ABDUL JALAL (2020)

Start from the beginning
                                    

"Nace fa bazani ba anemi wasu suyi ni bazani ba,"
Ta dau Jakarta ta bar ajin
Office malam Naziru yakoma yana mita
"Kajimin ja'irar yarinya nizata cewa bazata je musbaka ba wai anemi me zuwa"
Malam Yusuf ne yace
"Banga laifinta ba nan kuka sata a gaba da fada bama kai se yanzu kuma bukatarku ta taso kuce tazo tayi muku,
irin wannan yaran nasiha ake musu ba zagi ba duk abu suna da irin baiwarsu"
"Hmm ni ba wannan ba tunanin mafita nake kasan ta da taurin kai abune me wahala taja ga malam baya nan"

Jawwad ne ya tashi ya tafi amsa waya yayinda Jalal ya dukufa yana cin abinci saboda yunwar dayake Ji
"Masha Allah"
Wata budurwa ta fada, mikewa tayi daga inda take tazo kujerar gaban Jalal ta janyo ta zauna
"Sannu dai barka da wannan lokacin"

Dan dagowa yayi ya kalleta, ya maida kai ya cigaba da cin abincinsa
"Ehmm nace ba Dan Allah magana nakeso muyi da kai"

Still shiru yayi mata yaki magana haka tacigaba da surutun ta ko kallonta yakiyi
Jawwad ne ya dawo yasamu guri ya zauna
"Sannunku da fatan ban takura muku ba"
Jawwad yafada yana murmushi

"Mtseww kaga ci abunda zakaci mutashi mu tafi ni nagama kasan bana son kallo"
Jalal yayi maganar a fusace

"Dama yana magana?"
Budurwar ta tambaya
Dariya Jawwad yayi

"yanayi mana, gashi kuwa kinji"

"Amma nayi masa magana ya shareni"
Se Jawwad yai niyyar tsokanar Jalal
"Au be kulaki ba, aikuwa yana magana, haba bros ya zata na maka magana ka shareta"

Wani takaici ne ya tokare wa Jalal shi Sam baya San sabga da mata dan haka banza yai musu
"Au bazakayi maganar ba kuwa"
"Inaga nidin ce baze kulaba, ba komai nagode"
Ta mike zata tafi
"Kiyi hakuri fa Dan uwan nawane se a hankali"

Murmushi tayiwa Jawwad sannan ta mike ta bar gurin
Wani uban tsaki Jalal yayi yana hararar Jawwad
Sunkuyar da kai Jawwad yayi yana dariya Jalal ji yayi kamar ya naushi Jawwad
Haka Jawwad yagama cin abincin suka nufi Gida

Tunda Jalila ta koma gida sedata shafe kwana uku bata zuwa makaranta
Ummi tayi² tagaya mata meyasa bata zuwa makaranta amma taki, kullum seta ce mata bata da lafiya,
Seda malam Naziru da wasu malamai suka biyo Jalila har Gida akan takoma makaranta saboda batun musabaka
Ummi tace musu ba komai indai Jalila ce zataje musabakar insha Allah sukayi mata godiya suka tafi
Ta dawo Gida taitama Jalila fada meyasa zatace bazatayi musabaka ba har malamanta su biyota Gida suna lallabaki
Dan tsuke fuska Jalila tayi
"Ummi bakiga abunda sukayimin ba suka dinga min masifa kuma se yanzu yawani zo wai inje musabaka wallahi Dan kinsa bakine kuma Dan malam babba zani wallahi da bazanje ba"
"To yanzun ma kice bazakiba mana in dai za a biyewa halinki ai kullum se an zanekima ba fada ba"

Kayan da Jawwad yabashi yasaka ne duk suka isheshi da zafi Dan haka suna dawowa gidan su ya wuce domin ya canza wasu kayan zuwa kananan kayan daya saba sawa
Yana bedroom dinsa yana kokarin canza kaya yaji motsin Ilham a palour zata kwashe Warmer's din data kawo masa abinci, bubbudewa tayi taga baici ba
Fitowa parlour yayi ya tsaya a bakin kofa Dan dago kai tayi ta kalleshi masha Allah wani irin kyau taga yayi me daukar hankali kayan sun masa kyau sosai ta Dan kura masa ido
"Ke me ye haka uban me kike kallo, saboda tsabar kin rainamin hankali kika kawomin wannan abincin, kuma kinsan banacin wannan abun amma kika dakko kika kawomin yaushe nafara wasa dake dazaki min wannan rashin mutuncin"
Yasalam ta manta baya cin cous²
"Am...am wallahi Yaya namanta....."
"Shut up kwashe su kibarmin daki sokuwa kawai komai kin manta shiyasa kike dakikiya both islamiyya da boko kanki Sam baya Ja fita ni"

Ai garani ina zuwa kaifa
Ta fada a zuciyarta ta kwashe kayan tana zumbura baki tana kunkuni
"Ke ni kikewa kunkuni na tattakaki wallahi kinsan halina sha³ kawai"
Sum² ta bar dakin

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now