Jalila tace

"ba wani hadda shagwabarki da neman magana"

"wallahi Jalila ina jin tausayin Haidar sosai, bana laulayi se dai bakomai nake iya ci ba shine kullum ke nema min me zanci, Amma ba yadda zanyi ne"
.
"Allah sarki, Allah yarabaku lafiya, wai watan cikin naki nawane?

" wata na biyar "
Zare ido Jalila tayi " wai har munyi wata biyar da Aure? Amma kina shiga kikayi karo da shi? "

Hanan tace

"ban saniba, da shi naje, 'yar rainin hankali wallahi satina biyu, naita ciwon kai muna zuwa Asibiti aka ce cikine"

Dariya Jalila ta dingayi tace "angama iyayin, ana zuwa akayi karo, Allah yaraba lafiya"

"Ameen dai, ina mijin naki, fatan dai komai lafiya?"

"yana nan lafiya" Jalila ta bata amsa

Hanan tace "Ina fatan komai Lafiya Jalila, Allah yasa kun daidaita"

Jalila tace "gamu nan dai"

"gaku nan dai kamar yaya? Har yanzu ba kwa shirin ne"

"munayi sama sama"

"Jalila waike wane irin taurin kaine dake haka?"

Jalila tace "ke karki min fada mana, kin dameni fa, se anjima tafi gurin mijinki kiyi masa". Seda sukayi dan fadan da suka saba sannan sukayi sallama.

Jalila ta tashi ta dauki zuma ta nufi dakin Jalal, yana ganinta da container zuman nan ya hade rai, murmushi ta farayi tana cewa

"meye kuma na wani hade rai, sekace kaga wani abun gudu"

Jalal yace

"nifa nagaji da shan wannnan abar, kullum kizo kiyita bani, ciwon ciki take sani fa"

Jalila tace

"Ai ciwon cikin ba me damu bane, saboda magani nake baka, so nake inyi substituting din giyar da kake sha da zuma, kuma karatun qur:ani ne a ciki, Insha Allah very soon zaka dena shan giya"

Jalal yace

"ko yanzu ma aina dade ban sha giya ba, dan Allah ki dinga kyaleni da zumar nan, kodai wani abun kike zubamun, dan ki mallakewa Mummy danta?"
Yai maganar yana kashe mata ido, tareda yin murmushi

Dariya Jalila tayi tace

"Kai mallake ka wani wahala zemin ne, ai base na baka magani ba idan ina son hakan?"

"Allah ko?"

Jalila tace "Eh mana, yanzu dai karbi ka sha spoon biyu kawai"

Seda ya bata rai sannan ya karba ya sha yana ya tsuna fuska, dan jan dogon hancinsa tayi tace

"barakallahu fik"

Jinjina kai kawai yayi bece komai ba
A shagwabe Jalila tace

"baka fada ba fa"

Yace "Ameen, thank you"

Murmushi tayi ta shafa sumarsa "weldone dear, bari muyi Adhkar seka kwanta ko?"

Jalal yace "yadda duk kikayi"

Jalila tace "yawwa kafin muyi Adhkar bari muyi magana, wai yaushe zaka koma aiki? Kullum kana gida se dai kaje ka zaga gari ka dawo"

"bazan koma aikin nan ba"

"meyasa?"

" bashi da Amfani ina can zuciya ta tana nan, sam bana samun nutsuwa, ga banbancin Al'adu da dabi'u da muke dasu, gashi nika dai nake tafiya babu ke, akwai damuwane gara inyi zamana inta ganinki kullum ina jin dadi"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now