Default Title - ABDUL JALAL (...

By Ayshercool7724

56.5K 2.5K 216

Labarin wani matashi daya riga ya gurbata rayuwarsa da shaye2 da raina iyayensa, tareda wata matashiyar yarin... More

Abdul Jalal(2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 7
ABDUL JALAL (2020) 8
ABDUL JALAL (2020) 9
ABDUL JALAL (2020) 10
ABDUL JALAL (2020) 11
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 15
ABDUL JALAL (2020) 16
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 19
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 21
ABDUL JALAL (2020) 22
ABDUL JALAL (2020) 25
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 27
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 30
ABDUL JALAL (2020) 31
ABDUL JALAL (2020) 32
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 35
ABDUL JALAL (2020) 35
ABDUL JALAL (2020) 36
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 38
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 43
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 43
ABDUL JALAL (2020) 44
ABDUL JALAL (2020) 45
ABDUL JALAL (2020) 46
ABDUL JALAL (2020) 48
ABDUL JALAL (2020) 48
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 50
ABDUL JALAL (2020) 51
.ABDUL JALAL (2020) 53
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL part 2
part 2 55
ABDUL JALAL (2020) 56
ABDUL JALAL 57
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 59
ABDUL JALAL 60
ABDUL JALAL 61
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 63
ABDUL JALAL 64
ABDUL JALAL 65
ABDUL JALAL 66
ABDUL JALAL 67
ABDUL JALAL 68
ABDUL JALAL 69
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 72
ABDUL JALAL 73
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 74..
ABDUL JALAL 75
ABDUL JALAL 76
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 78
ABDUL JALAL 79
ABDUL JALAL 80
ABDUL JALAL 81
ABDUL JALAL 82
ABDUL JALAL 83
ABDUL JALAL 84
ABDUL JALAL 85
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 88
ABDUL JALAL (2020) 89
ABDUL JALAL 90
ABDUL JALAL 91
ABDUL JALAL 92
ABDUL JALAL 93
ABDUL JALAL 94
ABDUL JALAL 95
ABDUL JALAL 96
ABDUL JALAL 97
ABDUL JALAL 98
ABDUL JALAL 99
ABDUL JALAL 100
ABDUL JALAL 101
ABDUL JALAL 102
ABDUL JALAL 103
ABDUL JALAL 104
ABDUL JALAL 105
ABDUL JALAL 106
ABDUL JALAL 107
ABDUL JALAL 108
ABDUL JALAL 109
ABDUL JALAL 110
ABDUL JALAL 111
ABDUL JALAL 112
ABDUL JALAL 113
ABDUL JALAL 114
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL

ABDUL JALAL

1.3K 25 0
By Ayshercool7724

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 6️⃣1️⃣115

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

     

              _MY FIRST NOVEL _

Mummy tace "kai gidan Jalal fa nace zaka kaini"
Driver ya ƙara risina kai yace "eh Hajiya shi din fa, Jiya da daddare yazo layin nan shida matarsa, yace inje in kaisu filin jirgi yau, ɗazu na dawo daga kaisu"

Bata tsaya ta ƙarasa ji ba ta koma cikin gida kirjin ta yayi mata nauyi take tambayar kanta

"wace irin tsana Jalal yayi min har yazo layin nan ya tafi be ganni ba, be leƙo mun gaisa ba? Yazo shida matarsa suje gidan su matar sa amma suka kasa shiga su gaisheta, take ta kara jin wata muguwar tsanar Jalila tasan tabbas wannan makircin Jalila ne"
Da ta sake tuna cewar Daddy zeyi aure setaji gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi, tarasa me yake damun ta, kowa ya guje ta ya juya mata baya ciki hada dan cikin ta, ga dukiya tari guda, dukiyar da take ta hari tana kwaɗayi gata nan a jibge amma sam yanzu hankalinta ba'a kan dukiyar yake ba, da anjima kuma idan ta sake tuna irin masifar shaye2 da Jalal yayi, da yadda take riƙe da Ilham kaman ita ta haifeta ta tuna Abunda Saudat ta aikata mata se taji kaman a duk duniya ita ka ɗai aka tsana tarasa me zatayi taji daɗi, bacci ya ƙauracewa idanun ta, bata jin yunwa ma balle tasaka ran zata ci Abinci, idan tasa Abinci a gabanta za taci kuwa ji take babu test babu daɗi, bata da aiki se tunani da koke koke, Ankwace mata miji, wata ta kwace mata ɗanta ɗaya tilo se yadda tayi da shi, gashi 'yar uwatta data yadda da ita taci amanar ta tayi mata cutarwa mafi muni, ga ba wanda yake son rabarta saboda izzarta da jin kai da wulaƙanta mutane, nan da nan abubuwa sukayi mata yawa, ta fara fama da wani matsanancin ciwon kai da yake sakkowa har wuyan ta ko gani bata iyayi sosai, tunda Daddy ya tafi ko message be mata ba balle ya kira ta, saɓanin da da idan ya tafi se suyi waya sau biyu zuwa uku, yanzu ya tattara ta ya watsar ya shiga harkokin sa da shirye shiryen maida Auren sa.

7 hours cif su Jalila suka shafe ana tafiya a jirgi sannan suka isa London babban birnin England, Jalila ta gaji sosai tun ana tafiyar ta marmari tazo ta gaji, ta fara yamutsa fuska daga karshe ta kwanta a jikin Jalal tai bacci.

Jalal ya tashe ta suka sakko daga jirgin, yanayin weather garin ce ta tabattar mata lallai ta baro Nigeria, wani irin sanyi ne me ratsa jiki taji yana dukan ta, ta ɗaga kai tana kallon yanayin garin dukda dare ne amma tasan akwai banbanci da gida Nigeria, komai nasu cikin nutauwa da tsari, bayan sun gama clearing komai Jalal ya ja hannun ta sukayi gaba, wajen wata mota suka nufa kafin su karasa inda motar take aka bude motar na cikin motar ya fito.
Mahmud ne mijin Nana yazo ɗaukar su.
Cikin fara'a yace "Sannunku da zuwa bros nasan kun sha hanya, da ganin idon Jalila a gajiye take"

Jalal yace "wallahi kuwa a gajiye take sosai, muje ka kaimu gida seta huta gaba ɗaya"

Seda suka shiga motar sannan Jalila ta samu damar gaisawa da Mahmud har take tambayar sa Nana, dan a gajiye take sosai ga sanyi da a take ji gaba ɗaya ta dunƙule guri ɗaya a jikin Jalal.

Ya kaisu gidan daya kasance nan ne masaukin su, ya kawo musu Abinci daga gidansa sannan yai musu sallama ya tafi.

Jalila dai wanka tayi da ruwa me zafi ta shafe jikin ta da mai tasa ka kayan sanyi dan ta rage sanyin da take ji, shikam Jalal ko a jikin sa dan shi ya saba.

Lumshe ido yaga tana yi alamun bacci take ji

Yace "matar yakamata kici Abinci kafin kiyi bacci"

Tayi miƙa tare da tura baki gaba tace "ni ka nunamin ɗakina bacci nake ji"

"A waje zaki kwana idan baki ci Abinci ba"
Ya takura mata ya zuba Abinci ya zauna ya fara bata a baki, ji tayi gaba ɗaya Abincin babu daɗi, amma ta daure kar Jalal yaji babu daɗi taci kaɗan tace ta ƙoshi, shima be wani ci dayawa ba ya ajiye sukayi shirin kwanciya.
A zaton Jalila Jalal ze saurara mata ganin gajiyar tafiya da suka sha, amma tun a lokacin ya fara nasa honeymoon din, da ƙyar ta samu tai bacci Jalal ya tara mata wata gajiyar da bata shirya mata ba.

Abun mamaki Jalila se juyi tayi taga Jalal baya ɗakin, tsoro ne ya kamata ta tashi zaune tana rarraba ido, can se gashi ya shigo ya dube ta yace

"ba'a yin salla ne? Ko baki san Asuba tayi ba?"

Cikin tsiwa tace "Eh bana yi shiyasa jiya ka...." se kuma tayi shiru, dariya Jalal yayi yace
"ƙarasa mana, ya kika yi shiru?"

Ta ɗan murguɗa baki tace "bazan ƙarasa ɗin ba, Amma dan Allah ina kaje ne? Nifa har na tsorata"

"Sarkin tsoro, naje masallaci ne"

"Masallaci kuma? Dama akwai masallaci a wannan ƙasashen"

"Akwai masallaci hada na juma'a, ai suna da musulmi suma, akwai musulmi sosai a unguwar nan"

Jinjina masa kai tayi ta sakko taje tayi alwala tazo ta tayarda sallar Asuba.

Gari yayi haske sosai amma Jalila ba ta dena jin sanyi ba har yanzu, Yanzu ma Mahmud ne ya kawo musu Abincin safe suka gaisa sannan ya tafi, da Jalila ta fito tana kallon yanayin tsaruwar gidan, ba irin fasalin gidajen mu ne na Nigeria ba, hotunan Hajiya Salma ta gani a falon da su Mahmud tace "Zauje nan gidan Anty Salma ne?"

"Eh gidan ta ne, a nan Ummi tayi jinya ma gidan mijinta ne da ya rasu, Lokacin da yayi jakadanci anan aka bashi wannan gidan"

Jalila ta jinjina kai tace "to yana ga ban ganta ba?"

"ta tafi Maiduguri, Ranar Friday za'a maida Auren ta da Daddy, zata koma can Dubai gurin Daddy"

Jiki a sanyaye Jalila tace "dama dagaskene Daddy ze maida Auren nan? Allah sarki Mummy koya za taji? Dama baka bawa Daddy wannan shawarar ba, da ka bari da kansa in yayi niyya ya maida ita"

"Baby look, Daddy yayi haƙuri a zamansa da mahaifiya ta ni na sani, girma ya fara kama shi ya kamata ace ya huta, Mummy mahaifiya ta ce, Amma Soyayya kawai ta iya amma bata san wani abu respect ba, kuma Ya kamata Daddy ya maida Anty Salma saboda hakan shine dai2, yana son ta har yanzu, ko kin manta tun farko gidan tane Mummy ta shiga ta fidda ita? "

"Hakane Zaujee, Amma kishi babu daɗi, akwai ciwo me raɗaɗi"

"Jalila karki zama me son kai ban sanki da haka ba, Mummy a yanzu bata bukatar a tausaya mata, kamata yayi ta karɓi horo akan abunda ta aikata daga duniya"

"A'a zaujee, Macen da ta rasa soyayya da biyayyar ɗanta ya kamata a tausaya mata, please zaujee ka yafewa Mummy ka bata haƙƙinta na mahaifiyarka"

Ɗan lumshe ido Jalal yayi ya buɗe yace "Jalila a shirye nake da na karɓi mahaifiya ta in danne zuciya ta in manta da abunda ya wuce, Amma Abunda nake nuna miki har yanzu Mummy ba ta ɗau darasi ba, yanzu ina raɓarta zata fara kawo min abubuwa na son zuciya ta tursasni tace se nayi, ni kuma bazan biye wa son zuciyar ta ba, Jalila duk lalacewar ɗa yasan uwar sa, ko lokacin da nake shaye2 ina kaunar mahaifiya ta halayen ta ne bana so, sune suke ɓata min rai, halayen ta ne suka sa nake gudun ta ko inda take bana son zuwa, ko yau Mummy ta dena halayen ta marasa kyau zan mata biyayya, sedai bazanyi biyayya ga abunda nasan ze cutar dani ba"

Jalila ta yunƙura za tayi magana Jalal ya katse ta ta hanyar ɗora yatsan sa akan lips ɗinta yace "bana son jin wata magana, muci Abinci"

Haka Jalila tayi shiru ta kyaleshi.

Seda suka kwana huɗu sannan Jalal ya kai Jalila gidan Nana, babu nisa da inda suke da ƙafa sukaje. Nana tayi matuƙar farincikin ganin su, da ƙyar Nana take tafiya cikin ta yayi nauyi sosai.
Nana tace "Yaya Jalal tun ranar da kuka zo nake zuba ido amma baku zo ba se yau"

Jalal yace "yanzunma ba daɗewa zamuyi ba kuje minti biyar kawai ku gaisa zamu koma gida"

Mahmud yace "Haba dai brother ai ba zamu cinye maka ita ba" yai maganar yana murmushi

Suka dinga hira kaman wanda suka yi shekaru basu haɗu ba. Jalal da kansa ya bawa Mahmud labarin abunda ya faru a Nigeria. Nana ta kaɗu da jin abunda Ilham sukayi ita da Mahaifiyarta, Nana tace

"Allah sarki ashe shiyasa bata son Jalila ta tsane ta, kullum cikin faɗa suke"

Mahmud yace "Ai brother ka Auna Arziki, dama da mamaki ace lokaci ɗaya fa ka canza gaba ɗaya aka kasa gane kanka kasha wahala"

Jalal yace "munsha wahala dai, dani da Jawwad da Jalila, wato idan ina tuna wasu abubuwan da Jawwad yayi min a rayuwa har tunani nake anya Jawwad ba waliyyi bane? Jawwad ya wuce aboki a gurina, jinsa nake tamkar wani ɓangare na rayuwa ta, ya bani gudunmuwa a rayuwa ta, uwa uba matar so 'yar Aljanna wato wani abun idan na kalle ta har mamaki nake yi a ƙarancin shekarun ta ba kowace ƙwaƙwalwa ce zata iya tunani irin nata ba"

Sun sha hira sosai wuni sukayi a gidan Nana se dare suka tattaka suka koma nasu gidan.

Zuwansu ƙasar nan ba karamin yiwa ma'auratan daɗi yayi ba, suna more soyayya yadda suke so, Jalal ya kai ta gurare da dama na shaƙatawa da buɗe ido, wata irin soyayya yake nuna mata me cike da ban sha'awa, yayin da ita ma take dukkan ƙoƙarin ta gurin ganin ta faranta masa rai, gaba ɗaya sun manta da damuwar da suka baro a Nigeria, babban abunda yake damun Jalila be wuce yadda ba ko yaushe take samun irin Abincin da take so ba.

Kamar yadda Daddy ya faɗa ranar Friday ya maida Auren sa da Hajiya Salma, Mummy tana kwance tana fama da kanta wata ƙawarta wadda tasan wasu a family su Daddy ta kira ta, ta sanar da ita Auren Daddy hada bata labarin abunda Jalal da danginsa sukayi wa  mahaifiyar Jalila ai Mummy bata gama jin kanun labaran ba ta ajiye wayar ta miƙe zaune, kamar wata mara hankali ta kuma Janyo wayar ta hau danna lamabar Jalal amma seta tuna ba zata shiga ba tunda baya ƙasar, kenan ta tabbata Daddy yayi aure? Ji tayi numfashin ta yana sama yana ƙasa kaman ze ɗauke gaba ɗaya, ta lalubi wayar ta ta kira likita.

Kusan awa guda kafin likitan tazo,
"kiyi haƙuri Hajiya Khadija muna kan wani aiki ne shiyasa banzo da wuri ba, me yake damunki ne?"
Mummy babu baki sedai Nuni, likitar tayi gwaje gwajen da ya dace ta gano jinin Mummy yayi mummunar hawa, idan bata kula ba idan ta faɗi zata iya samun shanyewar ɓarin jiki.

Ta zauna taita bawa Mummy shawarwari amma sam Hankalin Mummy baya kan likita harta gama surutan ta tai mata allurai Mummy bata san me likitan tayi ba, ita dai tasan tana cikin tunani bacci ya kwashe ta.

Ilham an sallami mamanta daga Asibiti saboda ciwon ta bana Asibiti bane, Ilham tattar duk abunda suke dashi tana kai Umman ta gurin wasu 'yan tsibbun ko zasu dace amma abu yaƙi, daga ƙarshe ta ɗauki umman ta zuwa gurin wanda yayi Asirin farko shima ya tsufa sosai ko gani baya iyayi ya bayyana musu cewar

"Yawan karatun Al' qur'ani da kuma, zumar da Jalila ta dinga bawa Jalal ce ta illata Aljanin, sannan Jalila tana da tsari a jikinta sabo da riƙo da Al'ƙur'ani, shiyasa Aljanin ya samu nakasa kuma ya koma jikin Saudat, da an karya Asirin kafin Jalal ya haɗa shimfiɗa da Jalila da baze koma kan umman ta ba"

Ilham tace "Yanzu babu wata dabara ko wani abu dazaka iya yi mana akan wannan larurar"

"yarinya babu wanda ze iya yiwa mahaifiyar ki komai, sedai kukoma ga Allah ku zuba mata ido a haka, duk wanda yace ze muku magani ƙarya yake yi, tun a baya da yarinyar nan ta fara bibiyar sa na nusar daku, Amma kuka gaza ɗaukar wani ƙwaƙwaran mataki, yanzu se dai kuyi haƙuri"

Haka Ilham ta tattaro suka dawo gida, ba wani me basu wani taimako musamman idan akaji abunda sukayi, yayan Ilham yana prison baban su kuwa idan ya shura ya bar gida se ya shekara uku be zoba, ga dangi da 'yan uwa dama ba wani jituwa ake ba, Saudat bata ganin kowa da mutunci dan haka ba wanda ya damu da halin da suke ciki, a hankali komai nasu ya fara ƙarewa saboda jinya, ga Ilham ta fara gajiya taita hantarar Umman ta wasu lokutan, idan tayi ba haya ko fitsari a zaune setai tafiyar ta ta barta a gurin se ta daɗe cikin najasa sannan tazo ta kula da ita.
Abubuwa suka cakuɗewa Ilham abunda za suci ya fara nema ya gagare su, da dane da sedai tayiwa Mummy waya ta turo kuɗi, banda wanda zata sata ta kawo gida, se yanzu take dana sanin abunda tayi, da ta sani da ba ta ga yawa duniya su sukayi wa Jalal Asiri ba da koba komai baza su rasa Abunda za suci ba.

Jalila tana kwance a jikin Jalal tana chatting taga surutun da ake a group ɗinau na makaranta yayi yawa dan haka ta sauka ta shiga domin ganin surutun me sukeyi haka?

Sameera ce da Saleema 'yar gidan oga KB aka kuma kamawa a gidan karuwai suna aikata miyagun laifuka har an kaisu kotu an yanke musu hukuncin shekaru biyar a gidan gyaran hali.
Da sauri Jalila ta miƙe zaune tace "Zaujee kaga"
Ta nuna masa ya karɓa ya gani yace "Allah ya kyauta"

Jalila tace "Zaujee Saleema 'yar Oga KB ce, shi yana prison itama yanzu zata tafi prison na ɗauka tun a wancan lokacin ta shiryu"

Jalal yace "Jalila dan Allah karki saka damuwar wasu a ranki ki hana mana jin daɗi, shiyasa fa ban gaya miki su Hannah ma an kaisu prison ba, Sannan Jeje yayi rashin lafiya lungs cancer yai ta fama a prison ga rashin kula watansa guda da mutuwa, shima oga KB yana Aisbitin cikin prison paralyze ya kama shi"

"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un"
Shi Jalila ta dinga nanatawa ta kalli Jalal tace
"Zaujee me Jeje zeje ya cewa Allah, mutuwa ake tsoro dama, Allah ya karɓeka ba zato ba tsammani ba tareda ka shirya mata ba, Allah ya jiƙan musulmi"

"Ameen ya Allah, bance kuma ki zauna ki damu kanki ba, in kuwa naga kin damu na dena baki labari"

"to bazan damu ba" ta faɗa a sanyaye, amma ƙasan zuciyar ta so take tayi kuka

Seda sukai wata guda a UK sannan suka fara haramar tafiya, dama tana kewar Nijeriya sedai suyi waya da 'yan gida, ga shi tayi missing wasu abincin Nijeriya, dukda sun sha yawo sunsha soyayya sunyi ƙiba sunyi kyau daga ita har Jalal ɗin, sukaje suyiwa su Nana sallama.

Jalila tace "Yaya Mahmud yaushe Zakabar Nana tazo Nigeria gara ta haihu a Nijeriya"

Mahmud yace "Injiwa? Gara ta haihu anan semu taho Nijeriya"

Jalal yace "Sarkin wayo so kake yaronka ya zama citizen ɗin UK kenan?"

Mahmud yace "Ashe ka gane bros"

Haka sukayi sallama suka koma gida, Washegari ƙarfe goma Mahmud yaje ya ɗauke su ya kaisu airport sukayi sallama shi yakoma.

Maimakon  su sauka a Kano se suka sauka a Abuja gidan su Jawwad, Jalal be gayawa Jalila ba, ya dai ce mata ze kai ziyara Abuja sam bata kawo gidan su Hanan zasu ba.

Tana ganin Hanan suka rungume juna, cikin Hanan har yafi na Nana fitowa da girma.
Jalila taita tsokanar Hanan tana gwada yadda take tafiya, Jawwad kansa yaji daɗin ganinsu, gaba ɗaya sunyi ƙiba, Jalal kamar ba shine me yawo da Sarƙa, da askin banza a ka ba yayi ƙalau da shi ya zama babban mutum.

Jawwad ya ja Jalal suka fice suka bar su Hanan a gida, dukda ranar suka sauka Amma Jalila seda tayiwa Hanan gyaran gida da sauran abubuwan da bata iyayi, saboda tana shirin zata koma gida haihuwa.

Jalila se santin gidan Hanan take yi, ta fita ta ɗan zaga ta samu ƙanan guava sun faɗo ko nuna basu yi ba, take taji ranta ya biya ta tsinto tazo saka a leda ta jefa a jakarta, Hanan har mamakin ƙibar da Jalila tayi take
"Jalila anya ba'a gamu ba kuwa? Kinga yadda kika zama wata uwar mata"

Jalila tace "Aka gamu dame?"

"ciki mana" Hanan ta bata amsa

"An gaya miki kowa irinku ne, bani da komai hutawa ta nake"

Hanan tai murmushi tace "to me yake hanaki cin Abinci se kin zaɓa?"

Jalila ta ɗan yamutsa fuska tace "ke nifa ba abunda yake damuna, ni ba laulayi nake ba, bani da komai tunda muka bar Nijeriya komai ya dena min daɗi ne kawai Abincin su bana jin daɗin sa ne"

Hanan ta ƙyale Jalila dan tasan ta da taurin kai.

Kwanan su Jalila uku suka baro Abuja zuwa kano, Hanan kuma  ta tafi Bauchi a can zata haihu, tunda suka taho Jalal yake lura da Sam Jalila bata son Abinci se dai ciye ciyen shirme, ga bacci kamar wata kasa duk inda ta samu bacci, abu kaɗan ze mata ta fara kuka yanayin nata ya ɗan fara damunsa daya takura taci Abinci seta fara kuka ga yawan complain na ciwon ciki da take yi.

Haka suka dawo gida, kwanan su biyu da dawowa Jalila ta matsa masa suje yaga halin da Mummy take ciki, ba dan yaso ba ya shirya da daddare suka tafi.
Abunda ya basu mamaki be wuce yadda ta rame ba, da ƙyar take iya miƙewa ma bata da lafiya sosai.
Duk tsaftar Mummy amma gidan duk yayi ƙura, ko magana bata iyayi.

Suka ɗauke ta zuwa Asibiti, likitoci suka rufu akan ta saboda a galabaice take.
Jalal suna reception suna jira, ya hango doctor Salis ya miƙe yaje suka gaisa cikin fara'a doctor Salis yace
"Jalal keine ka koma haka? Kayi ƙalau da kai se jin labari nayi wai kayi aure daga kai har Jawwad ba labari"

Jalal yace "Aini nawa Auren ne yazo ba shiri, Mummy muka kawo Asibiti babu lafaiya, kuma muna tare da madam ɗinma kuwa dan Allah ka dubamin ita na kasa gane kanta"
Jalal ya nuna masa inda Jalila ke zaune tana danna waya, suka ƙaraso inda Jalila take doctor Salis yace
"kai wannan ai Jalila ce, ita ka aura Jalal"

"Eh itace"

"Allah sarki ashe shiyasa aka dinga yimin hanya2 ashe kaine a gurin, masha Allah, Allah yasanya Alkhairi ya baku zaman lafiya"

Suka amsa da Ameen
Suka bi doctor Salis office ɗinsa ya tambayi Jalila me yake damun ta tace "ni lafiya ta ƙalau, wannaan gobar da nake ci ce baya so"

Jalal yaiwa doctor Salis bayanin abunda take yi ya rubuta musu tests, yace suje lab ayi, da safe suzo su kawo masa  result ɗin.

A daren aka fito da Mummy, likita yai musu bayanin cewar hawan jini ke damun ta kuma ya fara taɓa mata zuciya dan haka tana buƙatar kulawa, ba ƙaramin damuwa Jalila ta shiga daa jin hakan ba, a daren Jalal ya maida Jalila gida yace bazata kwana a Asibiti ba bata da cikakkiyar lafiya.

Da safe Jalila tayi girki ta taho Asibiti bata jira Jalal yazo ɗaukar ta ba, da ta je ɗakin Mummy ba kowa a ɗakin, Mummy na kashingiɗe tana tunani, Jalila ta shigo da sallama tana gaida Mummy Amma Mummy tayi mata banza, Jalila ta zuba mata Abinci ta zauna a kusa da ita tace

"Mummy ki daure kici Abinci seki sha magani"

make plate ɗin Mummy tayi tace "ke wace irin mayya ce bazan ci ba, kina so ki ƙarasa ni kiji daɗin mallake min ɗa ko? To baki isa ba ki tashi ki bani guri"

Jalila ta girgiza kai tace "Mummy wallahi ni bawani abu da nakeyi dan in mallaki Jalal, ina ƙoƙarine kawai inga ya gyara rayuwarsa, Amma wallahi ni ba wani abu da nake yi in mallake miki ɗa" Jalila na cikin maganar ne Jalal ya shigo ɗakin yana murna gaba ɗaya ya manta da Mummy a gurin yace

"sweet heart yanzu naje gida ba kya nan, congratulations you are soon to be a mother"

Kallon shi tayi da mamaki "mother kuma"

"yes matar so you are 3 months pregnant"

Mummy ji tayi kaman ta mari Jalal taji tamkar ya soka mata mashi a ƙirjin ta.



Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️

What's app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724

Continue Reading

You'll Also Like

47.6K 2.9K 47
Na kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu...
220K 11.1K 90
Being flat broke is hard. To overcome these hardships sometimes take extreme measures, such as choosing to become a manager for the worst team in Blu...
85.9K 2.2K 32
A little AU where Lucifer and Alastor secretly loves eachother and doesn't tell anyone about it, and also Alastor has a secret identity no one else k...
7.7K 155 44
When walking home, Hinata is hit with a mysterious gas that transforms him into a girl in a matter of hours. As Hinata tries to navigate his new body...