"tashi ki tafi kibani guri kuma kar inkuma ganinki a part din Jawwad dai 2 wannan lokacin, dan kinsan baya nan inkuma kika kuma zuwa to nasan abunda kikazo gani"

Sumi2 ta tashi, taje bakin kofa ta tsaya ta kalleshi

"to me zanzo gani,? kaikanada abun kallone jiki duk gashi ba kyan gani sekace jikin biri, kokuma wannan jijiyoyin na jikin ka zanzo kallo?, jiki kamar dan wrestling aikai ko kyan gani baka dashi, kasa wannan katon hannunka ka matsemin yatsuna Allah yasakamin dan ban yafeba kuma duk barazanar ka bazan dena fadan gaskiya ba, sannan kayi kadan kayimin Illa ko a yanzu ko a gaba, mugu kawai"

tai ficewarta, Jalal kam yana jinta tana banbaminta ko dago kansa beba balle ya kalleta.
Ta wuce cikin gida tana yarfa hannu saboda zafi, tana zuwa daki taga Nana ta shirya da alama fita zatayi
" Ya dai naganki kin hade rai, me akayi miki ne? " Jalila ta yamutsa fuska "Bakomai" "Shikenan dama kenake jira kizo ki rakani gidan, Yaya mairo, tace tana son ganina"
"Tab amma badani Jalilan bako?"
"Kamar yaya?" "kamar yadda nagaya miki mana, haka kurum ketace tana son gani baniba, dan haka ba inda zani, banje gidanta ba ma cimin mutunci take, inaga innaje mata gida, kitafi kawai, ba inda zani" "Shikenan tunda bazakiba, dama banason tafiya nikadai ne" "sauka lafiya ki gaishesu"

Bayan Jawwad ya dawo daga school suka zauna domin cin Abinci rana shida Jalal, Jalal ba karamin dadi yajiba ganin wainar shinkafa ce, sunci Abincin nan sosai, Jalal yace "Jawwad dan Allah in da sauran Abincin nan ka zubamin in kaiwa daddy, kasan yana son wainar shinkafa" "Hakane Allah yasa akwai, bari inje cikin gida in duba" Jawwad ya tafi domin dubawa koda Abincin, Jawwad na fita aka kirashi waya, Jalal ya daga wayar ya duba, seyaga sunan Hanan, Murmushi yayi ya daga wayar
"Jawwad ka manta dani ko? Baka daga wayata, nashiga wani hali banajin dadin abunda kakemin" gyara murya Jalal yayi
"ba Jawwad bane, Jalal ne" "Jalal kaine yakake ya gida" "lafiya kalau ya Abdallah, kodayake muna waya dashi" "Yana lafiya, Jalal kaga abunda Jawwad yakemin ko? Banajin dadin hakan, dan Allah kasa baki, Jalal inason abokin ka da wasa na dau abun amma yanzu serious nake sonshi, Jalal help me, so masifa ne, da ban yadda da hakanba se yanzu" "kinaji Hanan, kiyi hakuri Jawwad inyace baya Sonki karya yake, kawai yana duba alkar dake tsakaninki da kanwarsa, amma karkidamu zamuyi magana dashi"
(🙄🙄🙄 nikam nace su Jalal dama an iya rarrashi haka) Ajiyar zuciya Hanan tayi "to nagode sosai Jalal, agaida su Ilham"
Jawwad ya shigo da food flask a hannunsa, ya ajiye ya kalli Jalal, "gashi nan Abincin Baby ne tace abawa daddy, amma dawa kake waya haka a wayata"
"Jawwad" "Na'am ina jinka" "Meyasa kakewa yarinyar nan hakane" "Wace yarinyar kenan?" "Hanan mana, ta damu da kai, kamanta kaikake min fada akan Ilham segashi kaima kanayi, meye marabar Hanan da waccan fitsararriyar banzan, ba gara Hanan din bama tafita nutsuwa da saukin kai" "Haba Jalal, Jalila da soyayyar ta na tashi, banason yin abunda zan bata mata rai, tarayyata da Hanan baze haifar da da me idoba, kuma Hanan da kake ganinta itama rigimammiyace, kaikewa Jalila wani kallo dan bakwa jituwa"
"Jawwad yakamata kakoma hankalinka, kayi wani abu akan yarinyar nan mana, kana ganinta so classic nasan da wanine ba kaiba zata sauke ajinta tace tana sonsa ne? Kayi wani abu mana" tsaki Jawwad yayi
"Ina tsawon shekaru Ilham ta dauka tana nuna maka so, kai mekayi akai"
"Jawwad kasani nasani, nida Ilham bamu dace ba, kuma kasan dalili, kuma bari in sake jadadda maka, kokuma in tunamaka wani abu, mahaifiyarka bazata taba bari ka auri Jalila ba, musamman in wannan magananniyar matar tana nan, kaima kasani, kayi tunani Jawwad kafin al'amura su kwabe maka" yana gama fadin haka ya kwashi food flask din yai ficewarsa, yabar Jawwad a zaune yana tunani.
Jalal yana zuwa gida ya tafi part din daddy da fara'arsa, "daddy ina fatan bakaci Abincin rana ba? " "banciba ina shirin ci dai" "Abincin daka fiso nakawo maka" Jalal ya turawa daddy flask din ba karamin murna daddy yayi ba daganin Abincin da Jalal ya kawo masa, "Jalal inaka samo wannan Abincin?" "a gidansu Jawwad" "yaushe rabon da inci masa" daddy ya dan kalli Mummy "Madam kindenamin Abincin gargajiya, mussaman favorites dina" "hmm ba gashi danka yakawo maka ba sekaci ai" daddy yai murmushi "Jalal wayayi girkin nan yayi dadi" "nima bansaniba" Mummy tace "nasan baze wuce Jalila ce tayishiba, dan Maama bata fiye yin girki ba Nana kam dama ba a maganarta akwai son jiki"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now