"Madam ba magana? Ko gajiyar ce?"
Hannaan tac
"kai ba'a magana nagaji kam" dubawa yayi yaga Jalila a motar, kafin yayi magana Abdallah yaja motar zuwa makekiyar harabar dake cikin gidan, Abun yabawa Jalila mamaki bayan sojojin dake bakin gate akwai wasu a cikin gidan, Hanan tafara fita sannan Jalila dukda magariba tayi, amma ko ina hasken fitulu ne, Jalila ta bude motar ta sakko, ga mamakin ta gaba daya idan mutanen dake harabar gurin yadawo kansu, harta dan fara tsarguwa, Abdallah ya bude motar yana janyo kayansu.
Abdallah ina kasamo wannan kuma? Ko dama Hanan tanada sister ne? Suka dinga jerowa Abdallah tambayoyi, Hanan ta kalli wani soja tace Phillips ga kaya nan shigo dasu upstairs taja hannun Jalila suka shige cikin gidan. Gidan shiru se kamshin turare da Abinci dake tashi, gidan shiruu wani tangamemen palour suka shiga, tundaga palourn Hanan take kiran "Anty fiddo, kina inane?" wata matashiyar mace ce wadda bazatafi shekaru Ashirin da biyar ba ta fito tana cewa

"Hanan wane irin kirane haka, Salla nakeyi ai yau kinzo kowa se san kin iso wannan ba.... Bata karasa maganar ba tayi shiru, ganin Hanan tareda Jalila, matar tace
"Hanan menake gani haka, ina kika samo wannan me matukar kama dake?"
Jalila tai murmushi tace "ina wuni Anty"
Hanan tace "daga zuwanmu kin isheni da tambaya, ina mutan gidanne?"
"suntafi shirye shiryen biki, anjima maybe kiga sun shigo" ta kalli Jalila tace "Sannu da zuwa baiwar Allah, shigo"
Hanan tace "aiba gurinki tazo ba, innancy tana dakinta ne?"
"Hanan ko kara babu, tana daki tana salla" Hanan taja hannun Jalila zuwa wata kofa, dakine me dauke da katuwar katifa da tv da bandaki da komai a ciki, gefe wata dattijuwace sanye da hijjabinta tana salla, daga imda Jalila take tana iya ganin dattijuwar fara ce tas daganinta kasan tana hutawa amma Jalila gani take kaman ta taba ganinta amma ta manta a inane.
Hanan tace "Shugabaa Inna salla ake tayi ne? Jalila ga toilet nasan zakiyi Alwala bari in dawo" Jalila tace to, koda Jalila ta shiga cikin toilet din shima ya hadu, kaman ba na tsohuwa ba, Jalila tai alwala ta fito harta tada salla tsohuwar bata idar ba.
Koda Hanan ta fito se tambayoyi suke mata ina suka samo Jalila, Hanan tace "Anty fiddo kimfiye tambaya wallahi"
Abdallah yace "kusan shekarunsu takwas kenan a tare, yarinyar da daddy yake gaya muku ce yayi ya mekama da Hanan, itace yace zekawow Inna taganta"
Wadda suke cewa Anty fiddo tace "Masha Allah, sekace wadda taimana maganin Hanan ce, kai amma Abdallah bantaba ganin wanda ba yan uwa ba masu kama kaman Hanan da wannan yarinyar ba, bari in kaimata Abinci masha Allah ashe itace 'yar daddy"
Jalila ta idar da salallolinta a lokacin tsohuwar ta kammala nata lazimin, kurii ta zurawa Jalila ido, Jalila ta idar tazo kusada tsohuwar ta zauna tace "inna barka da yamma" kasa amsawa tayi sedai kallon Jalila da takeyi, Anty fiddo ce tashigo tareda su Abdallah, Inna ta daga kai ta kalli Hanan ta kalli Jalila tace "Haba nifa imce, nasan Hanan bata da wannan nutsuwar, amma ko idona neke ganin ba daidai ba, kamar duk Hanan dince?" tsohuwar kana jin yadda take magana kasan bafulatana ce, hausarta bata fita sosai
Anty fiddo tace "daidai idonki ke gani, kinga me kama da Hanan ko? Ita daddy yake cewa ze kawo miki ki ganta ai"
Inna tariko Hannun Jalila tace "mairo ashe dama kina raye zankuma ganinki, baki ganeniba, hafsatunki cefa? Allah sarki mairo ina kika shiga tsawon lokaci bamganki ba" sosai tsohuwar ta rike Jalila tana kuka, saroro Jalila tayi tana kallon Inna, Hanan tace "kekam Inna wai har yanzu bazaki dena wannan abun ba dan Allah?"
Abdallah yace "Inna idan mairon takice haka zakiganta bata tsufa kamarki ba, wannan fa yarinya ce sosai, bakuwarmuce kamar da takeyi da Hanan dinki yasa Daddy yace ze kawo miki ita ya nemi alfarmar mahaifinta alfarmar mahaifinta ankawomiki ita amma kina kuka"
Goge hawayenta tayi tace "yi hakuri yarinyata, daga zuwanki zanmiki shirme, zauna kusada ni"
Anty fiddo tacewa "Inna bari muje taci Abinci se adawo miki da ita" inna tace "ita ya sunanta ne? Ko itama Hanan din ce" Abdallah yace "sunanta Jalila"
"Kai wannan sunan da wahalar fada, na dauka itama Hanan dince ko mairo" Anty fiddo tace "Jalila taho muje" Jalila ta mike suka fito,
Anty fiddo tace "Kiyi hakuri haka takeyi wani lokacin haka takewa Hanan ma, wani lokacin setayi ta kuka wai Hanan tana abu kaman kanwatta, kumafa mu bamu san kanwartata ba, bawanda yasan inda take wata kilama ta mutu, amma har yanzu inta tuna setaita kuka"
Jalila tace "Allah sarki, kinsan babu abunda yafi dan uwa dadi duk tsufansa duk yarintarsa"
"Hakane kam"
Sun karrama Jalila sosai sukayi dinner sannan Hanan takai Jalila masauki, Jalila tace "Hanan bari inwa Inna seda safe ko?"
Hanan tace "inkikaje bazatayi bacci ba kuka zata cigaba, ki kyaleta seda safe"
"to shikenan, amma Hanan meyasa duk gidan nan naku sojojine, koduk saboda babanane?"
"Aiba daddy ne kadai soja a estate din nan ba, sannan duk wanda kika gani a estate din duk family dinmune, kaso uku bisa biyu na mazan dake estate din naan sojoji ne shiyasa kikaga sojoji ko ina, yanzu gobe in Allah ya kaimu zan kaiki kigansu akwai yan mata kamanmu, amma basu san munzoba, da yanzu an cika part din nan, Inna itace tushen family din nan, duk yarantane da jikoki da yaran jikokinta, sekuma kanin mijinta shima ya rasu amma akwai yaransa shima da jikoki a cikin estate din nan, mijin inna ya rasu shekaru bakwai baya, amma bata tunanin sa kaman kanwar nan tata tanabamu labarin kanwar ta, babban dantane kawai ya san kanwartata, shima bashida wayo sosai lokacin amma haka wataran take birkicewa ta wuni kuka"
Jalila tai ajiyar zuciya tace "Allah sarki, tunda kika ga haka ba karamin shakuwa ne tsakanin ta da kanwar tata ba" sukayi ta hira sannan suka kwanta bacci, amma Jalila tana tunanin meyasa bata dakko Al'qur'anin nan ta taho dashi ba, tana son sanin me Jalal ya ajiye a ciki, ita tsawon lokacin da qur'ani yayi tareda ita bata tab ganin komai a ciki ba, to me Jalal yake nufi.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Donde viven las historias. Descúbrelo ahora