ABDUL JALAL 103

Começar do início
                                    

"to ko inyi musu magana a nemo miki magani?"

"A'a base kinyi hakan ba, A yanzu dai babu wani magani daze warkar min da wannan ciwon kan"

Suna cikin wannan mujadalar ne Anty ta shigo da tray din fruit a hannunta tace
"Jalila kuci Abincin mana, ga dangin baban Jalal can suna son ganinku kafin su tafi"
Nana tace
"Anty Jalila fa taki cin Abincin, wai kanta ke ciwo"
"Subhanallah har yanzu kan ke miki ciwo? To daure kici Abincin se a kira likita ya dubaki"
Da kyar Jalila ta cakali Abincin nan ta barshi.

Suka fito parlour inda dangin Daddy keson ganin Amare, se hausa suke suna hadawa da yarensu, sunga fuskar Nana yayinda Jalila ta dukunkune a mayafi taki bari su ganta, dare ya farayi sukayi musu nasiha da Addu'oi, tareda jadadda godiyarsu ga Jalila sannan suka watse a hankali.

Dakin da'aka bawa Su Jalila yana da kyau da matukar girma, suka koma suka canza kaya, Hajiya Salma da kanta ta kawowa Jalila magani ta sha, tana shan maganin ta nemi guri ta kwanta tayi lamoo akan gado, tana missing din wayarta, tun randa Jalal ya kwace be kuma bata ba, tana son tayi amfani da wayarta amma ya rike a gurinsa sekace shi ya saimata.

Nana na kwanciya Mahmud ya kirata a waya, Suka dinga hira suna soyewa, kaman ba gobe zasu tafi ba, suna ta soyayya gwanin sha'awa, Jalila ta tuna kowacce a cikin 'yan uwan ta ta samu zabinta, ta auri wanda take so suna cikin farinciki amma banda ita, an haďa ta da wanda be damu da kansa ba ma balle wani, take taji wasu hawayen na zubo mata, ta tabatta Auren Jalal wani sabon shafi ne na kaddarar Rayuwarta.

Hanan kam gidanta yana da girma amma ba can ba, Amma ya tsaru anyi masa gini na zamani, dauke da wadataccen gini, an kashewa gidan kudi sosai, Sannan daddy ya zuba mata kaya yadda yakamata.

Wanda sukayi wa Hanan rakiya suna zuwa a ranar suka juyo gida, suka barota tanata rikici, Seda kowa ya watse bayan sallar magariba sannan Jawwad ya shigo gidan, ya sameta tayi zaman dirshan a kasa ta jingina da gado, ta takure kanta sosai, tayi kuka harta gaji, dan girgiza kai yayi ya karaso gabanta ya tsuguna se kamshin turare yake, A hankali yace

"Haba Hanan, kukan ya isa haka, i know you miss home, Amma ba gani ba, sekace wadda akayiwa auren dole, ko kin dena sona ne?"
Girgiza masa kai tayi alamar A'a

"Yawwa my love 😍, kukan ya isa haka, yau ranar daza muyi farinciki ne, kar kanki yayi ciwo, ko nima kina so ki sani kukan ne?" ya fada yana goge mata hawayen fuskarta.

A hankali tace "A'a ni karkayi kuma nadena kukan" tai maganar cikin shagwaba

Murmushi yayi mata yace "Yawwa ai nasan baza kiso ki ganni ina kuka ba, shiyasa nima bana son ganin kukanki"

Haka ya cigaba da rarrashin ta har ta dan saki jiki tana hira, Jawwad da kansa yaje kitchen ya dakko plate da cups, ya bude musu kazar da ya shigo da ita, ya cika mata kofi da youghut me sanyi, yace "Bismillah"
Ta kalli kazar ta kalleshi tace
"Ni na koshi"
"me kika ci da kika koshi?"
"bakomai" ta bashi amsa, ya lura gaba daya a firgice take, har hakan yaso ya bashi dariya amma ya maze ya ďan bata fuska yace

"in baki ci ba, zan kwana da yunwa ne, kuma ni inajin yunwa sosai, tunda aka fara biki bana samun cin Abinci fa, se Ulcer ta kamani ko?"
Yai maganar a ďan shagwabe, dariya ya bata tace

"in Ulcer ta kamaka ba rabin zamce ai, Dama haka ka iya shagwaba, wallahi tayi maka kyau"

tai maganar tana dariya, cikin hikima yanayi ya namata hira ya dinga bata kazar tana ci, seda suka kammala, Jawwad ya jagorance su sukayi Sallar nafila, domin nuna godiyarsu ga Allah da kuma fatan zaman lafiya me dorewa a cikin Rayuwar Aurensu.
Se Hamma take tana lumshe ido, da alamun gajiya da kuma bacci a tareda ita, Jawwad ya kalleta yace

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Onde histórias criam vida. Descubra agora