"karka tsananta tambaya dan bazan gayamaka komai ba amma lokaci zenuna komai, mahaifiyarka zatayi nadamar abunda tayi, kayi kokarin ganar da ita, tun kafin tasamu kanta a halin datawa mahaifiyar take ciki, nima da datawa damuwar nazo maka amma bari in kyaleka ka huta, kacigaba dayaimana addu'a kaji dan uwana, banason damuwar ka ina kaunarka dan uwana kadena damuwa" Jalal ya dan daddaki bayan Jawwd alamun rarrashi, daga nan ya tashi ya fice.

Jalila yadda taga rana haka taga dare, se tufka da warwara kawai takeyi, gashi tunda ta dawo Nana ko dakin bata shigaba, Maama ta hanata Nana bata kwana a dakin ba a can gurin Maama ta kwanta.
Bangaren Jawwad ma hakane, juyi kawai yakeyi, ya daga waya ze kira Jalila yaga inya kirata ma mezece mata, tunda be tabbatar Jalila taji abunda Maama taceba haka ya haƙura da kiran nata.

Washegari Sam Jalila bata nuna da wani abu a ranta ba, sedai ko karyawa batayiba ta fita domin tafiya makaranta, a kofar gida tasamu Manu yanata goggoge mota, suka gaisa takoma gefe tana jiransa yagama su tafi, Jalal yana cikin motarsa a kofar gida, zeje wani guri, daga cikin motarsa yana ganin yadda ta rame, da ganin idonta kaman bata samu bacciba ta kwana cikin damuwa, lokaci2 tana goge idonta da handkerchief, Jalila tanada yawan fara'a bata fiye hade raiba, musamman in ta samu abun tsokana, amma yau fuskarta sam babu annuri, setayi kaman wadda ta dade tana jinya, har cikin ransa seyaji babu dadi ganinta a haka, haka manu ya dauketa ya kaita makaranta.

Hannah abun duniya ya dameta tarasa ta ina zata bullowa lamarin Jalal, amma tanason sanin matsayin Jalila a gurinsa, yazama dole taga Jalila, amma bari inje gurin wannan garan sena hadu da Jeje, Hannah ta shirya tsaf ta dau mota, ta tafi inda tasan Zata hadu da Jeje. Jeje na ganin Hannah yafara murmushi yana tafa hannun sa

"barka da dawowa Gimbiya Hannah"

daga masa hannu tayi alamar bata son surutu, guri ta nema ta zauna tana facing din Jeje, Jeje ya rigata magana ta hanyar cewa

"dama nasani Hannah zaki dawo, zaki cigaba da aiki damu kin temaki kanki da kika gane hakan, don Jalal baze taba aurenki ba, ni kaina yau rabon da Jalal yazo mashaya ya dade, shiyasa wani shirin muke sakeyi akansa zuwanki a yanzu kinzo akan gaba"

Hannah ta katse shi ta hanyar cewa

"kaga dan Allah kayi shiru kaji meyake tafe dani se surutu kake, kai ka isa inyi magana in janye saboda wani banzan me gidanka baku isaba wallahi ka tsaya ka saurareni, nazone in gaya maka wanda yasa aka dauke Jalal ranar birthday dinsa ba kowa bane face wannan yarinyar data kawo cake" a razane ya kalleta

"are you serious?"

"sekaje kayi bincike, da bakinta tagayamin haka, sannan kasani in har tana raye to baka isa kuyi nasara akansa ba, seku sake shiri sannan nima bazan bari kuyi nasara akansa ba saboda aurensa zanyi, mataki ya rage ku dauka akan wannan yarinyar, danni nafi karfinku kasani"

Jeje yace "Amma hannah........"

"kaga ni na riga nagama magana"

ta mike ta bar gurin, jinjina kai Jeje ya dingayi yana tuna abunda Jalila tagaya masa daren da yafara ganinta akan Jalal, tabdijan yazama dole ya dau mataki akan yarinyar nan, Yazama dole anjima inje gidansu Jalal da kaina, inbahakaba akwai yuwar wannan yarinyar tamayar mana da aiki baya, bazan bari oga KB yaji wannna zancen ba mara dadi"

Anfito daga exams Jalila tana tafiya kaman wadda kwai ya fashewa a ciki, daka ganta kasan bata cikin walwala, gani tayi an sha gabanta tana daga ido taga saleema, matsawa tayi da niyyar wucewa, takuma shan gabanta

"Ke magana zanyi dake" Jalila ta kalleta "ina jinki" "Kashedi na karshe zanmiki akan Zahrah, ta kawo mana kararki dan haka ba ruwanki da rayuwar da takeso tayi, dan haka kidena mana shishshigi, bake ba zahra" Jalila ta dakko wayarta tana dannawa sannan tacewa Saleema

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now