ABDUL JALAL (2020) 11

300 21 0
                                    

_ABDUL  JALAL_
           (2020)

      _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
    (Daddy's girl)

               PAGE-  11

PART 1

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
What's https: //chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Is a free book

Ina yinku AbdulJalal novel fans irin💯💯💯 da duk sauran masoya wannan novel ina jin dadin comments dinku love u all ❤❤❤

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢
Your comments give me courage

   

         -my first Novel-

Kafin su Ankara takuma yi musu wani shouting din
"Ku tafi kubani guri"
Sun² suka fice su ka bar gurin dakinta ta koma ta cigaba da sintiri to yanzu ya zatayi meye mafita washe gari takuma sawa aka nemo mata
Abiola da yarabanci sukayi magana wannan karon

(kunsan dai ni ba yarabanci nake ji ba Dan haka bansan me suka ce ba)

Naga Abiola ya daga kai ya kalleta a razane

"Ko bazakayi ba"
ta tambayeshi

"Zanyi yanda kikece"
Ya fada Kansa a kasa

"Mark u idan maganar nan ta fita wani yajita hukuncinka shine..
Tai taku biyu
" life imprisoned!!! "
Ya dago da sauri ya kalleta

"Yes " tafada tana kallonsa "you can leave"

Da la'asar har camp Abiola yaje ya lallabo Aliyu ya fito da shi kan cewar za suje yawon shakatawa ne,

Wani hadadden lambu ya kai Aliyu, an kawata lambun da kayan itatuwa masu matukar kyau gurin yayiwa Aliyu kyau matuka,

"Gaskiya gurin nan yayi kyau so cool"
Aliyu yayi maganar yana murmushi tare da shafa Kansa

"Dagaske gurin yayi maka kyau"
Sukaji muryar mace a bayansu
Abiola yasan muryar wace dan haka yakara nutsuwa tare da sunkuyar da kai

Aliyu ne ya waigo yaga me maganar sanye take da riga da skirts na atamfa kanta ba Dan kwali
matashiyar budurwace bazata fi shekara goma sha takwas ba ba dai fara ce ba amma tana da kyau black beauty ce

Takuma maimaita abinda tace
   "dagaske gurin nan yai maka kyau"
Tafada tana murmushi, Wanda seda dimples dinta ya lotsa ta kara kyau
Shima Aliyu murmushi yayi mata

"Sosai makuwa gurin yayi matukar kyau kuma da kikazo seyakara haskawa kyansa ya kara fitowa"
Murmushi ta kuma yi

"That's good"
Tafada tana kallonsa
"Akwai gurare masu kyau a garin nan gurare masu saka nishadi, Wanda nasan babu su a garinku"
Tafada tana Dan kashe masa Ido

"Kinsan garin namune kika fadi haka"

"No ba kayi kama da yan garin nan ba shiyasa nasan ba Dan garin nan bane kuma bana tunanin kanajin yarenmu"

Shikam abiola gefe yakoma ya nutsu kaman bashiba

"Hmm to garinmu yafi naku kyau"

"Wane gari kenan?"
Ta tambaya

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now