ABDUL JALAL (2020)

Start from the beginning
                                    

Se bayan magariba Jalal ya kuma ta shi wannan karon seya jishi sakayau babu ciwon kan se rashin kwarin jiki
Wanka yaje yayi ya rama wasu daga cikin sallolin dabe ba ya bar wasu Jeje ya kira a waya yaji yana ina yagaya masa
Kaya ya canza ya dauki motarsa ya bar gidan kai tsaye club din da yake haduwa da Jeje ya tafi kamar kullum yauma club din cike yake da "ya'yan da suka rasa mafadi maza da mata kowa na sharholiyarsa matan nan wasu sunyi shiga half nicked wasu na rawa yayinda wasu suka kama daki suna shagalinsu
Jeje naganinsa ya washe baki yana masa sannu da zuwa gaisawa sukayi Jalal yasamu guri ya zauna Jeje ya tafi kawo masa mutuniyar tasa wato giya
Duk gigin matan gurin nan basa zuwa inda Jalal yake saboda sun San halinsa basa gabansa shidai ze sha giya yayi mankas amma be yadda yayi zina ba
Jeje ne yasamu guri ya kira Hanna
" kina ina ne?"
"Ina Gida mana"
Hanna taba shi amsa
"Muna tare da mutuminki fa yanzu haka"
"Dan Allah dagaske dazu Dana kirashi abokinsa yace min bashi da lafiya"
"Ke dalla rabu da wannan sakaran kilma karya yakeyi"
"I wish in samu dama in fito yanzu inzo in ganshi"
"Ke rufamin asiri yanzu ma abu zan karbo masa ke dai kicigaba da kokari"
"Karka damu kaman yazo hannuna ya gama ne"
"That's good seda safe"
Sukayi sallama da jeje ya tafi bar domin karbo giya
Bayan ya karbo ne yazo ya nemi guri ya zauna ya Tarar da Jalal yanata salansa yana bawa sama hayaki tabarsa kawai yake sha
Jeje ne ya tsiyayawa Jalal giya a cup ya tura masa gabansa
Wayar Jalal ce ta fara ringing ya Dakota seyaga unknown number seyaki dagawa ya cigaba da abunda yake haka wayar taita ringing
"Maza wayarka fa ake kira"
Sedayaja wasu seconds sannan yabawa Jeje amsa
"Nagani"
Dan tabe baki Jeje yayi yacigaba da shan giyarsa
Messages ne suka dinga shigowa wayarsa
Tsaki yayi ya dau wayar yafara duba messages din
       "Haba fitilar rayuwata         meyasa zakamin rowa, just want hear your sweet voice
I really care for u, bazan iya bacci ba in banji muryarka ba love u baby
         From your lovely bae"

Ire² wannan messages dinne ake ta turomasa tsaki yayi sannan ya danyi shiru yana zancen zuci anya kuwa Ilham ce take turo masa wannan messages din, wacece ta kira dazu sukayi waya da Jawwad?
Ya tambayi kansa still wayar ce tafara ringing da Sauri Jalal ya yinkurin dagawa domin yiwa ko wacece rashin mutunci seyaga Jawwad ne yake kiransa dan zaro ido yayi sannan ya daga wayar
"Jalal kana ina?"
Jawwad ya tambayeshi
"Na dan fitane"
"Hmmm daga samun saukinka harka fita ko ka tafi gurin Wanda sukafi kowa mutumci a idonka shikenan seda safe"
Jawwad ya katse kiran mikewa Jalal yayi yadauki mukullan motarsa ze fice
Jeje ya kalleshi
"Ya dai ba dai tafiya zakayi ba?"
"Tafiya zanyi mana dama bana jin dadi Jawwad yaje bana nan naji ransa a bace dole in tafi inje ba shi hakuri"
Wani bakin cikine ya tokarewa jeje ji yayi kamar ya rufe Jalal da duka,
Yadda Jalal baya son bacin ran Jawwad da iyayensa yakewa haka da ya dace
Anya ba asiri Jawwad yayiwa Jalal ba jeje yayi maganar a zuciyarsa
Shikam Jalal besan yanayi ba dan tuni ya bar gurin

Ilham ce ke ta safa da marwa a dakinta tare da fatan Jalal ya sha tea din nan da se tafi kowa farin ciki gajiya tayi da tunane² dan haka ta yanke shawarar ta dan fita taje gurin Nana
A daki ta tarar da Nana suna waya da Jalila dan haka ta nemi guri ta zauna daga baya data fuskanci Nana da Jalila take waya seta wani hade rai
"Naji kaman kinyi bakuwa se anjima"
Jalila tayi maganar
"Ba wata bakuwa ceba Ilham ce fa"
"Hh kice Juliet ce, to kice mata a dai dinga sassauta masa adena wahalar dashi"
Dariya Nana tayi tare da fadin
"To Ilham kinji dai sakon Jalila"
Tsaki Ilham tayi dan yanzu ta kara tsanar Jalila mussaman akan abunda yafaru shekaran jiya Jalal ya dinga zaginta

"Kinga ni na tafi nazo gurinki kina rainamin hankali"
Ilham tai maganar tana mikewa
Nana tayi saurin rikota tare da kashe wayar
"Ke bakisan wasa ba indai Jalila ce wataran se ta saki kuka"
Da Sauri Ilham ta kalleta "kamar ya?"
"Eh mana ai ita yayinda taga ba kyason abu to lokacin zata dinga yimiki dan tabaki haushi"
"Wallahi nafi karfin kamata wata Jalila ta Sani kuka"
"A'a dai yadda kike da saurin fushin nan Lokacin daza tasaki kukan ma baki Sani ba
Amma abunda yake burgeni da ita shine akwai kwanya musabaka sukaje Abuja fa tazo ta biyu"
"Ai nasani"
Ilham tabata amsa
"Ya akayi kika Sani?"
"Ke ni mu bar wannan zancen Nana damuwata kullum karuwa take akan Yaya Jalal amma gani nake ba wadda tsana kamar ni"
Ta karasa maganar cike da damuwa
Nana ta dafa ta
"Ilham ba tsanarki yai ba kinsan shi kawai miskiline baya son shiga sabgar mata mazan ma kinga ba kowa yake kulawa ba Sam baya son mutane watakila fa a ransa yana sonki, inaga Ku da haka naku labarin soyayyar ze fara"
Nana tai maganar cike da kwarin gwiwa
"Dagaske Nana kumafa se hakan yakasance ko?"
"Sosai makuwa wannan ai ba abun mamaki bane"
"Shiyasa kike burgeni Nana bakiji yadda hankalina ya dan kwanta da maganganun nan nakiba"
"Ai irin miskilan mutanen nan abune mawuyaci kagane inda sukasa gaba da wuri karkiyi mamaki sonki yana nan fal a zuciyarsa"
"Allah yasa haka Nana"
"Ai hakanne ma insha Allah Mrs. Jalal to be"
Haka Nana ta dinga ziga Ilham tana kwantar mata da hankali Akan abunda bata da tabbas akai

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now