ABDUL JALAL (2020) 19

Start from the beginning
                                    

Bacci ne yafara fusgar Jalal dan haka anan gurin ya zube ya lumshe ido yana sauraren karatun Jalila har bacci yayi awon gaba da shi

Da safe Jawwad ne yazo ya tarar dashi yana bacci a parlour a kasa kan carpet ga kwalbar giyarsa yasha fiye da rabi
Girgiza kai Jawwad yayi
"Allah ya shiryeka Jalal"
Yasa hannu ya kwashe kwalbar da kofin ya fita dasu ya dawo ya tashi Jalal don yasan be salla ba balle ya karya
Hannu ya kai ze tasheshi yaji kansa yayi zafi, bayansa ya Dan bubbuga a hankali Jalal ya bude ido ya mayar ya lumshe
"Ka tashifa gari yayi haske kayi salla kazo mu karya"
Jalal ne yake tunano abubuwan dasuka faru jiya da daddare gaskene kokuma mafarki yayi ji yai kansa yakuma sarawa

"Kaina ne yakemin ciwo sosai Jawwad"
"Sannu ka tashi in muka karya seka sha magani"
Da kyar ya lallabashi yaje yayi wanka yai sallar asuba, Jawwad ya dakko musu Abinci

Ilham CE ta fito tana taka kafa da kyar mummy ta kalleta
"Meyasameki kike taka kafa da kyar"
"Dutse na taka jiya a garden"
"Subhanallah bakiji ciwo ba dai ko?"
"A a banjiba kafar ce dai kawai take ciwo"
"To ko asibiti za a kaiki a duba kafar"
"A'a mummy zata dena ne Insha Allah"
"To shikenan ni zan fita ne zanje ganin likitan Ido, ga breakfast can na gama in wancan Dan zeci yazo ya dauka kema kije ki dau naki"
"To mummy adawo lafiya"
"Allah yasa"
Mummy ta fita

Jalal ne ya dakko wayarsa ze kira daddy yaga message ya shigo wayarsa Dan haka ya bude message din bakuwar lambs ce

"Barka da safiya jarumin
maza fatan kana lafiya
Zanso ace a halin yanzu
Muna tare ina kallon wanna kyakykyawar fuskar
Amma lokaci na nan zuwa
Dazamu kasance tare kaji Dadinka masoyina
From ur lovely bae"

Wani uban tsaki Jalal yayi
"Nasan Ilham ce zataci kaniyarta zata gane innin sa,'anta ne"

"Ya dai meyafaru ne kake surutai haka"?
Jawwad ya tambaheshi
"ba komai ci abincinka kawai"
Ya mike ya nufi cikin Gida tundaga parlour yake kiran sunan Ilham amma bata nan dakinta ya nufa yana zuwa ya tarar tana dakinta tana karyawa
A firgice ta dago tana kallonsa

"Uban meye wannan kika turomin a waya wai meyasa ba kyajine Ilham"
Kallonsa tayi cikin rashin fahimta
"Wane sako kuma ni ban turomaka komai ba"
Ransa ne ya kuma baci wato raina masa hankali zatayi gadan² ya nufi inda take da niyyar ya ci kaniyarta
Ta mike tsaye tafara kuka tana
"Wallahi Yaya bansan laifin danayiba"
Yana karasowa Inda take yaji tana warin wannan turaren na jiya kansa ne ya Sara yaji yana Neman ya fadi, da sauri ta taho inda yake
"Yaya menene?"
"Dalla tsaya karki karaso inda nake"
Bango ya daddafa yabi kofa ya fice da kyar ya koma part dinsa Jawwad ne ya ganshi ya rike kai yana dafa bango
"Subhanallah Jalal kanne dai"
Jawwad yafada yana riko JALAL
"Jawwad kaina kaman ze fashe"
"Bari mu tafi asibiti ina key din motarka?"
"Kaga kyaleni bazani wani asibiti ba"
"Meyasa meye amfanin ka zauna a Gida baka da lafiya"
Guri Jalal yanema ya kwanta ji yake duniyar tanata jujjuyawa
Kai tsaye cikin gidan Jawwad ya tafi ya nufi part din daddyn Jalal yasameshi a parlour yana breakfast
Suka gaisa Jawwad yagaya masa halin da Jalal yake ciki, tare da daddy suka taho gaba daya part din Jalal
Suka tarar dashi a kwance yanata juyi akan gado ya rike kai Juyin duniya ya tashi su tafi Asibiti yace baza shi ba kunsan mutumin da taurin kai
Se wani likita aka kirawo yaimasa allura se yasamu yayi bacci

Alhamdilillah Jalila ita tazo na biyu a gasar musabaka da akayi tasamu kyautuka da dama kuma an karrama malamanta
Ita Jalila duk ba haka taso ba na daya taso tazo
"Duk wannan sakaran ne yajamin haka kawai naita mafarkinsa nazo musabaka ya hanani sukuni"
Haka taita mita suka kamo hanyar dawowa Kaduna suna murna amma ita haushi duk ya isheta
Har Gida motar makaranta takai Jalila, siyama tana gidan tana Jiran isowar Jalila
Ummi tana ganinta ta rungumeta tana murna, amma Jalila tai kicin² da fuska
"Lafiya kuwa babyna?"
"Ummi ta biyu fa Nazo"
Tafada kaman zatayi kuka

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now