Antyn Jalal ta kalli Jalila data tattara duk wata nutsuwarta kaman tana daukar karatu tace
"kinga rana tayi, shabiyu takusa, kuma da azahar zamu koma maiduguri, zan kara takaita miki labarin nan dannima bakomai nasani ba, Amma kinsan meyasa khadija tayi nasara ta kwace mijin Salma?"
Girgigiza kai Jalila tayi
"Salma ta zurawa Habib ido tana ganin kaman yadena sontane, maimakon ta tashi tsaye tayi fighting ta gwada masa soyayya, ta kwaci mijinta, seta karaya da wuri tana ganin kaman bazata iya kishi da khadija ba tafi karfinta, ta zuba musu ido"
Haka rayuwa tacigaba, seda Khadija ta zubar da ciki kusan hudu Habib be saniba, data fuskanci tasamu ciki setaje ta zubar, daga karshema taje tai planing hankalinta kwance ba wanda yasani, tacigaba da cin amarcinta, yau suna wannna kasar gobe suna waccan kasar, khadija tayi duk me yuwuwa takara farraka tsakanin Habib da Salma baya Jin maganar kowa se khadija, khadija yar kwalisa ce yar gayu, ta iya gayu ga girki da iya magana, yanzu zatayi laifi amma take zata mantar dashi duk wani laifi datayi, seda khadija ta shekara uku tana cin duniyarta da tsinke ta taka wanda takeso duk meson wani abu a hannun Habib seya biyo ta gurinta, Salma kam yau da lafiya gobe babu saboda bacin rai kullum cikin guma mata khadija take, duk wani abu datasan zatayi ta bata mata shi takeyi.  Sedai ta shiga daki tayi kuka.

A yan shekarun nan Saudat haka takeyinsu ba walwala tayi iya tunaninta taga hanyar dazata rama abunda Khadija tayi mata amma takasa samu, kuma tayiwa kanta Alkawarin kozata mutu wajen daukar fansa setayi, zata nunawa khadija ba ita kadai ta iya makirci ba, zata rama inda babu wanda ze gani balle ya tausayawa khadija. Saudat haka tasamu FCE ta shiga take zuwa makaranta dan ta ragewa kanta zafi. Tsawon shekarun nan uku zazzafar gaba Saudat tajeyi da khadija duk abunda tasan ya shafi khadija nuna masa kiyayya take muraran, har mutane suka fara fuskantar hakan, yan gidansu sunyi mamakin dama akwai abunda ze hada khadija da Saudat dazesa sununawa juna kiyayya kasancewar ba'ajin kansu.

Khadija ta hurawa Habib wuta kan lallai ita seyasamo mata Admission a Dubai ko Egypt tafara karatu, ya nunamata yan uwansa bazasu yadda da hakaba, tayi hakuri duk makarantar datakeso a Nigeria ze kaita amma banda kasar waje, amma fafur ta badawa idonta toka taki, haka yafara nema mata Admission a Dubai ba wanda yasani seshi da ita, Allah ya temaketa tasamu, yasamu Salma yace itama ze nema mata se sukoma can gaba daya, Salma tace bazata ba sedai su barta anan duk sanda yayi niyya in yasamu lokaci yazo yaganta, ya kada ya raya amma Salma tace itafa bazata ba suje se sun dawo.
Haka Habib da khadija sukaje suka tare a Dubai, ita tana karatu shikuma yana kasuwancinsa, seyafi wata uku bezo Nigeria ba gurin Salma ba inma yazo bayafin kwana goma ze juya, hatta mahaifiyarsa ta zuramasa ido, tana masa Addu'ar Allah ya shiryeshi, yana daga cikin kaddararsa Auren hatsabibiyar mace.
Wani zuwa da mahifiyar Habib tayi itada kannensa mata nida yayata,
Gidan bakowa se Salma kawai mama ta tambayeta ina Habib ina khadija nan ta fashe da kuka tagaya mama duk abunda yake faruwa, Mama hankalinta ba karamin tashi yayi ba, ta dinga yiwa Salma fada, danme bata gayamata irin rayuwar da takeyi agidanba kenan, nan da nan ta kira Habib tace kome yakeyi ya yanke su dawo Nigeria tana nan tana jiransa. Yagaywa khadija tace wallahi bazat bar karatunta ta taho ba, shidai ya tafi shikadai, haka Habib ya taho yabarota a can.
Ba karamin bacin rai mama ta nunawa Habib ba tace masa yazama wajibi yadawo da Khadija Nigeria bata yadda da batun karatu a kasar waje ba tunda bashida hankali, ya tare a gindin mace yana zaluntar yar uwassa, yaita bata hakuri, gefe yana fargabar yadda ze sanar da Khadija batun fasa karatunta.
Yaita bawa mama hakuri amma fafur taki yadda tace se khadija ta dawo kasa Nigeria, hankalin Habib ya tashi yarasa ya zeyi da wannan batuna A
Mama, haka ya shirya ya koma dubai yasanarwa khadija hukuncin mama, amma tace ita bazata dawo ba, yasan yadda zewa mama ta hakura amma ita karatunta yafara nisa dan haka yayi hakuri.
Mama tanata matsa masa lamba akan ya dawo da khadija gida, ana cikin wannna halinne khadija ta fuskanci tana dauke da juna biyu abun ba karamin mamaki yabawa khadija ba, yaza'ayi ace tana planing amma tasamu ciki, nan da nan ta shiga damuwa. Tabass barin cikin nan shize hanata da ciigaba da karatunta, gashi bata san kowa ba a Dubai balle tanemi maganin zubar da ciki, dan haka ta samu Habib tace masa ta yadda sukoma Nigeria, ba karamin mamaki yayi ba yadda akayi ta yadda ta dawo Nigeria.
Bayan sun dawo ne, taje inda tasaba samun maganin zubarda ciki tazo ta sha, seda ta kwana biyar tana zubarda jini ba wanda yasan me yafaru, da kyar tasamu jinin ya tsaya amma ba karamin galabaita tayi ba.
Ammame bayan jinin ya dauke haka tacigaba da rashin lafiya, kullum ba lafiya tana kwance kusa  wata biyu taki zuwa asibiti seda taji tana neman ta mutu sannan ta shirya ta tafi Asibiti lokacin Habib baya nan, Asibitin dasuke zuwa taje sukayi mata gwaje2 suka tabattar mata tanada cikin wata uku da sati biyu, abun yabata mamaki dama cikin nan yana nan be fitaba, suka dubata suka bata magunguna, tana barin Asibitin bata zame ko inaba se chemist din da take karbar magani, tai masa bayani yabata wani maganin dayafi  wancan karfi, sannna ta tafi gida.
Khadija na barin Asibitin, doctor Hisham yakira Habib ya sanar masa yanzu amaryarsa tabar Asibitinsu kuma tana dauke da juna biyu na wata uku da sati biyu. Habib yayi murna a take yaiwa Hisham transfer na kudi, tukuicin Albishir, yana katse wayar ya kira khadija
"Madam sannu ya jikin naki"
"Wayace maka banida lafiya?" *"Hisham ya sanarmin kina dauke da babyna, na wata uku Ashe shike wahalar min dake, Allah maji rokon bawa abunda nake ta nema tunda kikayi bari se yanzu Allah yasa aka kuma samu, Masha Allah, Allah yarabku lafiya my deeja" hade rai tayi kaman tana gabansa amma ta maze
"Hmm Hayatee ka kyaleni, nasha magani duk jikina ya mutu"
"Eyya sannu, i wish ina kusa danamiki tausa, amma a satin nan zan dawo Insha Allah"
"shikenan se anjima" ta kashe wayarta, lallai doctor Hisham munafikine shine har ya kira yagayawa Habib, to gara ma yadena rawar kafa dan "kafin kadawo na zubar dashi ta rariya sedai kai yadda zakayi se burina yacika, senayi karatu me zurfi a abroad "

Haka takuma shan maganin zubar da ciki ta dinga malalar da jini, ta kira Habib tagaya masa hankalin sa ya tashi sosai, amma bata gayamasa wani abu ta shaba, yakira doctor Hisham ya sanar dashi, har gida sukazo don duba khadija, dole suka dauketa zuwa Asibiti, da kyar aka ceto ta saboda tasha wahala sosai, a satin Habib ya dawo an rike Khadija a Asibiti ana bata kulawa ta musamman still akayi scanning still cikin yana nan be fitaba, doctor Hisham ya gano tayi Amfani da Abortion pills amma be gayawa Habib ba.
Ya sameta ya dinga mata nasiha, sannan yace idan makamancin haka yakuma faruwa ze sanarda Habib gaskiya, ze gayamasa tana shan Abortion pills ne.
Sannan doctor Hisham ya sanar da Habib cewa zata samu sauki ya kwantar da hankalinsa.
Tunda Habib yasamu labarin cikin nan yakuna tattare a gurin khadija, yake matukar lallabata, itakuwa khadija batun cikin nan ya tsaye mata a rai, sam bata kaunar cikin nan, ga cikin ya hanata sakat saboda laulayi yauda lafiya gobe ba lafiya Habib yana bata kulawa iyayinsa amma ita kawai yadda zata zubar da cikin nan takeyi, takuma shiryawa ta tafi tasamu me chemist din nan tace masa ita so take inba ze iyaba ya hadata da wanda zasu ciremata cikin nan.
Me chemist din nan ya nuna mata illar yin hakan zata iya rasa ranta kokuma tajawa kanta mummunan ciwon daba lallai ta warke ba. Haka khadija takoma gida, duk yadda zatayi cikin nan ya zube wannan karon kin fita yayi, dukda basa jituwa da dangin Habib amma sunyi murna da cikin nan nata,
Abun duniya yakara hadewa Salma, tarasa meyake mata dadi, gaba daya Habib ya canza kaman ba Habib dinta dasuka sha soyayya a bayaba, ga sharri da khadija take mata taita hadasu rigima da Habib, ga rashin lafiya data ketayi, tana zuwa  Asibiti Akai mata gwaje2, aka sanarmata mata jininta ya hau sam hankalin Habib da nutsuwarsa ya tattarasu akan Khadija.
Salma ta shirya taje maiduguri tasami mahaifiyar Habib tace mata dan Allah tasa baki Habib ya saketa bazata iya zama dashi ba ta gaji, mahaifiyar Habib tai kokarin bata hakuri amma ta fashe da kuka "mama wallahi in Habib be sakeni ba zan iya rasa raina, dan Allah ki amince ya a raba Aurenmu" mahaifiyar Salma ma ta yadda tace a sakar mata yarinyar ta baze yuwu a kashe mata ya da bakinciki ba. Mama takira Habib tace tanason ganinshi ya shirya ya tafi.
Koda yaje maiduguri mama tagaya masa abunda Salma ta bukataHabib kuma yace besan zance ba, mama tace yadda Salma takeson Habib harta bude baki tace ya saketa lallai abun ya kai makura dan haka ta goyi bayan ya saketa ta huta haka,
Salma taje ta samu Habib tace
"Habib nasoka tun bansan meye soba, ka koyaddani sonka, Habib ina maka sona gaske shiyasa banason ka kasance cikin wanda Allah ze hukunta ranar Alkiyama, Habib banason Allah yakamaka da laifin rashin adalci a tsakanin matanka, shiyasa nakeso ka sakeni dan Allah Habib, sakina shize kara tabattarmin har yanzu akwai tausayina da kaunata a zuciyarka ka sakeni Habib " tana zuwa nan a maganarta ta sume a gigice Habib ya dakko ruwa ya zuba mata amma bata tashiba haka aka kaita Asibiti jininta ya hau sosai, kwanam ta guda da wuni a asibiti sannan ta farfado, koda ta farfado da kuka ta farfado akan dan Allah Habib ya saketa,
Mama ta titsiye Habib tace seya saki Salma,
"Mama wallahi bazan iya sakin Salma ba ina sonta"
"Kana sonta ka hada kai da makirar matarka kuke neman kasheta, Ka Saketa kokuma in maka baki"
Jiki a sanyaye ya furta ya saketa saki daya. Take Salma tayi ajiyar zuciya tareda murmushi tace "Nagode Habib ina maka fatan rayuwar Aure managarciya da matarka, Allah yabani mesona har abada"
Habib yayi zarya maiduguri akan Salma ta dawo amma fafur aka rasa me goya masa baya, Salma kuma tace itada gidansa har gaban Abada!!!
Khadija kam ko a jikinta, Murna ma tayi tace zata cigaba da rayuwarta yadda takeso, dama kishi da ita se wadda tayi gagarumin shiri, ganin yadda Habib yatada hankalinsa yasata tayi duk yadda tayi ya manta da babin Salma suka cigaba da Rayuwarsu.
Ba karamin kaduwa Saudat tayi ba dataji labarin Salma ta bar gidan Habib, bata taba tunanin hatsabibancin khadija ya kai taraba Salma da Habib ba. Dan haka abun yakara yiwa Saudat ciwo, yanzu duk wannan uban gidan da uwar dukiyar ita kadai ce matar gidan. Nan take taji Ranata yakara baci, "zaki gane baki da wayo khadija wallahi sena miki Abunda ga dukiya amma seta gagareki ci cikin kwanciyar hankali"
Haka khadija tacigaba da rainon cikin da tayi kokarin yafita amma yaki.
Wata tara labour yazo amma bazata iya haihuwa da kanta ba se cs akai mata aka ciro mata da namiji kato kaman Habib yayi kaki ya tofar saboda kama.
Seda akayi sati biyu ta warke saboda cs din da aka mata sannan akayi gagarumin shagalin suna, sam be gayawa khadija sunan dazesawa jaririn ba se ranar suna, ya sanar da sunan yaron ABDUL JALAL, sunan mahaifin Salma kenan!!!!

Tabdijan da alama Habib ya debota da zafi sunan baban Salma fa yasakawa dan khadija.

A ko yaushe ina alfahari daku masoya wannan Novel ina godiya da addu 'oinku.

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
What's app only 07063065680.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now