Gajiya Jalila tayi da zaman tunanin ta mike ta tafi cikin gida, Nana tana zaune a palour suna waya da Mahmud,
"Nana waike dan Allah ba kya gajiya da wannan wayar ne? Kuyita surutu tun ana fadar gaskiya se an koma fadan karya"

Nana taki kula ta seda ta gama wayarta sannnan tace

"waike Baby an gaya miki kowa irin kine me tsarin tsiya, ke yadda ba kya son yawan waya kowa ma hakane, ai a rana inji muryar Mahmud sau hamsin bazan gajiba, musamman mu da muke distance relationship, ai Ahmad din nan ma ban wani yadda kina sonsa ba"

"Inasonshi sosai, amma hakan bashi ke nufin a dinga uzzuramin da surutu ba"
"Hajiya Jalila, kyaji da shi dai"
Hanan ca ta kira Jalila a waya, ta daga tasa a kunnenta
"hello Baby, 'yar uwata rabin jikina ashe Family dinmu daya Baby? Narasa inda zan sa kaina dan farinciki, dazu Abba yake gayamin kuma wai an kawo kudin Aurena da Haidar, Baby na rasa me zanyi dan farinciki"
Murmushi Jalila tayi tace "na riga ki ji ai, kiyi Azumi ki godewa Allah"
"queen na rasa inda zan saka raina dan farinciki, daddy yace zasuzo karbar kudin Nana, narasa yadda zanyi dan murna"
"haka Al'amarin ubangiji yake Hanan, yana juya komai yadda ya so"
"Hakane Queen, amma naji haushi da baza'a hada da nakiba, ni ina Jalal ne ma?"
"yaje interview din nan ai, an turashi lagos zeyi wata uku"
"Allah sarki bawan Allah, wallahi Jalila bana kaunar Aurenki da Abokin Yaya Yusuf din nan, in duniya da gaskiya Jalal ya kamata ki Aura"

Wani dogon tsaki Jalila tayi ta kashe wayarta, dan bata son Hanan ta bata mata rai.

Jalila ta mike har zata bar palourn taga Maama tazo ta wuce kitchen, gaba daya Jalila bata jin dadin yadda kowa ya fita harkar Maama, dukda abubuwan da Maaman tayi mata, Akwai lokutan da ta kyautata mata, dan haka taga be dace ta mata hukunci da laifin da take mata ba, dan haka tabita kitchen din, Maama na kokarin kunna gas Jalila tayi maza taje ta karbi lighter tace

"Maama kawo in kunna miki, me zaki dafa?"

"barmin Abina zanyi"
"A'a Maama, tunda ba abunda nake ki barshi in dora miki"

Jalila ta karbi lighter ta kunna gas, dan jimm Maama tayi tana Kallon Jalila, yadda Jalilan ke Acting kaman Maama bata taba yi mata wani abu na bacin rai ba.

Jawwad suka isa airport yayiwa Jalal Sallama amma ya amsa masa a ciki, sam baya walwala, yasan halin Jalal baya son takura, tunda be niyyar gaya masa meke damunsa ba, ya ja Akwatinsa yayi gaba yabar Jawwad.
Haka Jawwad ya taho yanata tunanin me akayiwa Jalal yake wannan bacin ran haka?

Bayan Jalila ta gama yiwa Maama girki, ta koma daki, ta dauki Alqur'anin nan tana ta jujjuyawa, Kamshin turaren Jalal yakeyi, hakama dan teddyn ta, tasa hannu ta ta dinga duba Alqur'anin nan page by page, amma sam bata ga komai a ciki ba, kodai Jalal dama yana son raina mata hankali ne kawai?
Shiru tayi ta tuna yadda taga yanayinsa bayan ya gansu tareda Ahmad, Fuskar nan tasa a daure babu alamun sassauci, tayi shiru ta cigaba da zancen zuci, ;yanzu ze tafi lagos bashi da kowa a can, babu me kula dashi, Allah kadai yasan meze aikata,
"kinfi so in cigaba da shaye2 na ko? Ke Garkuwa ce a gareni" ire iren wannan maganganun nasa da Maganganun Antynsa da take gaya mata tabata amanar Jalal ne yasa take tunanin Anya hukuncin data yanke yayi dai2 kuwa?
To Amma nikuma mutuncina fa? " gaba daya ta rasa me yakamata tayi? Yanzu tana gayawa Hanan, tasan Hanan zata canza mata magana tafara kawo wani abu daban, dan haka tabar Abun a ranta ta cigaba da Yiwa Jalal Addu'a.

'yan kwanakin nan sam Abba ya dena shiga harkar Maama, har gara Jawwad ma yana zuwa gaisheta, Nana kuwa seda Jalila tasata a gaba ta nuna mata be dace ba abunda take yiwa Maama, wannan abunda yafaru tsakanin ta da Abba ne da kuma' yan uwan ta, sannan ta samu Nana ma take shiga sabgar Maaman, Abba ya gayawa Maama ranar Lahadi zasuyi baki, za'a kawo kudin Auren Nana, abakin su Nana taji batun haduwa da 'yan uwan Abba a Bauchi, ba tayi mamaki sosai ba jin ance su Hanan' yan uwansu Abba ne ba, sakamakon matukar kamannin dake tsakanin Jalila da Hanan, sedai taji haushin rashin sanar da ita da Abba beba.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now