idon Jalila yayi jawur dan kuka, cikin matukar bacin rai da masifa Jalila tace
"Naji nakuma yadda kinfini iya tashanci, tunda kin tsotsa a Nono mana, nagode Allah har mahaifina ya koma ga mahallicinsa ba'akamashi da 'yar waniba, naki uban fa? Shekararsa biyar a prison da kyar aka karboshi, tashanci gashi nan ke kinayi yayarki da ďan uwanki nayi, sannan kinfini tashanci nikuma nafiki kai da iya wasa da hankali, ki kiyayi ranar dazan miki tonon silili, kuma Aure ne da yardar Allah baza' ayi shiba, saboda nagama shirina akanki, lokaci kadan ya rage kifada tarkona"

Nana data fito daga kitchen bata taba jin wannan labarin na mahaifin Su Naja ba, ita kuma Naja daskarewa tayi a gurin dan mugun mamakine yakamata, dan ta girmi Jalila kuma tun kafin a haifeta abun yafaru bakowa yasani ba, Amma ita ya akayi tasani.

Jalila tuni ta shige daki, ta nufi bandaki ta dauro Alwala tazo ta hau sallaya tafara gabatar da sallar magariba.

Jalal yanata rarrashin Jawwad
"Jawwad tun asalinka me biyayyane da hakuri ba kamar niba, dan Allah kayi hakuri ka kwantar da hankalinka, kasan iyayenmu mata daukar ziga baya musu wahala, ka kwantar da hankalinka kayi hakuri"
Wata irin Ajiyar zuciya Jawwad yayi yace

"Jalal Abunda yafaru naji babu dadi, amma abunda yafi batamin rai halinda wannan marainiyar Allah ke ciki, Jalal hakurin Jalila yakai a yaba mata, duk fitinarta tanada kawaici da hakuri, kuma tanada biyayya, duk abunda Maama take mata bata taba nuna mata bacin ranta ba, akan Jalila nasan Abba ze iya rabuwa da Maama, amma bata taba gayamasa abunda ke faruwa ba, Jalal inajin tausayin yadda rayuwar Jalila ke kasancewa daga wannan se wannan, nasan yau kwana zatayi kuka, kuma Jalal abunda Ilham tayi bata kyauta ba, be kamata tayiwa Jalila hakaba, son zuciya ba halinta bane"

"Nasani Jawwad, komai zezo da sauki zan dau mataki akan hakan, kaji ka kwantar da hankalinka"

"Shikenan Jalal, ka shirya jibi Insha Allah zamuyi tafiyar nan"
"Allah ya kaimu"

Jawwad ya amsa masa da Ameen, Jalal ya tashi ya fito, a harabar gidan yaci karo da teddyn Jalila da sweet dinta a kasa, yasa hannu ya dauka teddyn ya tafi dashi.

Bayan Jalila ta idar da salla, Nana tace "Jalila dan Allah meya faru kikewa Naja wannan maganar? Abun yabani mamaki ni bantaba jiba fa, kodai fushi ne yasaki"?

Jalila idonta Jawur ta kalli Nana tace "Nana duk bacin raina banawa mutum kazafi, kuma bana gori yauma raina ne ya kai makura a baci, sannan ba karya nayiwa mahaifin Naja ba, kuma na fada ne kozan samu sassauci akan bakanta min da ake, kullum aka tashi gori sedai ace uwata Arniya, kawai saboda...... Kasa karasawa tayi, maganar ta sarke saboda kuka

"Am really sorry sister, i feel your pain nasan ba dadi abunda yake faruwa dake amma kiyi hakuri dan Allah"
Wayar Jalila ce tafara ringing Ahmad ne Amma bazata iya dagawa ba ta kashe wayar.

Jalal na zuwa gida ya ajiye teddyn Jalila akan gadonsa ya tafi cikin gida, a palour ya tarar da Mummy amma ya shareta ya nufi dakin Ilham, tana kwance akan gado tana chatting ya fado dakin, zumbur ta mike zaune dan tasan indai taganshi a dakinta toba Arziki, ya kureta da jajayen idonsa yace

"Tambayarki zanyi, idan kikamin karya sena shakeki, yaushe kika kaiwa Jalila kudi tabawa Maama?" hade rai tayi
"Na kaimata kudi, nace ta ajiyewa Maama inji Mummy"
"karya kikeyi"
"niba karyanake ba"
"zan tattakaki wallahi, karya kike"
"wayyo Allah mummy, kizo ki temakeni" ganin tana ihu ya harzuka Jalal jikinsa yafara rawa ya janyota daga kan gadon ya zuba mata mari
"Nizaki rainawa hankali? Ni zakiyi wa ihu uban me nayi miki?"
Mummy kam a sukwane takaraso dakin
"lafiya meye haka metamaka?"
Banza yayiwa Mummy yace

"waike wace irin dabbace ne? Ranar akan idona kike soke kudi a jikinki, naganki da idona amma saboda baki da mutunci kin dorawa yarinya kinsa se kuka take, wace irin zuciya ce dake haka?"
Se yanzu Mummy tagane inda ya dosa dan haka tace "to mara mutunci, dama saboda waccan yarinyar kazo kake wannan zare idon kake kokarin shaketa, kaji kunya wallahi ka fifita wata banza can bare akan 'yar uwarka"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now