ABDUL JALAL 78

344 21 3
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 2️⃣5️⃣78

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com



_MY FIRST NOVEL_

Jalal Ya dau lokaci yana kallon ta.
cikin rawar murya Jalila tace

"Sannu ya jiki?"
shiru yayi bece komai ba ya lumshe idonsa.
"Ko inkira maka Jawwad?" still shiru yayi bece mata komaiba tamarasa mezatayi, idonsa a lumshe taga hawaye nabin gefen idon Jalal, hankalinta yakara tashi
"Inkira maka likitane?" takarasa maganar tana hawaye, bude idonsa yayi ya juyo yana kallonta a hankali yace
"Kukan mekikeyi? Ko Na kuma yi miki wani laifinne? Nasan bazakiyi kuka dan halin danake ciki ba, zakifiso in mutu saboda yayanki ya huta ba?"

Girgigiza masa kai Jalila ta shigayi amma takasa magana
Ya hade rai yace "kidenamin kuka, nagaya miki kin cikamin kunne"

Cikin muryar kuka tace "Yi hakuri na dena" tasa hannu ta share hawayenta.

Jawwad yashigo da likita suna zuwa kan Jalal ya bude ido, Jawwad ya zauna kusada shi yace "Sannu ya jikin naka?"
"Alhamdilillah naji sauki azo a sallameni"
murmushi likitan yayi sannan yace

"kai Jalal da wuri haka, bazamu sallameka yau ba, se mun tabattar dakabi dokokin dazamu saka maka, bamaso se mun Sallameka akuma dawo da kai Rai a hannun Allah"

Jawwad yace "rabu dashi doctor yi masa abunda yakamata, baza'a sallameshi ba seya warke gaba daya"

Jalal ya tashi zaune, Likita yakara duddubashi, sannan yayi rubuce2 a file din Jalal, ya rubuta wata takadda yace
"Ga wannan Jawwad bamu dasu a pharmacy sekaje cikin sabon gari zaka samoshi"
Sannan likitan ya kalli Jalal yace "Man yakamata ka cire abunda yake ranka, karka kashe kanka da kuruciyarka kana matashinka, kana da kudi kana cikin Ni"'imar ubangiji meze daga maka hankali haka? "

kallonsa Jalal yai ya dauke kai likitan yacigaba da cewa

"Jininka ya hau sosai, dole kadena damuwa sannan u must reduce the amount of cigarette and shisha you take every day (PEOPLE WHO SMOKE ARE ABLE TO DIE YOUNG!!!) so you should be careful, akwai sinadarin dayake saka hawan jini a cikin taba, shanta yana kawo lung cancer ko tuberculosis, and you should reduce Alcohol intake, ka rage shan giya shima, tana saka cututtuka da dama, kaman Ciwon Hanta, ciwon koda, tana kara asassa ciwon sugar akwai kuma nauo'in ciwon ido da take sakawa, dan haka a hankali yakamata ka rage, sannan kadinga cin Abinci kaga Ulcer yana nema yazeme maka chronic "
shiru Jalal yayi ya sunkuyar da kai, Jawwad yace
"Shikenan doctor za'a kiyaye Insha Allah"
"Yawwa masha Allah, Allah yakara sauki" doctor ya juya ya fita, Jawwad ya zagayo ya zauna kusada Jalal yace

"Kaji abunda doctor yace ko? Please and please ka kiyaye dokokin da aka samaka kaji Dan uwa" Jalal dai bece komai ba, ya sunkuyar da kansa, Jawwad ya juya ya kalli Jalila yace

"Baby miko kwandon Abincin nan a hada masa yaci se inje siyo masa maganin"
Ta dakko kwandon, ta zuba kunun gyada cikin wani katon kofi ta zuba dankali ta mikawa Jawwad, Jawwad ya zare ido yace "Kai Baby yazeyi da wannan kunun yayi yawa ai, bakiga bashida lafiya ba, aibaze iya shanye wannan ba"
Jalila ta ɗan tura baki tace "Au haba, ka tuna lokacin dana kwanta a Asibiti cikin katon kofin nan yazare min ido sena shanye, shima ka zare masa ido ya shanye" takarasa maganar tana dan tura baki.
Bakinta Jalal ya tsaya yana kallo shikuwa Dariya Jawwad yai yace "itaku kedashi, kema seki zare masa ido ya shanye, bari inje in siyo maganin" Jawwad ya mike ya fita.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now