"Gaskiya Abdallah ka dinga jin tsoron Allah muka katse namu hirar kace mu fito kaikuma ka zauna"
Taki kallon inda Jawwad yake, balle yasaka ran zata kulashi, Jawwad ya karbi key din motar a hannun Abdallah yace
"muje in bude miki motar, Abdallah bashida niyyar tashi yanzu"
Dan murmushi tayi ta juya, Abdallah yace
"tasamu abunda takeso, dama ba dan Allah tazo nan dinba, sarkin gulma wani inzo in bude mata mota, kawai kice Jawwad yataso gurinsa kikazo, sewani Iyayi kike"
Hanan taji kaman kasa ta bude ta shige, Abdallah mugun dan rainin hankali ne Jalal yace
"Ahha kai Abdallah ina ruwankane? Yada shishshigi haka?"
Abdallah yace "Auto nayi shiru, tunda ka goyi bayanta"

Suna fitowa Hanan ta nufi hanyar komawa cikin gida, Jawwad ya kira sunan ta, ta tsaya amma bata juyo ba, ya karasa gabanta yana kallon ta amma ta sunkuyar da kai,

"Hanan, menayi mikine? Tunda kikazo kin kula kowa amma ni kin shareni"
"Bakomai" ta bashi amsa
"Ban yadda ba komai ba, laifin menayi miki?"
"Haidar dan Allah ka kyaleni, banason matsala, kace baka sona, gaa nazo na tarar da wata tana gayamin ita zaka Aura ya zanyi? Ina kokarin in cireka a raina amma nakasa, ganinka din nan ma yana karamin pressure ne, na damu da kai sosai kai kuma ka nuna baka sona, base in hakura ba, mezesa incigaba da shishshige maka?"
Abun mamaki hawaye ke kokarin fita a idon Hanan, hakan na nuna maganganun da take fada har cikin ranta, Jawwad yace
"Zannemi wata alfarma daya a gurinki, zakiyi min? " yai maganar ƙasa 2
"Alfarma kuma? Wace iri"
"Sekinyi min Alkawari zakimin Alfarmar"
"Inkuma bazan iya bafa?"
"Bazan tambayi abunda bazaki iyaba ai, abune me sauki"
"To fadi in zan iya" yai murmushi yace
"Sonake inkuma jin sunan dakika kirani dashi please, yamin dadi"
Dan zumbura baki tayi ta noke kafada,
"Niba wani suna"
"Kince fa zakiyi min Alfarma" cikin shagwaba tace
"ni banyi Alkawari ba ai"
"Please, ko inyi kuka ne sannan ki fada"
"Eh to yi kukan in gani tukuna" sukayi dariya a tare, yanayin irin tsokanar Jalila haka Hanan takeyi, amma Hanan bata iya komai ba akan Jalila, Jawwad yace
"Hanan da bakina ban taba cewa bana sonki ba, ban taba soyayya ba, amma nasan ina son Jalila so ba na wasa ba, kinga akwai alaka me girma tsakanin ki da ita, sannan batun Naja da kikeyi Wallahi Hanan yanzu haka ina dauriya ne kawai, Naja zabin Maama ce, tanason in Aure ta ni inason yiwa Maama biyayya amma bana tunanin zan iya Auren Naja,
Hanan nasan kinshiga damuwa saboda ni but am very sorry, bana son kowani rai ya shiga damuwa saboda ni, ta mussaman ke ce a gurina"

Hanan tai murmushin da seda hakoranta suka fito, ta jingina da motar tace
"Kasan meyake kara burgeni da kai Haidar?"
"A'a sekin fada"
"A dukkanin maganganun ka kana kokarin fadar gaskiya ne, sannan kanada tausayi shiyasa nake kara sonka, Amma bari ingaya maka wani abu, alakar dake tsakanina da Jalila bazan so ta baci ba, saboda ina mata so na gaskiya, bazanyi wani abu in cutar da ita ba, Amma maganar gaskiya kanawa Jalila so ne irin na 'yan uwantaka ba soyayya ta Aure ba, haka ma zuciyar Jalila tana maka sone na' yan uwan taka, nasan zakayi mamaki, Jalila bata taba soyayya da wani ba, tanada Samari Amma har yanzu taki yadda zuciyarta akwai wanda takeso saboda taurin kanta, kaima zan baka lokaci zaka gazgata abunda nake nufi"

Gaba daya zuciyar Naja ta gaama tsinkewa, Ganin Hanan taki dawowa yasa ta fito harabar gidan, amma tayi tozali da Hanan da Jawwad se murmushi yake, tunda take da Jawwad maganar minti goma bata hadasu balle yaita wannan murmushin, Nana ma befiye shiga harkarta ba, a da tayi tunanin ko Jalila yake so, wato wannan yarinyar me girman kan bala'i ita yakeso, koma dai duka yake sonsu ne tana tsaye tana kallonsu
Jawwad yafara magana

"Hmm Hanan ina kika samo wannan ideology din, ya zaki ce Baby Akwai wanda takeso, kuma munayiwa juna son 'yan uwan taka?"
"Ban fada domin in shiga tsakanin ku ba fa, nawa hasashen ne haka, Ita kanta Jalila bata son wa take so ba, ba kowane e lokaci take yadda da zuciyarta ba tana karbar abubuwane da lissafin kwakwalwarta"
"Hanan ya akayi duk kika san Jalila haka ne?"
"Haidar a zaman danayi da Jalila motsi tayi nasan abunda take nufi, nasanta fiye da yunwar cikina"
kyar yake kallon Hanan ko kyaftawa bayayi yana juya maganganun ta a ransa, ganin yanata kallonta yasa tace

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now