ABDUL JALAL (2020)

Začať od začiatku
                                    

Yayi tari jini yana fitowa daga bakinsa
Usman ne yake share masa jinin yana masa sannu,
Sannan ya cigaba da cewa

"Kar kayi yinkurin raba baby da maryam yanzu, seta isa shiga Jami a nakeso takoma hannunka, sannan ka tabbatar in baby ta girma maryam takoma garinsu tanemi yafiyar iyayenta, nasan kafin nan sun huce daga fushin dasuke da ita baby taga dangin mahaifiyar ta
Tunda kaga mu kenan bamu dayawa,
Yayana bana so iyalina suyi maraicina in baby na ta isa aure kazaba mata miji nagari karka manta ka rike alkawarinmu dan uwana,
Kacewa innarmu ta yafemin, kagayawa maryam da diyata da soyayyarsu zan koma ga Allah"
Ya kalli Usman dake ta zubarda hawaye INA kaunarka Dan uwana"
Tarine yakuma sarke Aliyu yana numfashi da kyar
Kalmar shahada ya dinga nana tawa, sekuma yayi shiru jikinsa ya saki
Usman rungume gawar Aliyu yayi ya fashe da kuka seda yayi me isarsa sannan ya mike ya nufi dakin da aka kwantar da inna mairo, maryam ya gani a gabanta tana bata ruwa tana shan ruwan da kyar wani yana dawowa

Yana shigowa inna ta dago kai ta kalleshi tare da fadin ya mutu ko Usman, Aliyu na shima ya tafi,"
Ta fashe da kuka tacigaba da fadin
" Allah ya karbi bakuncinka Aliyu na yafe maka duniya da lahira
Maryam kikula da kanki ki rike mana Jalila kaima Usman kakula da amanar da Dan uwanka ya bar maka, maryama  karki manta da abunda nagaya miki inna mairo tayi maganar tana kuka tare da numfar fashi.

Lokacin da Aliyu yayi hatsarin aka kawoshi asibitin da inna take, an  turota a wheel chair ta dubashi,, tunda ta Ganshi taga halin da dannata yake ciki ta karaya jikinta ya kuma rikicewa,

Duk abin naan da ake Zainab bata taka kafarta Asibiti ta duba jikin inna Mairo ba balle Aliyu da ba Sa shiri

Da gudu maryam ta fita ta koma dakin da Aliyu yake ta tarar da shi an rufeshi da bargo dagaske dai Aliyun ta ya mutu
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un maryam ta dinga maimaitawa tare da silalewa kasa sumammiya
Kafin akawo motar daza a dau gawar Aliyu inna mairoma ta cika
*************************
    Ummi na zuwa nan a duniyar  tunani ta fashe da wani matsanancin kuka tare da furta Allah ya jikanka Aliyu na"
ta fada hankali.
  "Ummina kiyi hakuri idan magana ta ce tabata miki rai kiyi hakuri banyi Dan in bata miki rai ba "
Jalila tayi maganar daga inda take kwance ba tare da ta juyo ba Ummi bata CE mata komai ba taci  gaba da kukanta daga karshe ma ta fita ta dauro alwalaa ta tada salla

Washe gari da safe Jalila ta fuskanci still umminta bata walwala fuskarta ta kumbura saboda kuka
Jalila aikace² kawai take ba tare da ta kula ummin na ta ba seda tagama komai ta hado musu breakfast ta shiga dakin ta tarar da Ummi ta baje hotuna a gabanta tarike guda daya tanata kuka
Ajiye tray din hannunta tayi ta karasa gaban Ummi ta Sa hannu ta zare hoton da yake hannun ummin nata ta duba
Hotonta ne ita da Aliyu sun kalli juna suna dariya
Jalila ta dago ta kalli umminta, "

"Ummina soyayyar ce ta motsa kika Sa hoton abeena a gaba kina kuka,?"
Jalila tai maganar tana dan murmushi wanda iyakacinsa lebenta, saboda in da Sabo Jalila tasaba da ganin umminta ta dau hoton abeenta tasa agaba tana kuka, kokuma hoton family ta

Jalila ta cigaba da cewa

"haba ummina idan ina ganin karaya a fuskarki me kike tsammani daga gareni duk lokacin danaga hawaye a idonki karaya nakeyi ummina bana son ganin hawayenki kaddararmu kenan semu karbeta a haka muciga ba da hakuri Allah shiyasan abunda yake boye"

Jalila Tafada jikinta a sanyaye tana sharewa Ummi hawaye yayinda itama take zubda hawayen
Dukda karancin shekarun Jalila, in tana magana tana tsara zance daki² dukda tarin kuruciya dake dawainiya da ita wani lokacin tana tunani irin na manya

Riko hannun Jalila Ummi tayi tare da ajiyar zuciya,

"babyna Kidena kuka nima na dena ina tuna abubuwan dasuka wuce ne a baya Jalila bazan manta da halaccin mahaifinki ba a gareni, da kakaninki sunmin halacci ina miki fatan samun managarcin miji me kaunarki kaman mahaifinki sukuma Allah ya kai rahama kabarinsu"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now