"Ba sharri tayi maka ba Jalal, gaskiyane" juyowa yayi inda daddy ke magana, nan da nan idonsa ya canza ya harzuka matuka yace

"daddy da bakinka? Kaima ka yadda zannemi matan banza? Ka yadda ni Jalal zan kawo karuwa cikin gidan nan? Ka yadda ni Jalal ina neman matan banza, lalacewata bata kai haka ba" daddy yace

"Ya isa Jalal, ba sharri akayi maka ba, ni yarinyar tasamu a waje tace gurinka tazo, ita tacemin Akwai alakar dake tsakaninku wadda bata kamata inji ba, kuma lallai insaka Aureta shine kawai hanyar tsira da mutuncinta da naka, ka gayamin meye hakan inba neman mata kake ba?"

Shiruu Jalal yayi ya marasa meze ce, mamaki gaba daya ya kamashi, a iya tunaninsa babu wadda zatayi masa haka, su Jeje ne kuma zuwa yanzu suna hannu kodai duk shirin Mummy ne haka? Amma a tunanin sa be cancanci daddy yayi masa wannan mummunan zargin ba, ba tareda yayi bincike ba ana alakanta shi da dabi'ar dayafi tsana a rayuwarsa wato zina.

"Shikenan daddy naji na gode, Jalal danka mashayi kuma manemin mata,
Daddy da ina neman matan banza da lalacewar da zanyi tafi haka, da ba tun yanzu ba matan banza sun dade suna zarya a gidan nan, dukda Jawwad yana rufamin asiri a abubuwa da dama bana tunanin ze yadda ya zauna da mazinaci, shikenan nagode amma kusani Wallahi bazan Auri wannaan shedaniyar yarinyar ba"

Mummy tace

"dalla rufemin baki, kai har kanada bakin dazakace bakason Ilham? Ba rufamaka asiri zatayi ba, kanada bakin kiranta shedaniya ka.....

"Enough Mummy!!! Karki kara zagina waye silar komai, natsani Ilham natsani me sonta" yakarasa yana Zazzare ido, daddy yace
"Jalal ya isheka haka, danme zaka dinga cewa ka tasani yarinya metayi maka haka? Lokaci yayi da yakamata kadinga dagawa mahaifiyarka kafa"

Jalal yace "Daddy kayanke min hukunci bakayi bincike ba, kasan bana maka karya, nidai fatana kayi bincike kadena zargina, daddy kanamin uzuri a abubuwa da dama ban taba zaton haka daga gareka ba, sannan maganar Ilham wani abune daba lallai in gaya maka meyasa nace bana sonta ba, duk ku kwantar da hankalinku Insha Allah a satin nan zanbar muku gidanku, in bar muku kasarma gaba daya ku huta"

Ya juya a mugun fusace yafito daga part din daddy, gaba daya jikin daddy yayi sanyi tausayin Jalal ya kamashi, ya juya ya kalli Ilham yace "Ilham mekika yiwa Jalal ne yake miki haka?"
Ilham cikin kuka tace "daddy ni bansan menayi masa ba, yakemin wannan muguwar kiyayya"
Mummy ta dinga rarrashin Ilham.

Jalal kam tunda yafito yaji wani abu ya tokare masa kirji, dakin Jawwad ya tafi yana zuwa yatarar da Jawwad kwance akan gado ido a rufe, Jawwad yana kwancene zuciyarsa ba dadi yarasa yadda zeyi da matsalar ke damunsa, jin Jalal ya shigo ne yasa Jawwad ya bude ido, ya tashi zaune ya dake ya boye tasa damuwar ya kalli Jalal yace "Lafiya kuwa naganka haka meya farune?"

Kasa magana Jalal yayi, sedai jijiyoyin kansa da suka mimmike idonsa jawur, se huci yakeyi kai dagani kasan akwai damuwa sosai.
Jawwad yace
"ka gayamin mana meke faruwa?"

"Jawwad zan nemi visa, dole zan bar Nigeria a satin nan, kuma wallahi na tafi bazasu kara ganina ba"

"meyasa Jalal, meyasa zakace haka?"

"Jawwad nagama yanke hukunci, wannan karon karka cemin komai dan mutuwa ce kawai zata hanani tafiyar nan, zan bar Nigeria idan na tafi wallahi bazan kuma dawowa  ba".

A kwanakin nan sam Jawwad be gayawa Jalal shikuma tasa damuwar ba, sedai kokarin lallaba Jalal dayake yayi hakuri ammma fafur yaki se shirinsa yakeyi, sannan sam yadena shiga gidansu ya kashe wayoyinsa dan karma anemeshi.

Hanan da Jalila suna zaune suna hira da Inna a dakinta, Hanan tanata chatting ta dan dago ta kalli Jalila tace

"queen Haidar baya daga waya lafiya kuwa?" tai maganar a shagwabe
Jalila tace
"kunfi kusa ai, nima bamuyi waya ba"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now