Watan Jalal goma sha takwas, Khadija tasa Habib agaba tace tunda an hanata karatu a kasar waje ya nema mata Admission a Nigeria, bana gwamnati ba kuma ba a kano ba, Habib yana son khadija gashi mutum ne me matukar hakuri, dan a zauna lafiya yanema mata Admission a ABU Zaria, ba'asamu ba yace tabari wata shekaran se a duba mata, aamma taki yadda, taje ta nema a University na Lagos kuma ta samu, haka ta tsallake tabar dan tatsitsin jaririnta a hannun me raino ta tafi Lagos, a can idonta yakara budewa ta hadu da yaya da matan manyan masu kudi da suke kara huremata kunne, Labari yasamu mahaifiyar Habib cewar khadija ta tsallake ta tafi lagos karatu tabar Jalal, tasa akaje aka dakko mata shi daga kano.

Tunda Salma taje ta tarar da Jalal taji tana matukar son yaron sabida kaman an tsaga kara da Habib, dan haka ta dauke Jalal ta tafi dashi gidansu, wasu suka dinga bata da zuciya duk abunda Habib yaimata shine hada dakko dansa itakuwa ko ajikinta saboda tana son yara sosai, mahaifin Salma yayi murna da ganin takwaransa, ana nunawa Jalal gata a dangin mahaifinsa sosai, watansa biyu a Barno khadija ta dawo kano, ta tarar an dauke Jalal ta dinga bala'i, ga Habib baya gari dan haka ta shirya da kanta tafi maiduguri, taje tasamu maman Habib tace mata zuwa tayi abata danta
"da kinsan kina son dan amma kika tsallake kika bar yaro kamar wanna kika tafi lagos"
"Mama yama za'ayi in haifi yaron ace bana sonsa, inason dana mana, nidai abani abuna kawai" mama ta fuskanci idan tabiye Khadija zata iyamata rashin kunya dan haka aka kira Salma a waya tace tazo, ba dadewa sega Salma ita da Jalal, gaban Salma ba karamin faduwa yayi ba dataga Khadija, dan haka jiki ba kwari ta shiga palourn tana zama Jalal ya kalli Mummynsa yana nata murmushi, ba kunya khadija ta mika hannu zata dauke danta Jalal ya kwanta a kirjin Salma yaki zuwa, Salma tafara kuka tace "dan Allah mama tunda narasa Habib kisa baki abani Jalal" gaba daya suka juyo suna kallon Salma, a fusace khadija tace "lallai baki da hankali, in fitsari banzane meya hana ki haifa, inyi ciki inyi laulayi ga wahalar cs, ingama sekuma indauki dan inmikamiki, tunda gani sokuwa," ta fizge Jalal tayi waje abunta.
Mama ta dade tanajin zafin abunda Khadija ta aikata balle Salma da akafi ciwa zarafi.
Habib besan anyi hakaba, seda yaje maiduguri aka gayamasa abunda Khadija tazo tayi, ran Habib yayi matukar baci, betaba danasanin Auren khadija ba irin ranar, dayadawo kano, yaimata fadan dabata taba zaton ya iyashiba, sabida yayi fushi bana wasa ba. Satin khadija uku ta shirya Jalal ta tafi dashi lagos makaranta, Habib yabita har can ya karbo dansa yakaiwa mama yace ta rike Jalal.
Mama tace tana kaunar jikanta amma bazata iya karba ba, kar mahaifiyarsa tazo takuma cimata mutunci ya mayar mata da danta.
Tundaga abun nan da khadija tayi dangin Habib suka kara tsanarta, suka dena zuwa kano, suka tattara suka sakamusu ido.

Koda Habib ya dawo kano, se ya tattaro harkokinsa ya dawo kano, yasaka Jalal a day care, irin na manyan yaran masu kudi, idan takama ze tafi Dubai seya tafi da Jalal, Habib shikewa Jalal komai, Kusan koda yaushe zancen Jalal baya wuce "daddy yaushe mummy zata dawo, mudinga cin Abinci tare, ta dingayimin wanka"
Habib yana matukar jin tausayin Jalal, sam Yaronsa beyi dacen uwa ba inama ace Salma ce ta haifi Jalal ba khadija ba, wataran Jalal yadami Habib da koke2 ya daukeshi ya kaishi gidansu khadija, Jalal ya sake sosai a can sabida akwai yara gidansu kuwa dagashi se babansa seme gadi, koda Saudat taga Jalal take wani bakinciki yakara kamata, khadija nacikin dauka harta haifi yaro, kallo daya zakayiwa Jalal kasan dan hutune, amma ita ta barta bar yanzu tana gararanba. Seda Jalal ya kwana biyu a gidansu khadija sannaan Habib ya dakkoshi.
Har Jalal ya shekara biyar khadija bata gama makaranta ba, duk lokacin datazo hutu ya dinga kuka kenan, yana "mummy dan Allah ki tafi dani, koki siyomin baby mace mudinga wasa da ita" haka Jalal zesha kukansa, ya hakura itakuma ta tsallake ta koma.
Wataran Jalal yana tsaye a kofar school dinsu yana jiran daddynsa yazo ya daukeshi, yagaji daddy bezoba har yafara kuka, malamansu sunata rarrashinsa yakiyin shiru, seya hangi wani yaro a daya makarantar dake makotaka datasu Jalal yake, yaron yana zuwa yacewa Jalal
"meyasa kake kuka, matane fa suke kuka, uncle dina yacemin maza basa kuka" se Jalal yace masa "daddy na yaki zuwa ya daukeni, inaga shima yatafi gurin mummy ya banni anan" se yaron ya goge masa hawaye yace
"Zezo ya daukeka, amma kadena kuka, in Abbana  yazo daukana zance yajiramu in Abbanka yazo seya tafi dakai, in bahakaba zaka cigaba da kuka"
Suna nan zaune suna hirarsu ta yara, baban yaron nan yazo daukarsa, yaron yacewa babansa "Abba mujira Abban abokina azo a daukeshi inmuka tafi kuka zeyi"
Baban yaron yace to, yanemi guri ya zauna sukaita masa shirme, aka jima sega Habib yazo daukar Jalal, suka gaisa da baban wancan yaron, Jalal ya dinga dagawa abokinsa hannu.
Tundaga ranar kullum aka tashi daga makaranta seyaje gurin abokinsa Aliyu Jawwad, suka fara sabawa sosai ya kasance koda weekend's Jalal yana takurawa Daddynsa shidai ya kaishi gurin abokinsa. Seda daddy yanemo gidansu Aliyu dayake sun fara sabawa da baban Aliyu, saboda duk lokacin da'akazo daukar daya se ya jira anzo daukar daya a haka aka saba, Habib dakansa yake Jalal gidansu Jawwad, ranar da babu makaranta tare suke wuni, hakan yafara ragewa Jalal kewar mahaifiyarsa, yakasance in Jalal baya gidansu Jawwad to Jawwad yana gidansu Jalal, Habib ya roki baban Jawwad dayanaso ya hade musu makaranta saboda yaga Jalal yanason Jawwad sosai, da kyar baban Jawwad ya yadda. Wataran Jawwad yana gidansu Jalal, kanin mahaifin Jawwad dayatafi service yazo, koda yatarar  Jawwad baya nan aka gayamasa inda yake, yayi fada sosai yatafi har gidansu Jalal da nufin ya dakko Jawwad, amma yanayin yadda yagansu, da kukan da Jalal ya dingayi yasa ya kyaleshi, tundaga nan shakuwarsu takara karfi, koda khadija tazo hutu ta tarar da Jalal da Jawwad taji dadin yadda taganshi, baya takuramata da kuka yanzu ya maida hankalinsa kan Jawwad. Jalal najin dadin Rayuwar gidansu Jawwad sabida yara suna shiga suna fita yanasamun abokan wasa, ga kakar Jawwad mutuniyar kirki suna matukar sonta, saboda duk wani shirmensu tana biye musu.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now