ABDUL JALAL (2020) 7

Start from the beginning
                                    

"Ke Yar uwata ce Jalila ma Yar uwata ce ta shi kibarmin daki"

Jalila kam taji komai duk zancen da sukayi taji a bayan kofa ta jingina jikinta tana zubar da hawaye me kona zuciya
Jiki a sanyaye tayi wanka tafito wankan dabata da tabbacin tafita

Tana fitowa Nana ta kalli Jalila cike da damuwa zatayi magana saboda tasan taji abinda Sa'ada tafada

Amma Jalila cikin karfin hali da dakewar zuciya tace
"Nanancy yau me za a girkamana ne ne yau?"

"Kinga Jalila Dan Allah.........

Jalila katseta tayi ta hanyar cewa
" yau muyi dambu kinsan mutumina ne amma Allah yasa kin iya Dan kinsan nafiki iya girki"

Duk yadda Nana taso suyi zancen maganganun da Sa'ada tayi domin tabata hakuri Jalila taki se ta basar da zancen

Jawwad kam yakada ya raya Jalal ya bishi suje masallaci yaki yace shi inyaje Gida yayi sallarsa
Haka Jawwad ya tafi massalaccin shikadai
Bayan yadawone yace bari yaje cikin gida yakuma duba Jalila Dan haka ya nufo cikin gidan

Nana ta kalli Jalila tace
"Maama kuwa tasan kindawo"?

"A'a naga tayi bakuwa shiyasa banjeba kar in takuramata" Jalila tabata amsa
" bafa wata bakuwa bace Yaya mairo ce yakamata tasan kin dawo ai "
"Hakane bari inje"

Yana shigowa palourn ya ga Yaya mairo da Sa'ada gefe ga Maama a zaune
"Yau manyan baki mukai kenan Anty mairo ina wuni"

"Eh kace haka mana yausha rabonka da gidana baka da zumunci Jawwad Sam wannan halin naka a dangin ubanka ka samo shi Dan mu bahaka muke ba"
Tafada cike da isa

Shikam har ga Allah Jawwad baya zuwa gidan yaya mairo dukda kasancewarta yayar mahaifiyarsa irin matan nanne masifaffu Wanda basa raina abin magana ga ta da mugun Sa ido kuma intana guri kawai so take abinda ta yanke shiza a yi ga shiga abinda ba ruwanta
Shiyasa Jawwad baya kaunar zuwa inda take yanzuma komeye na sako dangin babansa oho?

"To yanzu Dai Allah yabaki hakuri insha Allah hakan bazata sake faruwa ba insha Allah zaki dinga ganina har kigaji da zuwana"
"Kaji dashi dai"

"Maama ya jikin Jalilan kuwa?"

Ya fada cike da kulawa yana basar da zancen Yaya mairo

Maama ta Dan yatsina fuska
"Wace Jalilan kuma bayan wadda na baroku tare a asibiti "

"Maama to ai tun dazu muka dawo baki ganta bane?"

Har Jalila zata fita daga dakin "
Nana tace tsaya mutafi tare karki fadi a hanya"
"Hh Nana kenan yadda nake jina yanzu ko dambe zamuyi ai sena zaneki yi zamanki bari inje"
Dariya Nana tayi lallai kinji sauki

   "Hmmm kingani ko dan Allah ji yadda yake wani nuna damuwa akanta jikar arna wallahi in baki wasa ba Zainab, yarinyar nan da uwarta se ta shanye miki ya'ya,
arna ba abun yadda bane karki tona sallar datake ganin idon mutane ne watakila a boye a can inda take ita da uwarta suna zuwa coci"

"Wlh nima bakiga wulakancin da Nana tayimin ba saboda wannan yarinyar hadda in fita in barmata daki"
Sa'ada ta tsoma baki, Sa'ada irin halinsu daya da uwata bata da kunya Sam
Daka ganta zakasan idonta a bude take fuskarta tayi Jawur saboda bleaching

Ran Jawwad ne ya baci matuka
"Haba Anty mairo wane irin cin zarafi ne wannan kuma hada mahaifiyarta wannan.......

" dalla rufemin baki sakarai Wanda besan me rayuwa take ciki ba ina magana kana gayamin wai cin zarafine, Yaya mairo ta katseshi a tsawace
Kingani ko Zainab kinga abinda nake fada miki ko kalli Jawwad ina fada yana fada saboda rashin kunya wallahi ki raba yayanki da waccan Yar arnan in ba hakaba wallahi wataran zaki gansu a church suma

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now