Alhaji Kabiru yashiga cikin matsanancin bakin ciki, yarasa me yake masa dadi, wai yarsa yakama da wanda ya amincewa wato jeje, abun bakincikin ankamoshi da 'yarsa a gidan karuwai, gashi ba'asan ainihin me yafaru ba amma zance yanata yada duniya, nan yashiga tunanin waima wacece wadda takirashi tace yaje gidanta ne?, in akajima ya tuna yadda yaga yarsa da jeje, se ransa yakara baci, ya kalli Jeje yace "Jabir (shine ainihin sunan jeje) Allah ya isa tsakanina da kai, duk halaccin danayi maka a rayuwa amma ka lalata min yarinya"

Jeje yace "dama can lalatacciyace, kuma halaccin dakayimin aiba kyauta kaimin ba aiki nake maka, shekaru nawa nayi inamaka bauta"

"Au hakama zakace ko, zamu fita ai zakaga abunda zanyi maka, kasanni kasan halina" Jeje ya kalleshi

"kabari kaga munfita lafiya tukuna, aisena bari munfita lafiya zaka samu damar yimin wani abu, dan haka sena fadi komai" zazzaro ido Alhaji Kabiru yayi,

"me kake nufine wai?" inbaka ganeba seka bari sena aiwatar zaka gane".

Duk yadda su Sa'ada sukaso bakantawa Jalila rai bata kulasu ba dan karma su bata mata farincikinta, tabar musu dakin takoma na halima ta kwana a can, tun sassafe tai salla, sukayi aikace2 dazasuyi itada halima a cikin gidan, sannan ta tafi gidansu Jalal itada Halima, tunda Ilham tai arba da Jalila takejin kaman ta dau wuka ta kasheta, suka gaisa da Mummy ta nuna mata kitchen Jalila suka shiga suka fara abunda yakamata, aka jima Nana itama tabaro wasu sa'ada gidan ta tabiyosu Jalila a ranar suka hada snacks din dayakamata, sukabar aikin dabasu gama ba zuwa gobe, kafin bakin suzo sesu karasa, Nana da halima suka koma gida, Jalila ta tsaya tana karasa gyara kitchen din, Jalal ya shigo da katon kwando cike da fruit ya ajiye yai waje abunsa, ta zauna ta shiryasu a fridge sannan ta tafi.

Wahsegari da safe Jalila ta dawo, bata tashi halima ba daga bacci saboda taga alamar tagaji sosai jiya, ta dama kunun gyada, ta dibi nata a dan karamin flask ta tafi dashi.
Jalila tayi busy sosai a kitchen, dan bata samu ko karyawa tayi ba, dogon wandone a jikinta da rigarta har gwiwa me dogon hannu, ta daure kanta da dankwali, amma karshen gashin ta yafito, taji alamun ana kallonta, bata waigaba ta basar tacigaba da abunda take, cikin kitchen din ya karaso ba sallama ba komai yakama dube2, bata kulashiba tacigaba da aikinta ya jijjiga tea flask bakomai a ciki, tsaki yayi ya bude fridge yana kallon arrangement din datayiwa fruits din, still ya rufe fridge din, Jalila ta fuskanci yunwa yakeji, ta kalleshi

"wai meyene?"
"bansaniba" ya bata Amsa

"karka sani din" ta faɗa tare da murguɗa baki. yaje ya duba kettle yaga akwai ruwan zafi a ciki, ya dakko ya zuba bako lipton, ya dakko madara da sugar yana kokarin antayawa, ita Jalila ma dariya yabata, ta dakko flask ta zuba masa kunun gyada a cup, ta zubamasa samosa, ta mika masa, bako kunya ya karbe, yanemi guri kan kujera a kitchen din yai zamansa yafara ci, itakuma tacigaba da aikinta, wayarta tafara ringing, sunan sweet hanny shine akan screen din wayar, tadaga wayar tasa a kunnenta
"Hello sisyna ya kike?" hanan tace "Hmm ba fada meyakawo gaba Baby, kin yadani, kin manta dani ko?"

"A'a hanan ban manta dake ba, ko zan manta komai bazan manta da yar uwata ba"

"Anya kuwa Jalila? Kina guduna saboda inason Jawwad ko? Karki damu hakan baze shafi zumuncinmu ba, amma yakamata kikawomin ziyara, in duniya da gaskiya bekamata ace tunda kikabar kaduna baki kuma zuwa ba"
Kwalla ce ta taru a idon Jalila, cikin muryar kuka Jalila tace "Hanan bazan iya zuwa kaduna, bazan iya zuwa anguwarmu ba, Hanan hakan ze tayarmin da hankali, inzo unguwarmu ummi bata nan, bansan inda take ba, kiyi hakuri Hanan, amma kina raina dake da sauran mutane masu mahimmanci danake dasu a garin" takarasa maganar hawaye nabin idonta

Hanan tace "Jalila na fuskanci abunda yake damunki, inajin damuwarki a zuciyata, kiyi hakuri mucigaba da addu'a kinji, kidena kuka"
gyada kai Jalila tayi kaman tana gaban Hanan, sannan tace
"Nagode Hanan, kigaida kowa da kowa mussaman babana"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now