ABDUL JALAL (2020) 27

Start from the beginning
                                    

Wajen karfe Tara sannan Jalal ya tashi daga nannauyan baccin da yayi kansa yana ciwo, jiyayi yana warin turaren Ilham tsaki yaja yafara tunanin abunda yafaru wannan wane irin sha³ mafarki yayi kuma ma da Ilham (shi a zatonsa abunda yafaru mafarkine)
Mikewa yayi yaje yai wanka ya fito yayi sallar asuba karfe Tara na safe

Jalila tana kokarin shiga makaranta taji ana tayimata horn bata waiga ba ta koma gefe akakuma tahowa inda take a fusace tajiyo tana masifa
"Wai meye hakane anyi Horn na canza hanya ankuma biyoni if you like bi ta kaina komawaye"
Bude motar yayi ya fito tana dariya Allah yabaki hakuri Yar baba,
Yayan Hanan ne Abdallah yakawo Hanan makaranta murmushi Jalila tayi
"Au ai bansan kai bane ina kwana"
"Lafiya kalau ya mamanki"
"Tana lafiya"
Juyawa yayi ya kalli motar yace"ke Hanan fito mana kin wani Zauna a cikin mota"
Sannan ya dawo da kallonsa kan Jalila "Yar baba kaman kuwa kinsan daddy yace agaisheki har yabada sako abaki"
Hanan ya kalla wadda se wani cika take tana batsewa
"Hanan bani sakon nan"
A wulakance ta bude Jakarta ta miko masa wata Leda
Ya karba yabawa Jalila
"Kai amma nagode sosai Yaya Abdallah ka cewa baba Yar baba ta gode, Allah yasaka masa da Alkhairi yabashi abunda yake nema duniya da lahira, Allah yabashi ladan kyautatawa marainiya"
Ba Karamun burge Abdallah tayi ba,"zangaya masa insha Allah"
Tsaki Hanan tayi ta wuce abunta cikin school, Jalila ma cikin makaranta ta shige, duk zafin kan Hanan bata kuma kallon seat din Jalila ba balle takuma sha awar zama a gurin,
Zama Jalila tayi ta dakko abunda akabata chocolates ne kala² a ciki murmushi tayi gaskiya mutumin nan yana da kirki
Bayan anfita break Jalila taje seat din Hanan ta zauna a kusa da ita tace kawata ya kike
Wani mugun kallo Hanan tayi mata ta dauke kai, bude chocolate dinta tayi tafara sha sannan ta kalli Hanan kawas
"Bismillah"
"Abun ya fito daga gidanmu sannan kice insha ke dai da kike kwadayaiyiyya seki sha dama Dan talaka akwai iya shishshigi,"
Murmushi Jalila tayi sannan tace
"duba ajin nan akwai 'yayan Wanda sukafi mahaifinki dukiya, amma abun be baki mamaki ba ina Yar talaka amma nake makarantar' yayan attajirai kaman Hanan rasheed, ashema Baku wani Tara ba tunda har Yar matsiyata kamar Jalila Aliyu take a irin makarantar Ku"
Mike kafa Jalila tayi ta Dora a saman bencin
"In ana batun gata Hanan, be kamata kisaka baki ba, Dan baki da gatan da Jalila take dashi"
Jalila se gayamata bakaken maganganu take tana shan chocolate dinta, Hanan tana fargabar ramawa saboda gani take Jalila bata Risina ba zata iya maimaita mata abunda tai mata amma duk da haka ta dake tana ramawa

Jawwad ne yakuma dawowa gurin Jalal amma Jalal yayi masa banza yaki kulashi, haka ya hakura ya tafi ya kyaleshi

Bayan an tashi daga makaranta Jalila ta dawo Gida amma ummi bata nan wani bakin ciki Jalila taji ta tsani ta dawo Gida taga ummi bata nan
Waya ta dakko ta kira ummi
"Ummi ina kika tafi ne?"
"Kinganmu a asibiti Hawwa muka kawo ta haihu Dan ba rai yanzuma Karin jini ake mata"
Zaro ido Jalila tayi
"Wace hawwan dazu fa da safe tazo"
"Bayan tafiyarki tafara nakuda"
"To meyasa akayimata aure yanzu se wahala takesha?"
"Aa seki bari in danginta sunzo ki tambayesu"
"Allah yabaki hakuri itakuma Allah yabata lafiya amma Dan Allah ki dawo Gida"
"Bazan dawo ba din a can zan zauna"
Ummi ta kashe wayar

Seda Jalal ya shafe sati baya kula Jawwad, sekuma daga baya Dan kansa ya sakko, suka shirya
yayinda kullum se Jalal yaje mashaya, Hannah tasamu damar cigaba da cusa kanta, a gefe daya itama Ilham tanata nata kokarin, sunsaka Jalal a gaba, Jalal dai se kara shirircewa yake

Alhamdilillah Neman maganar Jalila daga Islamiyya har boko yayi sauki, ta fara nutsuwa, yayinda mahaifin Hanan keta kyautatawa Jalila, amma Jalila ta takurawa Hanan, kullum tana manne da ita, Hanan ta zageta ta gaya mata bakaken maganganu amma Jalila batajin haushi takance mata"Hanan mahaifinki yana da karamci, yana kyautata min, komai zakiyi min bazanji haushi ba, shiya hadamu kawance kuma ni na karba"
Hanan mulkinta take zubawa a cikin makarantar daga malamai har dalibai shakkata sukeyi,amma banda queen J

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now