"Shikenan in an nagama zan maka magana se mutafi tare"

ta dan kumayin shiru tace "A'a idan na koma gida zanci Abinci, bazan iya cin Abinci yanzu ba, in aka tashi zan maka magana"

Ta kashe wayar, tana juyowa gabanta ya fadi, Jalal ne a tsaya a bayan ta, ya kura mata ido ko kyaftawa ba yayi
Dan tsayawa tayi itama tana kallonsa, tunda yazo ko sannu bata hadasu ba, ba karamin kyau manyan kaya sukeyi masa ba, gashi gaba daya ya cika gurin da kamshin turarensa, tayi kokarin bin ta gefensa ta wuce, ya kara tare mata hanya, dagowa tayi tana kallonsa ya hade rai kamar be san meye dariya ba yace
" Zoki wuce mu tafi"

Tai masa kallon ban gane nufinka ba tace "Kamar ya, mu tafi ina?"

"ban sani ba, ki wuce mu tafi nace" yayi maganar cikin fushi"

Zumbura baki tayi, tace

"Wallahi ba inda zani ba'a gama ba"

yasan halinta da taurin kai, dan haka yasa hannu ya janyo ta har tana kokarin faduwa saboda takalmin ta me tsinine, ba shiri tabi shi be tsaya da ita ko'ina ba se gaban motarsa, ya bude motar yace
"Shiga"
ta kalleshi, cikin muryarta me sigar shagwaba tace
"meyasa zan shiga? Ina zaka kaini kowa yana can ana abun Arziki"

"Wallahi in baki shiga ba zan sakaki da kaina"

Zare ido tayi ta kalli idonsa, babu alamun wasa a abunda ya fada tabbas ze aikata, ba shiri ta shiga motar, ya za gaya ya shiga ya kunna motar, yafara tuki cikin nutsuwa ya bar harabar gurin, yafara tukin kenan aka kirashi a waya, ya daga wayar yasa a hands free, da'alama abunda ya shafi aikin suke tattaunawa shida wanda ya kira shin, dukda zuciyarta a kule take da haushi, Amma bayan ya gama wayar tace
"Ya Aikin kuwa?"
Kamar jira yake tayi magana yace

"ban sani ba, bakida kunya, saboda ke na tafi aikin nan for almost four months baki nemeni ba, Rayuwa ta kaman wanda yake cikin rijiya ne yake neman taimako, kin mikomin abu ina kokarin fitowa kin saki nakoma ruwa, dan kinga ina lallabaki kikemin wulakanci ko? "

" ni wani wulakancin nayi maka? Mekake so in maka kuma? In cigaba da bibiyar ka mahaifiyarka tana min kallon mazinaciya? Da kazo garin nan kana kallona shekaran jiya, har kusa faduwa nayi saboda dalilinka, ko kallona bakayi ba, so kake inta binka, kokuma goyaka zanyi? Ni kawai ana can ana Ta shagali nikuma ka dakko ni, duk gurin nan nika dai na tsole maka ido, ga Ahmad ma yana jirana, yanzu se yayi ta jirana, idan ya tarar bana nan bazeji dadi ba"

ya lura gaba daya a fusace take, yai mata shiru taita mita, yadda Jalila ke kuma fadar Ahmad yafi komai bata masa rai, dan haka yaja wani uban birki a kan titi da seda ta firgita, ya juyo yana kallon ta.

ya matso da fuskarsa daf da tata, har suna jin numfashin juna, Jalila najin saukar numfashinsa a fuskarta, gaba daya Jikin Jalila ya hau rawa, taji numfashinta na kokarin tsayawa, gaba daya kamshin turarensa ya cika mata hanci, ga kuma wani mugun kwarjini da yayi mata, cigaba da matso da fuskarsa yake daidai tata, har dogon hancinsa na shirin taba nata tamkar me shirin sumbatarta, rintse ido tayi sosai jikinta na cigaba da rawa.
A hankali ya dauke fuskarsa, yace mata
"stop shivering, kina tunanin wani abun zan miki? Ba abunda zan miki, sedai ina kokarin nuna miki illar shigar da kikayi ne, look at yourself,"
Jin abunda ya fada, Yasa A hankali ta bude idonta tana cigaba da sauke numfashi.
Ya kuma kallon ta yace

"kalli jikinki babu mayafi, kin hau stage kina Rawa, kowa ya zubo miki ido kina rawa, kalli jikinki, kalli yadda kayan nan suka matse ki, hakan ya dace? "

Kallon kanta tayi, taga yadda rigar ta zauna a jikinta, taga irin yadda Jalal yasata a gaba da kallo, gaba daya seta ji kunya ta kamata, Amma ta maze ta dake, takuma hade rai tareda dauke kanta tace

"Ai dai bahaka na keyi ba, dan dai yau daya, ana biki zaka wani takuramin, naga kai da gajeren wando kake yawo a layi, waye ya dameka?"

Jalala seyayi kamar besan dashi take ba, ya fuskanci rigima takeji, idan ya biye mata fada za suyi a titi, banzan da yayi da ita, hakan ba karamin batawa Jalila rai yayi ba, wayarta ta fara ringing, tasa hannu ta ciro wayar daga jakarta, ta daga wayar tasa a kunnenta, beji me aka ce ba, sedai Jalila cikin shagwaba tace

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now