"A'a ba daya, in kayi inma bakayi ba kanka kayiwa ba Jalila ba, Amma kaji tsoron Allah, kakiyaye dokokinsa sannan ka kulada ibada" ta mike jiki a sanyaye ta fito waje, maganganun da Jalal ya gayamata babkaramin bata mata rai sukayi ba, dukda taji zafin maganganun da Jalal yagaya mata, amma idan ta tuna itama abubuwan data dinga masa abaya setaga bata kyauta ba.

Daddy ya kalli Jawwad yace "Jawwad Abbanka kuwa yana gari ina son ganinsa" Jawwad yace "A'a Daddy be dawo ba tukuna yana lagos amma a satin nan ze dawo Insha Allah" daddy yace "Allah yadawo da shi lafiya, Yaww Jawwad naji Jalal yacemin ka kamalla Masters dinka last Couple of months ko?" Jawwad yace "Eh Daddy Alhamdilillah na kamalla, ina jiran sakamakone, atayamu da Addu'a" daddy yai murmushi yace "Kullum cikin yi muku nake? Kuma nasan da sakamako me kyau zaka fita Insha Allah, nasan yarona akwai himma ai, dama vacancy na samu, federal zata dauki ma'aikata a farkon sabon shekara anbani vacancy na mutum daya a babban branch din NNPC na Abuja, shine nace ka turomin CV dinka ta Email dina, inkuma zaka karo karatune kuma to, semuga yadda za'ayi kaje ko England ne can wajensu Mahmud ka karasa" shiru Jawwad yayi ya sunkuyar da kai yakasa cewa uffan daddy yace "Jawwad kona bata maka raine?" Jawwad ya girgigiza kai yace
"Daddy banida bakin yi maka godiya, tun ina karami kake dawainiya dani, amma ina tunanin dan uwana, daddy Jalal shifa me za'ayi wands za'a tallafawa Rayuwarsa" daddy yai ajiyar Zuciya yace
"Jawwad bana tunanin koda Jalal yanada dan uwa ciki daya ze nuna masa kaunar da kake masa, Amma Jawwad ba yadda zanyi ina za'adauki Jalal aiki a wannan halin da yake ciki, yana shaye2 baya son mutane, ga zafin zuciya kana gani ko mahaifiyarsa baya raga mata, anyi2 yakoma makaranta yaki " Inda na godewa Allah ko bayan raina Jalal yanada kadarorin da in ya tattala ze iya rike kansa, inkuma yabarnatar shikenan" Jawwad yace

"Daddy bazanyi musu da hukuncin ka ba, amma inaso Jalal ya samu makoma shima, koya koma karatu koya samu aiki, amma idan na tafi Aiki na barshi a wannan halin senake ga kaman banyi masa halacci ba, kuma shaye2 munmasa addu'a muna fatan ze dena very soon, tunda ya rage ba kaman da ba" shiru daddy yayi yana kallon Jawwad dayake magana idonsa taf Hawaye dake nuna hakikanin gaskiyar abunda yake fada har zuciyarsa.

"Jawwad kenan Allah ya dawwamar da haske a cikin Rayuwarka, gwagwarmaya da kaunar dakake wa dana banida abun biyanka, Allah yatemakeka ya baka abunda kake nema duniya da lahira"
"Ameen daddy" daga haka ya tashi ya fita.

Oga KB yana zaune yatasa Samira da wata katuwar bulala, da alamu jibgarta yagama yi, jikinta duk a kumbure dan fuskarta a kumbure gefen idonta yana zubar da jini, Oga KB yace
"Tun tsawon wani lokaci kike tareda Jeje?"
Cikin kuka tace "Ranar muka fara haduwa da shi" kafin ta rufe baki yakuma zuba mata bulala tareda fadin
"Karya kikeyi, munafuka zaki gayamin ko sena takeki na kasheki, matsiyaciya yanzu shikenan Sunana yagama lalacewa a idon duniya, nida 'yata a gidan karuwai, dana san irinki za' a haifamin da tun a ciki sena zubar dake, Wallahi idan Nagano wanda ya shirya min wannan manakisar sena kasheshi kowaye, ki gayamin tun yaushe kuke tare?"kokuma yanzu inkasheki da poison na kashe banza shedaniya"

Cikin kuka tace "Shekararmu biyar Tare dashi" zaro ido yayi "Shekara biyar amma bansaniba, Cigaba ina jinki se akayi yaya?"
"tun ina secondary muke tareda shi, bayan haduwa ta da Saleema, nasanshi ne ta hanyarta, daga baya yake nunamin yasanka, Yaronka ne akwai aikin dayake maka, duk lokacin danazo maka da bukata baka damuwa da bukatuna, kafi son faruk dani, kana cewa bazaka kara yadda da mace ba koda yar cikinka ce, nikuma bukatuna bakamin, umma ma bayimata kake ba, balle nima ina sa rai, shine Jeje yajani a jiki shine ya koyamin bin maza, yana baani kudi masu yawa sannan ya hadani da masu kudi Shida Saleema, Sau biyar ina zubar da ciki biyu duk nasane"

Wata irin zuface ta shiga tsatstsafowa Alhaji Kabiru mikewa yayi ya shake Samira yana fadin
"Samira anya kuwa nine Ubanki, kodayake a rina barewa bata gudu danta yai rarrrafe uwarkima karuwanci tayi ta tuba na Aureta, watakila bayan na Auretanma bata tuba ba"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now