ABDUL JALAL 104

1.2K 21 1
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣1️⃣ 104

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

_MY FIRST NOVEL _

Tunda aka gama biki Maama bata dawo ba, seda takuma kwana goma a Bauchi, taji dadin zaman garin sosai, gashi mutane ne masu karamci da son 'yan uwa, Abba ne yazo ya dauketa suka koma gida kanon dabo.

Bangaren Angwaye da Amare da sukayi Auren soyayya Se shan soyayya da kauna suke, tsakanin su banda Jalila da Jalal da babu wanda yake neman wani a tsakanin su,
Jalila ita wannan zaman hutun ya isheta, ita dama kano suka batta tayi zamanta a gurin Maama ya fiye mata wanna zaman.

Tana ta zancen zuci ne Husna 'yar gidan Anty ta shigo da waya ta mikowa Jalila, Jalila tasa hannu ta karba, video Call ne ta ďaga wayar tana ďagawa taga fuskar Jawwad cikin sauri ta mike zaune

"Yaya Jawwad kaine?"

"Nine Baby, yaya borno yasu Anty?"

"lafiya kalau Yaya Jawwad, kayi kiba sosai kaman ba kaiba, ina Hanan?"

"tana kitchen tana girki, kema gaki nan kinyi kibar ai, ya mijin naki?"

Tabe baki Jalila tayi tace "yana can lagos" Hanan ce ta taho da gudu ta haye kan cinyar Jawwad tace

"Hi queen, ya kike?"

"Wow Hanan, wannan kwalliya haka, masha Allah, naji dadin ganinku wallahi nayi farinciki, Allah ya albarkaci rayuwar aurenku, yara muku kaunar juna"

Tausayinta yakama su Jawwad, Hanan tace "Jalila kunyi waya da Nana kuwa?"
"Eh munyi waya da su, ya Abuja ya zaman kadaici?"
Jawwad yace

"muba ma zaman kadaici ko My sugar, masu zaman kadaici suna Azabtar da zukatansu sun san kansu"

yai maganar yana kallon Hanan, Hanan tace

"Sosai makuwa, ba wani kadaici, kullum muna tare, kema kice akaiki gidan mijinki kigani in zakiji wani kadaici"

"Allah ya kiyaye" Jalila ta fada tana harar Hanan. Wayar Jawwad ta fara ringing, Jalal ne yake kiransa, Jawwad yace
"Baby mijinki ke kirana, bari inje in amsa" Hanan ta zauna akan kujera tace
"Jalila wai yaushe zaku sauke wannan taurin kan ke dashi ku fuskanci juna?"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now