son gaskiya takewa Jalal yanzu ita meye abunyi meyakamata tayi, shiru tayi daga can kuma tayi wani guntun murmushi.
Koda dare yayi, Jalal rasa abunda yake masa daďi yayi, tunani ya dameshi, ransa yagama baci Jalila ta dameshi, to amma dagaske take baya son daddy? Shidai yasan yana son daddynsa to amma fa wataran shima yanamasa masifa kaman yanda yakewa Mummy, to hakan yana nufin hakan danakeyi daddy bayajin dadinsa? , to meyasa nake hakane? Gaskiya ina son daddy na, dan bani da takamarsa, jiyayi kirjinsa yafarayi masa nauyi dan haka yatashi yakunna sigari, yana gamawa ya dora da giyarsa seda yafita hayyacinsa sannan ya kwanta bacci

Share please
More Comments............

🖊️ 🖊️ 🖊️ 🖊️ 🖊️ 🖊️

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now