Abba yace "Hakane, Amma zangaya maka wani abu, inkaga zaka bawa Jawwad 'yarka a haka to shikenan, inkuma kaga baze yuwu ba semu hakura"

Daddy yace "ina jinka fadi muji"

Abba yace "kaga maganar gaskiya a yanzu a bangaren mahaifi Jawwad bashida kowa se Allah sekumani, sedai bangaren mahaifiyarsa, banida wa bani da kani, kani na ďaya shine mahaifin Jalila kuma Allah yayi masa rasuwa tun Jalila nada shekaru biyar, kuma daga ni har mahaifinta babu wanda yasan suwaye dangin iyayenmu sakamakon suma gudun hijira sukayi daga garinsu, in kana ganin zaka iya bashi 'yarka a haka shikenan"

" Haba Alhaji Usman, Ai Jawwad ko ďan tsintuwa ne babu abunda ze hana in bashi' yata indai yana sonta, yanada hankali ga nutsuwa da tarbiyya wannan ba abun damuwa bane ba, bari muje ku gaisa da Mahaifiyata semu karasa gidan Yayana, shi ze karbi kudin Auren"

Abba yace "Nagode kwarai da wannan karamcin naka general, Allah yasaka da alkhairi"
Daddy yace "tsakanina da kai babu batun godiya, bari muje".

Jalila takoma gida ta fara baccin dole saboda azabar zugin da hannunta yakeyi, se kusan la'asar ta tashi, shima hayaniyar Naja ce ta tasheta dayake ita Naja wani lokacin kaman banza haka take bata magana a hankali, ga hauma hauma kamar rainon gabuwa, wannan hargowar ce ta tashi Jalila.

Sannan da alamu har yanzu Maama bata gaya mata sakon Abba na tabar masa gida ba, dan har yanzu tana giginta da rawar kai, Jalila ta tashi tayi sallar la'asar tanemi abun zubawa a cikinta.

Shikuwa Jalal tunda yaje ya sha giyarsa yayi tatul wani nannauyan bacci ne ya kwashe shi be farkaba se magariba, ya shiga yai wanka yai sallolinsa, bayan ya idar ne ya dau wayarsa yakuma kiran Jawwad, wannan karon Jawwad ya dauka Jalal yace

"wai dan Allah ina ka shiga ne haka? Tun safe ban ganka ba, na tambayi kanwarka tace bata san inda kake ba"

"Aiba bata nayi ba, kuma ba saceni akayi ba kaganni tareda Abba muna Bauchi"

"Bauchi kuma? Me ka keyi a Bauchi?"

"bazaka gane ba, sena dawo kawai akwai Labari"
Murmushi Jalal yayi, yadda yaji muryar Jawwad yasan yana cikin farinciki, Jalal yace
"To seka dawo din, amma tafiya ba sallama haka?"

"Nima ban san da tafiyar ba, babu shiri Abba yace inzo mutafi"

"to shikenan Allah yadawo daku lafiya"
"Ameen ya Allah" sukayi sallama
Bayan sunyi sallamane Yusuf ya shigo palourn daddy, Sallama yayi suka amsa gaba daya, Yusuf ya kalli Abba ya durkusa ya gaisheshi ya amsa masa cikin sakin fuska, ya juya ya kalli Jawwad ya mika masa hannu suka gaisa.

Daddy yace "Yusuf ga Abban Jalila fa"
Murmushi Yusuf yayi yace "Ai ina shigowa jikina yabani, ina kallonsa naga akwai alakar Jini, wannanne yayanta kenan sirikinmu"

Daddy yace "ya akayi kasani?" Yusuf yace

"Kai daddy yadda yarinyar nan ke fadarsa, ko kunya ba taji ranar inajinta itada Nawwara (matarsa) tanata yabonsa hada yi masa waka, kaf estate din nan ba wanda besan haidar ba ko ince Jawwad"
Gaba daya sukayi dariya, Yusuf yace

"ďan uwa Allah yabaka wuyan ďauka, dan wallahi Autar daddy fitinanniya ce, ga yarinta a cikinta" haka sukaita taba hira Yusuf yajanye Jawwad suka fice zuwa bangaren Inna.

Suka shiga da sallama, kamar kullum tana kan darduma tana lazimi, suka zauna a gefe suna taba hira harta idar, sannan ta juyo ta kallesu dan kura musu ido tayi, Jawwad yace "Sannu Inna"

"Yawwa ďan nan, Yusuf wannan kuma ina ka samoshi, kar in fadi wani abu ace nayi rikici"

Yusuf yace "Inna Yayan Jalila ne"
Murmushin fuskarta ya faďaďa sannan tace

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now