ABDUL JALAL (2020)

Start from the beginning
                                    

Wani Dan guntun murmushi Jalal yayi sannan yabi bayan Jawwad

  Itama Ilham ta karasa cikin Gida dan ta sanar da maama abinda yake faruwa

Suna zuwa suka tarar da Jalila kwance akan cinyar mummy bata numfashi, se kadan²

"Subhanallah Jalal bani key din motarka mu kaita Asibiti" Jawwad yafada da sauri
  Key din ya danka masa
memakon ya raka Jawwad sema ta shi da yayi yai ficewarsa

Jawwad beyi wata² ba ya dauki Jalila yayi waje da ita yasaka ta a mota ya tada motar kenan
Nana ta shigo  gidan ya tsaya ta Shiga motar

"Yaya maama tace muyi gaba zata taho in Abba ya dawo"
Be amsa mata ba yaja motar

"Ilham ki bisu mana kirakasu ko Asibitinne kinga ni badamar in fita yau babanku ya dawo" maama tayi maganar tana duban Ilham

"Ba inda zani wallahi Allah ya bata lafiya in nabisu ai bani zan bata lafiya ba"

"Haba Ilham amma ai a gidanmu abun yasameta"
"Ni wallahi mummy a gajiye nake ba inda zan iya zuwa yadda nagajin nan  hutawa nake sonyi"

Ta wuce daki abunta
"Ohh ni hadiza yaran nan se a hankali kowanne da halinsa
 
    Suna zuwa Asibitin aka karbesu aka shiga da Jalila emergency don ceto rayuwarta

  Wajen karfe Tara na dare Maama sukazo asibitin ita da Abba

Wanda yai dai²Da fito da Jalila daga emergency aka basu daki
Alhamdilillah numfashinta ya dawo dai² se dai tanata bacci ga drip da aka saka mata

" Allah sarki diyata Allah yabaki lafiya, Amma nayi mamaki iya sanina bata da wani ciwo makamancin haka"
Abba yafada cike da damuwa yana kallon maama
Dan tabe baki maama tayi

"A'a to ai ba dolene kasaniba watakila tana dashi mune bamu saniba kasan uwatta bakomai zata gaya mana ba tunda...."

"Ya isa haka Zainab.." Abba ya katse maama
"Yanzu lafiyarta muke fata ba wani surutu ba"

Likitan ne ya shigo domin kara dubata

Jawwad ne yayi gyaran murya
"doctor meyake damunta ne?"

"Eh blockage ne akasamu a airways dinta maybe ta kwarene ko kuma ta shide da wani abun,
Zatasamu lafiya insha Allah munyi mata allurai zatayi bacci karku damu Allah yabata lafiya" suka amsa da Ameen

Guraren sha daya na dare
Abba da Jawwad suka tafi Gida akabar Nana da da maama suka kwana a gurin Jalila

   Washe gari da sassafe Jawwad ya tashi ya shirya da nufin ya koma Asibiti, dayake motar Jalal a hannunsa ta kwana kafin ya wuce ya maida motar gidansu Jalal,
Jawwad ya tsaya  suka gaisa dame Gadi yayai masa yame jiki dayake yasan meyafaru,
ya" amsa da sauki,"

Jawwad ya juya zefita se yadawo da baya ya kalli me gadin
"Jalal yana nan ne"
"Eh yana nan yana bangarensa"
"Nagode"
Jawwad ya juya ya nufi part din Jalal Lamar kullum ya na kwance yayi dai² yana bacci babu alamar yayi salla
Jawwad ya daddaki pillown da Jalal yake kwance
A hankali Jalal ya bude ido

"Tashi kayi sallah Dan nasan bakayi ba"
Seda yadan ja seconds sannan ya tashi zaune yana hamma bece masa komai ba ya mike yaje
Yai alwala yagabatar da sallar asuba karfe 7:30am

"Jalal fushi nake da kai"
Jawwad yafada tare da Dan hade rai
Jalal ya kalleshi
"Why"
"Kanwata ba lafiya rai a hannun Allah amma ko ka tambayeni ya jikinta talk less of kace zaka min kara ka dubota to ni na roki arziki ka rakani Asibiti"

Dabeyi niyyar zuwa ba amma yaga in yai haka be kyautawa amininsa ba wato Jawwad Dan haka yace

"Sorry bross karkayi fushi dani bari in shirya muje"

Default Title - ABDUL JALAL (2020) Where stories live. Discover now