"Enough daddy" Jalal yai maganar a fusace, "Wannan maganar daga ina? Duk matan duniya in rasa wadda zan aura se wannan, in har farinciki kake nafara maganar aure, to da saurana, wait wai wama yagaya maka wannan maganar, kodayake base ka gayamin ba nasani," ya kalli mummy "Ke kika gaya masa nasan haka, nidake na taba cemiki ina son wannan yarinyar ne? Meyasa kikemin hakane, meyasa kikeson kuma rusa al'amuran rayuwata, ke a ganinki Ilham ta dace da zama matata, kimin adalci kiyiwa kanki mana, akoda yaushe kidena duba maslahar kanki kawai, kuma Ilham tunda Ubanta na raye se ta bar gidan nan, ai ba gidan ubanta bane ba, akanme za a dinga batamin rai haka, wallahi sena kakkarya yarinyar nan inga uban da ze tsayamata" daddy yai gaggawar mikewa da nufin tare Jalal amma Jalal ya kauce ya nufo hanyar fita,
Ilham taiwa Jalila wani mummunar kallo

"ai dama da ganinki base an fada ba ke mayyace, bari inkuma jadadda miki, duk maitarki kurwata data Jalal tafi karfinki haka kika ganmu haka zaki kyalemu, nidashi mutu ka raba"

Jalila tace
"to dan kincemin mayya ai ba haushi zanji ba, ko ina cin kurwa bazanci taki data Jalal ba saboda bazanci kazamar kurwa ba, kuma kina bani mamaki, dakikancinki yayi yawa Ilham bansan lokacin dazaki gane cewa niba abunda zanyi da wannan dan giyar ba, kuma kema dakike ta wahala akan se ya aureki don cikar burinki, ABDUL JALAL baze taba aurenki ba Ilham, tunda yace baya sonki baze sokiba, kuma kinsan daddyn sa yana goyon bayansa, nasan hanya dayace dake dazakibi ki aureshi hanyar sihiri kuma wannan hanyar bata bullewa"

da sauri Ilham ta kalli Jalila tanaso tayi magana amma takasa,

"Karya kikeyi, Yaya Jalal yana sona kuma bani da wani mugun nufi akansa, ubanwa yagaya miki saboda wani dalili nakesonshi, munafuka duk masifarki wallahi haka zaki kyalemu, dan banga uban daya isa ya hanani auren Jalal ba"
"Eh kinyi mamaki ko? Ya akayi nasani, da bakinki kika fada, ba a gurin wani naji ba sannan.....

" A gidan ubanwa na taba gayamiki ina sonki meyasa ba kya ganewa, sa'anki neni, mahaukaciyar inace ke dakike tunanin zan aureki? Yau zaki tattara kibar gidan nan tunda bana ubanki bane, akanme zaki dage cewar nikikeso nace bana sonki bana sonki meye haka wai, mekike nema a gurina ne Ilham"

Jalal ne yakewa Ilham magana cikin fada, da sauri daddy ya fito tareda Mummy, daddy ya karaso inda Jalal yake "haba Jalal ai duk abun be kai hakaba, koba komai kanwarkace, kayi hakuri"
"

" Daddy wace irin magana kakeyi hakane, seta bar gidan nan koni inbar muku gidan, akan me za a takurawa rayuwata, for what reason dad, ace kullum mahaifiyata batada buri se ganin bacin raina" Jalila rasa abun cewa tayi, ta kalli wannan ta kalli wannan,

"Haba Jalal ya ina matsayin mahaifiyarka zakace bana son cigabanka, Aurenka da Ilham alherine ni banga aibun Ilham ba, a tunanina komai ya wuce" wani mugun kallo Jalal yaiwa Mummy duk ya birkice idonsa yai jawur "Kikace komai yawuce, karki yaudari kanki mana, kodayake son zuciya baze barki kidinga ganin gaskiya ba, nayi dana sanin kasancewarki mahaifiyata, kullum bakida burin daya wuce gayyato matsala cikin rayuwar dan dakika haifa, haka sauran iyaye sukeyi"

Jalila kasa jure abunda Jalal yake tayi , wanda hakan yasa ta mike ta fice daga palourn jikinta a sanyaye, tafito ta jingina da bango tai shiru tana tunani "meyake damun Jalal ne? Dole nasan dalilinsa na cin zarafin iyayensa musamman mahaifiyarsa, ina tausayawa Jalal ya mutu yana sabawa iyayensa, zanso inji dalilin hakan kozan iya temakamasa, wulakanta iyaye ba abune me sauki ba"
Ilham se kuka take, duk yadda daddy yaso ya shawo kan Jalal ya kasa, seda yai me isarsa sannan ya bude palourn ya fito a fusace, yana fitowa Jalila tana gurin a tsaye akan hanyar daze wuce, hannu yasa ya hankadeta gefe yai gaba abunsa ya nufi part dinsa, mamakine yacikata, kodayake ba abun mamaki bane kadan daga aikin giya.

Jiki a sanyaye ta baro gidan, sedai me tana fitowa taga motar Hannah a kofar gidan, ta fito tana ta kiran lambar Jalal amma yaki dagawa. Jalila a ranta tace "lallai Jalal kana cikin iftila'i" dayake duhun magariba yafara yi, Hannah bata gane wacece ba, dan haka tace "Dan Allah baiwar Allah naga kaman daga gidan kika fito Jalal na ciki ne?"
Karasawa Jalila tayi gabanta

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now