Seda ta gama wayarta tace ace masa ya tafi ba zata zo ba . Saudat ta shigo dakinta tace
"khadija wai dan Allah wani zazzafan kika samune haka kusan awa uku kina waya, naga duk saurayin dakikayi bakya yiwa Kabir wulakanci amma yau kin shuka masa dayawa fa" khadija tayi wani shu'umin murmushi tace

"ai ke bar gara kawai, najefa fatsata a ruwa kuma da alamu nakamo kifi me nauyin gaske, ba kama kifinne matsalar ba, sedai zanyi gwagwarmaya kafin kifin yazama mallakina saboda akwai masu farautar wannna kifin dayawa abakin ruwan"
ta kuma kallon Saudat tace "kodayake kince ranar biyan bukata rai ba abakin komai yakeba yar uwa, dan haka zan jure gwagwarmaya da kubale in mallaki kifin nan"

Saudat tace "kinga ni kiyimin hausar dazan gane, se wani kwana2 kikemin, nibangane mekike nufi ba"
"karki damu zaki gane very soon yar uwa"

Bangaren habib kuwa, Salma ta damu matuka baya kaiwa tsawon wannan lokacin a waje, amma yau ya kai, tayi2 yagayamata dalili yace bakomai wani abune ya rikeshi haka ta hakura.
Wasa2 taga ya maida hakan dabi'arsa baya shigowa gida se bayan goma, dataga bashida niyyar denawa itama ta watsar dashi tacigaba da sha'aninta, seta ajiye masa abincin sa akan dining tayi kwanciyar ta, hakan yakara bashi damar sakewa suyi waya da khadija sosai.

Ranar juma'a da yamma suka shirya zasu hadu a wani gurin shakatawa, saboda khadija bataso yazo da rana gidansu Saudat ta ganshi, yarigata zuwa gurin yana zaune yanata duba agogo har yafara fidda ran kozatazo, yana kokarin kiran layinta ne, yaji kamshi me dadi yacika masa hanci, dukda yajuya baya, amma tana kallonsa tabaya tasan shine, a hankali ta tako tazo bayan kujerar dayake ta tsaya, ta durkuso da kanta a hankali tace
"Hayateee barka da zuwa" ya dago kai ya kalleta daga sama har kasa, doguwar mace ce, sannan tana da dan kiba kadan, baza akirata da fara tas ba amma tanada hasken fata sosai, tabbas khadija tana da kyau dai dai2 gwargwado, murmushi yayi mata "sannu da zuwa masoyiyar boye" murmushi tayi ta zagaya ta zauna akan kujerar datake facing dinsa, suka gaisa sun sha hira sosai sannan ya dauketa ya kaita har bakin layinsu shikuma ya tafi.

Khadija tayi nasara samun zuciyar habib tana nunamasa soyayya iyayinta, haka habib yasake da khadija suke soyayya ba tareda Salma tasani ba, yakanzo gurin khadija tadi, Saudat ta fusakanci 'yan kwanakin nan khadija tana cikin farinciki. Bayan sun gama cin Abinci khadija ta tafi daki ta shafe kusan awa uku tana waya, a iya sanin Saudat data yiwa khadija tasan bata son doguwar waya, amma ya akayi kwanan nan take waya haka? mikewa tayi tabi khadija daki, taje ta tarar da ita tanata zuba shagwaba a waya, tana ganin Saudat ta shigo dakin tai maza tayiwa habib sallama ta mike zaune
"Saudat lafiya kuwa na ganki haka ba zato babu tsammani?"
"hmm dole kice haka mana almost 3hrs kina waya, ba'a kojin mekike fada, shikam wani me nasarar ne haka? Kodai kin hadu da dream hubbyn nakine?" wani kasaitaccen murmushi khadija tayi
"kwarai kuwa kedai kiyitamin Addu'a"
"shine babu ko Labari balle a gabatarmin dashi?"
'mekikeci na baka na zuba, shida zezama sirinkinku sekin gaji da ganinsa "Saudat tace" Allah sarki Kabir yanata tsuma ze aureki "
Tsaki khadija tayi

"ke dalla kidenamin zancen wannan wawan, nifa badan ina tausayinsa ba da tuni na dade masa wulakanci, kodayake wulakanci na nawa, bashida zuciya ne"
"Mhmmm nikam nace khadija waime ake ciki game danawa damuwar ne, wallahi khadija ko baccin kirki bana iyayi" Ajiyar zuciya khadija tayi tace

"gaskiya Saudat ina tausaya miki, abun nada matukar tausayi, nikaina na kagu inga kinshiga wannan daula amma semunbi komai a sannu, bakisan iya kokarin danakeyi miki ba, yanzu haka nabada cigiyar in yadawo a sanar dani, naje har layin gidansa dakaina, amma ance an hana shiga layin ba tareda wanda zakaje gurinsa yasaniba, amma inata miki kokari "
" to khadija Allah yasa adace"
"zama adace kakri damu Saudat".

Duk ranar da Habib zezo gurin khadija tadi sedai su hadu a gidan kanin mahaifiyarta acan suke zancen, soyayya ce me karfi tashiga tsakanunsu, duk kasar dayatafi A gaggauce yake ya dawo domin ya hadu da ita, baya jure dogon lokaci basu hadu ba.
Habib da kansa yacewa khadija ze turo iyayensa ayi maganar aure, amma zeje maiduguri tukuna in yadawo seya turo, tayi murna ranar kamar ta zauce bata taba zaton a abubuwa zasu mata da sauki haka ba.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now