ABDUL JALAL 104

Começar do início
                                    

"Hanan ya kikeso inyi ne? Nagaya muku Jalal ba sona yake ba, kawai an lika masa ni ne, tun lokacin biki nake rashin lafiya be nemeni ba, ko ta kaina baya bi, se ranar da ze tafiya ya ajiyemin takadda, sam be damu dani ba, Hanan ku kukayi dacen Auren soyayya amma bani ba, nasan da Ahmad na Aura baze watsi da lamarina ba"
kan Jalila ta gama maganar har hawaye ya wanke mata fuska. Cikin taushin murya Hanan tace

"Jalila, kina da Aure yanzu be kamata kidinga ambaton wani namijin ba, Sannan Jalila kinsan halin mijinki tun kafin kuyi Aure, bashida shiga sabagar mutane, dukda ke matarsa ce yanzu, Amma kiyi hakuri, komai ze wuce Jalila, kalli yadda kikayi kyau kamar a saceki a gudu, i wish yana nan yaga wannan kwalliyar taki se ya rude, waima me suke bakine kikayi wannan kyan"

Murmushin takaici Jalila tayi tace

"Hanan kenan, kina tunanin zanyi wani abu daze gani ya yabane? Ko ya burgeshi, shi ba sona yake ba kawai an aura masa ni, be damu da yasan a halin da nake ba balle ya yaba kwalliya ta, se an jima ki gaida Yaya Jawwad.

Jalila ta ajiye wayar ta dora sabon kuka me sauti.
ji tayi an dafata, ta dago ta kalli wanda ya dafata Husna ce fuskarta dauke da damuwa tace

"Sorry dear, please stop crying, kidena kuka ko tunanin broz Jalal baya sonki, is not like that, ina kula da yadda kuke share juna kedashi, which is total bad, an riga an daura Aurenku, kamata yayi ku manta da abunda ya wuce, Jalal has a social disabilities at times, tun lokacin da yakoma drunker, mutane suke kyamarsa he decided to isolate himself from the people, he dint interact with people as before, believe me he loves you bazaki gane hakan ba sekin zauna da shi, yanada kirki sosai, ki dena yawan kukan nan please "

Jinjina mata kai Jalila tayi Husna tace

" Yawwa mrs Jalal, Jalal bashi da matsala bayan ta shaye2, zaki maida shi yadda kikeso, yana sonki ne shiyasa yakeyin abunda kike so, ba dan haka ba a duniya akwai abunda ba wanda ya isa Jalal yayi wani abun yayi. Husnah ta cigaba da rarrashin Jalila, a lokacin take gayawa Jalila Tanada Aure, mijinta baya gari ne, shiyasa itama tazo tayi zamanta a gida.

Ilham takasa zaune takasa tsaye, kwanata kusan shida a gidansu suna sakawa da warwara akan yadda zasu bullowa lamarin ita da umanta, yanzunma zancen da suke kenan

"Umma kin san kashinmu ya bushe idan yarinyar nan ta tare da Jalal, aikin ze lalace ne fa, zamu rasa komai, jiran da mukayi tsawon shekaru mu dauki fansa ze tashi a banza ne, indai yana tareda yarinyar nanmun rasa komai, daular da muke hange bazamu sameta ba"

Umman Ilham taja numfashi ta hura hanci tace
"Bazan taba yadda tsawon wannan lokacin daukar fansa ta ya tsaya akan lalacewar Jalal ba, dole in wulakanta khadija in mallake dukiyar da take takama da ita, sena ga ta wulakanta daga ita har Habib din"

Ilham tace "Umma to tayaya?"

"ki kylaeni kawai, nasan abunda zanyi, tunda ke kinkasa abunda ya kaiki gidan tsawon lokaci"

"Umma kenan, ba kasawa nayi ba, nayi iya yina, ba daban wannan Jalilan ba da tuni an wuce gurin, Amma ni hankalina a tashe yake umma, kin san abunda Aure ga Jalal yake nufi fa a shirin mu, so soyayya da wata mace bayanni ga Jalal kim san barazana ce a garemu, wallahi ko bacci bana iyayi"

"ni nace ki bar komai a hannuna, nasan me zanyi"
"Shikenan Umma"

Mummy har gidansu Jawwad taje da kanta, ta tarar da Maama tana ta fama da aikin gida. Cikin fara'a Maama ta tareta tana mata sannu da zuwa

Aikuwa a fusace mummy tace
"kinga niba yashe bakinki nazo gani ba, ba hakoranki nazo ki nunamin ba, baban su Jawwad na nan ne?

" A'a baya nan lafiya kuwa? "

" ina fa lafiya, saboda tsabar munafunci a haďa kai da ke a cuceni, a Aurawa Jalal wannan yarinyar dake kanki kinsam bata da cikakken Asali, meyasa baki yadda an
An aurawa ďanki ba se nawa ďan, wannan yarinyar mara mutunci akan me? Sumi2 da ita kamar ta Allah amma tana bin ďana"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Onde as histórias ganham vida. Descobre agora