ABDUL JALAL 63

Start bij het begin
                                    

"hmm Jawwad za aci amana kenan? hakan yafi ai, dan baki dace dashiba gara ya auri mutuniyar kirki, dan duk jarabarki bazaki auri dan uwana ba, Jawwad da salihar mace ya dace ba irinkiba mara kunya"

kallonsa tayi sannaan tace

"nice ma kai a rashin ji, aigarani da kai, kaima kasan hakan kuma duk bakin cikinka sedai kayi, dan nafi karfin ace za'a kyamaceni a matsayin mata, dan nasan nafi wannan doluwar kanwartaka Ilham"
"Hmmm meye kuma nasakota a wannaan zancen? "
"kaika sani, nikawai ka budemin in fita" banza yayi mata yacigaba abunda yake, wasa2 kusan mintunansu talatin a tsaye Jalal yaki tafiya, hannu takuma sawa zata fizge tabar bakinsa cikin zafin nama ya hada da hannunta ya rike, ya juyo yana kallonta, wani mugun kwarjini yayi mata ta kasa magana ta sunkuyar da kanta kasa, ƙirjinta yana ta bugawa da ƙarfi

"karki kuskura, bar ganin na kyaleki dazu" sakar mata hannu yayi, yacigaba da abunda yake, karfe tara hada rabi, amma Jalal yaki kaita makaranta, tarasa mezatayi kawai tafara kuka, seda Jalal yaga dama sannan yaja motar yacigaba da tafiya, wannan karon kuma a hankali yake tafiya kaman bayaso, hannu yasa ya kunna radio motar inda karatun Al qur'ani yake tashi, Jalila aranta tace "Tab dama yanajin karatun qur'ani?" bata gama tunanin ba taji Jalal yanabin karatun a hankali, juyowa tayi tana kallonsa, danta tabattar anya kuwa shine yakeyi, sosai yakebin karatun cikin suratul Ibrahim, dan tabe baki tayi tana jinjina lamarin dama Jalal ya iya karatu haka, amma koda wasa bata tunanin ko bismillah ta tabajin yayi, se masifa da wake2, tana cikin tunanin taji yayi parking,

"inkin gama kallon nawa seki fita"
" Baka da abunda zan tsaya ina kallo, ko Meye amfanin zuwanama, tunda dai na makara nasan ba lallai inyi jarrabawar ba, kaida Allah in abunda kayimin dai2 ne, kodayake baka san darajar jarabbawa ba shiyasa kamin haka kuma Insha Allah se" "Ke!!!!" ya dakamata tsawar data tilasta mata yin shiru
"wallahi duk randa bakinki yai kuskuren yimin muguwar Addu'a akanki zata kare, gobe in ankuma cewa kibi namiji mara daraja irina se kikuma biyoni, fitarmin daga mota, inba hakaba na kunna motar nan senaje gida zan tsaya, kyasan yadda zakiyi"

bude motar tayi tanata kunkuni gashi ta hade rai sosai, ta fice tabar motar a bude tai tafiyarta.

ankai ruwa rana sosai kafin abar Jalila tashiga hall din exams saboda ta makara, Jalila ji take kaman tana komawa gida takama Jalal ta shakeshi seya suma, haka tai exams din ta fito cike da takaici.

Tasamu guri ta zauna a karkashin wata bishiya, ta zauna babu dadewa Zahra ma tazo gurin

"Jalila ya akayi kika makara haka yau?" dan tsaki Jalila tayi

"kedai bari, wani ne yajamin wallahi, kuma ze gauraya dani"

"hmm Jalila kenan me jama'a, Amma ke sir Hafiz fa yace ince miki kije, nifa nakasa gane meke shirin faruwa tsakanin ku"
Jalila ta kalleta ta dauke

"ki goge zuciyarki tsaf kidena bari tana kawomiki wani tunani" zahrah ta jinjina kai

"ke ba wannan ba Jalila, ina mafita anawa lamarin? Ina cikin damuwa wallahi"
"Nasani Zahrah, amma abubuwan dasuke kaina dayawa ga wannan jarrabawar ga sauran abubuwa"

"to nidai kitemaka Jalila, karsuyi nasara akaina"
"Ai yazama dole in temaka miki, sabida indai nayi nasara, kikayi yadda nace to nikeda riba, zangaya miki yadda zamuyi, amma banason gaddama da taurin kai, duk abunda nace kiyi, bazan bari kiyi abunda zaki cutu ba"

"to shikenan inajinki" Jalila ta gyara zama

"zaki Amince da bukatar su Sameera" zaro ido Zahra tayi

"Amma meyasa?"

Nan Jalila ta tsarawa zahra yadda abun ze kasance, zahra ta yadda da abunda Jalila tagaya mata.

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu