"kinga sauraramin bana son salon munafurci, nafada bana sonta, kuma bazasu taba ganin haske ko albarka a rayuwar Auren nan ba, kuma wallahi sena kashe Auren, babu wani alkhairi ko amfani da take da shi a gurin Jalal, wannan dunkiyar tasa kawai take kwadayi, shiyasa ta aureshi ta juyamin shi, to wallahi bata isa ba, tunda nina haifi ďana, shida abunda ya mallaka nawane, muddin ta shiga gidan Jalal tafara kirga ranakun bakinciki a rayuwar ta har seta kyalemin ďana, shegiyar yarinya mara usuli"

Tunda ake fadawa Jalila rashin mutuncin Mummy bata taba zaton ya kai haka ba, wata hira da suka tabayi da halima ta fado mata rai da halima take ce mata "Sayyada karki bari wani abu ya hadoki da matar nan dan bata da mutunci" sosai Jalila miyagun maganganun Mummy suka daki zuciyarta.

Hajiya Salma tace "Shikenan mungode da wannan karbar da kikayi mana muda matar ďanki, Amma ki sani idan kin rabani da gidan mijina kin zauna lafiya, bazan taba bari ki lalata auren nan ba, Allah yafi ki sannan a wannan karon dai2 nake dake, Aure an riga anyi shi kuma mutuwa ce zata raba shi"

"Se ayi in gani ai"

Anty tace "Jalila tashi mu tafi"
Jalila ta mike wani irin jiri na kwasarta, se rarrashinta Anty take,
Ilham ce ta shigo palourn da alama daga wani gurin take, wani kallon banza Ilham tayiwa su Hajiya Salma kafin idonta ya dira akan Jalila, dukda Jalila tana cikin lafaya, amma Jalila tayi kyau, jikinta yayi sumul sosai ga wani kamshi da dakin yake yi, hannunta ya sha kunshi ja da baki.

Ilham na ganin ta wani azababben kishi ya taso mata, gurin Jalila ta nufa gadan2 idonta ya rufe gaba daya tace

"Wallahi bazan taba yafe miki ba, kin rabani da ďan uwana abunda na dade ina so shekara da shekaru, wallahi zakigane baki da wayo, munafuka kece me cewa babu abunda zakiyi dashi, kinsha kiransa namiji mara daraja, mara tarbiyya da yake makirace kika zagaya kika Aureshi, algunguma.... Sosai Ilham take kuka tana kokarin fizgo Jalila

Hajiya Salma a fusace ta sa Jalila a bayanta tace "Ke lafiya meya haka?"

"ban saniba wallahi sena yi mata rashin mutunci, seta gane ni ba kanwar lasa bace, naga ta yadda zatayi zaman Auren a kwanciyar hankali"
Jalila tasa hannu ta ďaga lifayarta ta kalli Ilham ido duk hawaye, ga idanunta sunyi jawur, kallon da Jalila tayi mata seda gabanta ya fadi yadda taga Jalila ta hade rai tana mata wani irin kallo.

Sunkuyar da kai Jalila tayi ta cigaba da zubda Hawaye, Jan hannun Jalila su Anty sukayi suka fice waje.

Anty tace "Anty Salma su dangin su khadija tun asalinsu basu da mutunci, masifa acikinsu kamar barkono"

Hajiya Salma tace "Allah dai ya kyauta, ki kwantar da hankalinki Jalila komai ze wuce Insha Allah"

Suka sa Jalila a mota zuwa gidan ABDUL JALAL.

Dukda kan Jalila na cikin mayafi amma gidan ya tsaru sosai, suka kaita daki suka ajiyeta, akaita mata nasihohi, daga nan suka tafi suka barta a gidan, sakkowa tayi daga kan gadon ta nemi guri ta zauna a kasa, tana tuno irin maganganun cin mutuncin da Mummy ta dingayi mata da wulakanci, take taji mugun danasanin Wannan Auren yakara rufeta, Hawaye kawai takeyi, Mummy ta riga tayi mummunan furuci akan Auren nan, dama gashi bata tabaccin shi kansa Jalal din yana sonta, ga Ilham ma miyagun maganganun da ta dinga faďa, shikenan ni kowa na raba nazama abar kyama, Allah ka yafemin in wani laifin na aikata.

Har wajen goma na dare sannan Jalal ya shigo gidan, milk din yadine a jikinsa me laushi, da hula akansa, dakin da aka kai Jalila ya nufa dauke da ledoji a hannunsa, yana shiga ya tarar tayi zaman dirshan a kasa tanata zubar da Hawaye, dan tsayawa yayi yana kallon ta dan be san ta ina ze fara ba, a hankali ya karasa gabanta, tana jinsa amma ta share ta cigaba da kukanta, ya sa hannunsa ze janye nata daga dukunkunewar da tayi a mayafi, da sauri ta janye hannunta ta ja da baya sekace taga dodo.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now