Default Title - ABDUL JALAL (...

By Ayshercool7724

56.5K 2.5K 216

Labarin wani matashi daya riga ya gurbata rayuwarsa da shaye2 da raina iyayensa, tareda wata matashiyar yarin... More

Abdul Jalal(2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 7
ABDUL JALAL (2020) 8
ABDUL JALAL (2020) 9
ABDUL JALAL (2020) 10
ABDUL JALAL (2020) 11
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 15
ABDUL JALAL (2020) 16
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 19
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 21
ABDUL JALAL (2020) 22
ABDUL JALAL (2020) 25
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 27
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 30
ABDUL JALAL (2020) 31
ABDUL JALAL (2020) 32
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 35
ABDUL JALAL (2020) 35
ABDUL JALAL (2020) 36
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 38
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 43
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 43
ABDUL JALAL (2020) 44
ABDUL JALAL (2020) 45
ABDUL JALAL (2020) 46
ABDUL JALAL (2020) 48
ABDUL JALAL (2020) 48
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 50
ABDUL JALAL (2020) 51
.ABDUL JALAL (2020) 53
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL part 2
part 2 55
ABDUL JALAL (2020) 56
ABDUL JALAL 57
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 59
ABDUL JALAL 60
ABDUL JALAL 61
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 63
ABDUL JALAL 64
ABDUL JALAL 65
ABDUL JALAL 66
ABDUL JALAL 67
ABDUL JALAL 68
ABDUL JALAL 69
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 72
ABDUL JALAL 73
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 74..
ABDUL JALAL 75
ABDUL JALAL 76
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 78
ABDUL JALAL 79
ABDUL JALAL 80
ABDUL JALAL 81
ABDUL JALAL 82
ABDUL JALAL 83
ABDUL JALAL 84
ABDUL JALAL 85
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 88
ABDUL JALAL (2020) 89
ABDUL JALAL 90
ABDUL JALAL 91
ABDUL JALAL 92
ABDUL JALAL 93
ABDUL JALAL 94
ABDUL JALAL 95
ABDUL JALAL 96
ABDUL JALAL 97
ABDUL JALAL 98
ABDUL JALAL 99
ABDUL JALAL 100
ABDUL JALAL 101
ABDUL JALAL 102
ABDUL JALAL 103
ABDUL JALAL 104
ABDUL JALAL 105
ABDUL JALAL 106
ABDUL JALAL 107
ABDUL JALAL 108
ABDUL JALAL 109
ABDUL JALAL 110
ABDUL JALAL 111
ABDUL JALAL 113
ABDUL JALAL 114
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL

ABDUL JALAL 112

1K 26 0
By Ayshercool7724

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣8️⃣111

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com
Watpad @Ayshercool7724

_MY FIRST NOVEL _

Ummi ta rungume Jalila sosai a jikinta, Jawwad ya dakko ruwa me
Sanyi a fridge aka shafawa Jalila ruwan a fuska, a hankali Jalila ta bude ido tareda jero ajiyar zuciya ta sauke idonta akan Ummi, kara kankame Ummi tayi tareda sake fashewa da kuka.

Maama tace

"Jalila ba kuka zakiyi ba, kamata yayi ki godewa Allah ganin mahaifiyarki da kikayi"

Abba yace

"hakane yakamata ki godewa Allah sannan ki godewa mijinki da danginsa"

Kallon Abba tayi cike da rashin fahimtar abunda yake nufi

Daddyn Hanan yace

"gaskiya kam, mijinki ya cancanci yabo, da shi da danginsa, kuma kafa da kafa zamuje domin nuna godiyar mu da farincikin abunda sukayi"

Sam Jalila bata san inda zancen nasu ya dosa ba.

Ummi ta share hawayen fuskarta tace

"tabbas bayan godiya ga Allah daya nuna muku naku ahalin, zanyi godiya ta musamman bisa Jajircewarku da kulawa da tarbiyya yarinya ta, nagode Allah yasa ku dauka a gidan Aljanna, Jalila bata taɓa kukan rashin mahaifi ba sanadiyar tarasa wani abu ba nagode kwarai.

Tabbas Jalal yasan inda nake, lokacin dana bar ku nayi sallama domin zuwa garinmu, motar mu ta tsaya domin musulmin cinkinmu su gabatar da salla, bayan nayi salla ne na tsallaka wani restaurant na sai Abinci, na fito zan tsallaka titi mota ta bigeni, mutane suka fara taruwa a gurin, wanda ya bigeni dan sanda ne, dan haka ya nuna musu id card dinsa ya daukeni ya tafi dani.

Ya kaini wani Asibiti na kudi, inda aka tabattar masa dana samu matsala a kashin bayana, sannan nasamu internal injury akaina, lokacin da labarin bata na ya iskeku Jalal ya shiga zuwa offisoshin yan sanda domin an gaya masa dan sanda ne ya bigeni, Allah ya temake shi yasamo wanda ya bigeni yaje har Asibitin da nake, koda yaje yaga halin da nake ciki, yai magana da mahaifin sa akayimin visa zuwa Dubai a wani Asibiti, na dade ina jinya saboda aikin da'akayimin Kashi- kashi a bayana saboda matsalar dana samu.
Dana fara samun sauki Jalal yai magana da Hajiya Salma aka maidani Can England gurinta take jiyyata aka cigaba da bani kulawa a can.

Hajiya Salma ta zauna dani kaman 'yar uwatta, a gurinta na warke gaba daya, tun ina Asibiti Jalal yaso ya bayyana muku inda nake amma nahana shi saboda ina cikin mawuya cin hali, bayan na warke nai shirin dawowa Nigeria nacewa Jalal bana son kusan inda nake musamman Jalila, idan har Jalila tasan ina raye bazata taba yadda ta zauna a gurin Abban Jawwad ba, nikuma bana son Abunda ze shafi Addinin ta, Yarenta, da Al'adar ta, saboda ni dangina nada banbancin Al'adu da Addini, kuma yin hakan kaman na saba Alkawarin da nayiwa Aliyu ne kafin ya koma ga Allah.

Jalal da mahaifinsa, Hajiya Salma, wanda ya bigeni da Mijin Antyn Jalal me sunan Abeenki su sukamin rakiya har masarautar mu, Abunda ya bani mamaki be wuce yadda masauratar suka karbeni kai tsaye ba cike da kauna da girmamawa, sannan na tarar anbawa mutanen dake gidanmu damar kowa yayi Addinin da yake so ciki hadda musulinci, mahifiya ta ta musulun ta, kakana kuma ya rasu, Yaya na ke mulki yanzu"

Ummi ta kalli Jalila tace "Jalila ban guje ki ba, a duniya ina matukar sonki ke nake kallo in tuna Aliyu, nayi haka ne domin gyaran rayuwar ki, nayi haka don ki tsaya da kafafunki ko ba kowa tareda ke zaki iya rayuwa keka dai, kin koyi darusan rayuwa daban2 da nake ta nuna miki a baya kika kasa ganewa, lokacin da Jalal ya gayamin an daura muku Aure amma kince bakya sonsa, na shiga damuwa sosai, dan tuntuni nake miki Addu'ar samun miji nagari, kuma koda Ina jinya Jalalya gaya wa Hajiya Salma ta gayamin yana sonki, banji ina kin abunba saboda nasan kina son Jalal kema"

Ummi ta kalli Jalila tace

"Jalila tsawon lokacin dana dauka bana tare dake kowane lokaci kina raina ina miki addu'a a duk inda kike, zaki shiga damuwa idan kika ga halin da nake ciki na jinya, Amma Alhamdilillah naji dadin yadda naganki, Allah ya albarkaci rayuwar ku gaba daya"

Daddyn Hanan yace

"Masha Allah, Kinga abunda muke gaya miki tun a wancan lokacin ko 'yar Baba, yanzu da kin wulakanta Jalal da wani ido zaki kalleshi, ba ke kadai kikayi masa halacci ba, shima yayi miki, da fatan zaki kara rike mijinki ki kula da shi, duk da halayen Jalal na ki, Amma mutumin kirki ne, Abun mamaki duk yadda yake da Jawwad be sanar masa ba, se last month ya fada, watan mahaifiyar ki guda a gidan nan, kuma har can garin nasu muma munje, sannan munje maiduguri ma, Insha Allah a satin nan zamuje dake maiduguri kema ki musu godiya sannan muje kiga 'yan uwan mahaifiyar ki su ganki, dan munji dadin yadda suka karbemu cikin girmamawa da mutunci"

Jalila kasa magana tayi, yanzu take tabattar tayi wauta, da ta cigaba dayi wa Jalal rashin mutunci da wani idon zata kallesu, ta tuno yadda ta kusa bijirewa Auren, Allah sarki dukda halin bakin ciki data shiga a wasu lokuta a baya, Amma ga karamci da kauna da wasu mutane da bata hada dangi da su ba sukayi mata ba tareda ta sani ba, ga jajircewa da wannan dattawa da kokari da suke tayi a kanta da Mahaifiyar ta Abba da kuma Daddy Hanan.

Mikewa tayi ta tafi gaban Abba ta zube akan gwiwowinta ta riko hannunsa amma takasa magana sema wani kuka da ya sake kwace mata.
Ba wanda beji tausayin Jalila a gurin nan ba dan Hanan da Nana ma kukan suke taya ta.

Abba yace

"Jalila kukan ya isa haka, ai murna yakamata kiyi ba kuka ba, kar kanki yayi ciwo sarkin kuka kawai"

Jalila cikin kuka tace

"Abba narasa me zance, Allah ya biyaku ladan dawainiyar da kukayi dani, Ummi dan Allah ki bawa su Abba hakuri, naso na bijirewa maganar Auren da sukayimin a baya, Abba dan Allah kuyi hakuri ku yafemin, Sannan shima a bashi hakuri abubuwan da nayi masa"

Abba yace

"Ai baki bijire mana Ba Baby na, ba abunda kikayi mana, kinmana biyayya yarinya ce ke me matukar hakuri da biyayya, Allah baze tozarta ki ba Jalila, halinki daya da mahaifinki, sadaukarwa da kawaici Allah yayi masa rahama"

Daddy yace "in ce ko yanzu kina son nashi dai?"

Daga kai tayi alamar eh, seda ta basu dariya, amma babu Alamar Jalila zata sassauta kukan da take yi.

Maama tace
"zanyi Amfani da wannan damar in baki hakuri Maryam, na cutar dake da Jalila a baya, Amma nayi nadama, sharrin shedan ne da kuma zigar 'yar uwata, Amma daga baya nayi nadama, wallahi samun yarinya me halin Jalila se an tona, bata taba min rashin kunya ba duk abunda nake mata, dan Allah Maryam ku yafemin "

Ummi tace

"Haba Zainab, wallahi kin gama min komai a rayuwa, tunda kika zauna da Jalila kika rike ta, abubuwan da suka faru da ni da ita itace kaddarar mu, kuma ko yanzu Alhamdilillah, karki damu ni ban rikeki da komai ba, Allah ya yafe mana gaba daya"

Suka amsa da Ameen gaba daya, Babu alamar Jalila zata dakata da kukan nan, dan da kyar take jan numfashi ma.

Daddy ya kalli Anty fiddo yace

"fidausi ku kai yarinyar nan daki ta kwanta ta huta, wannan kukan ze iya jamata matsala"

Haka akayi suka kama Jalila zuwa daki suka kwantar da ita, suka kukkuna mata fanka, tana ta sauke numfashi.

Yusuf yayi mamaki, yaji labarin rayuwar Jalila da kuma waye Jalal, tabbas babu wanda ya dace da Auren ta se Jalal.

Seda aka kira likita yayi mata allura tayi bacci dan bata gane waye akanta, dan kukan da tayi ya saukar mata da zazzabi me zafi da ciwon kai.

Ilham ta shirya ta tafi gidan su Yaseera, tana zuwa tayi sa'a yaseera tana nan, suka gaisa da babar su yaseera sannan suka wuce Dakin ta, suna shiga yaseera ta kalli Ilham tace

"Ilham abun har ya kai haka? Kinga yadda kikayi duhu, kin wani rame ko baki da lafiya ne?"

Ilham tace "wallahi Bani da lafiya yaseera, Amma ban damu da rashin lafiyar ba, ina cikin damuwa kuma mafita nake nema cikin gaggawa ko wace iri ce"

Yaseera ta gyara zama tace "ina jinki, nasam dai ta tsuniyar gizo bata wuce koki, akan Jalal ne ya ake ciki? Har yanzu baki hakura ba?"

"ta yaya zan hakura yaseera, kinsan son Jalal ya zame min bala'i?"

"ban gane ya zame miki bala'i ba, ina dama can soyayya ta shiri ce zakuyi dan ya aureki?"

"yaseera wallahi ashe son gaskiya nakew Jalal ban san hakan ba seda yayi auren nan, Yaseera yarinyar nan muguwar player ce, wallahi soyayya suke kamar ya hadiye ta, Yaseera uwar sa fa yake gayawa wallahi ko a gaban waye se ya fada yana son matar sa, Yaseera zan iya rasa raina saboda yadda soyayya Jalal ke kara ruruwa a raina"

"tabdijan Ilham kinga da Jalal yana jin maganar mahaifiyarsa to tabbas zata tirsasashi ya aureki, amma yadda yake din nan a duniyar nan babu me iya raba shi da ita, ni tun a baya na fuskanci abun nan nasu akwai soyayya a ciki, Amma nayi gudun in gaya miki saboda karki ji haushi"

"to yaseera meye abunyi yanzu?"

Yaseera tace "wane kokarin ummanki take akan lamarin"

Dan tsaki Ilham tayi tace "itafa kawai burinta ta dauki fansa, bata tausayawa halin da nake ciki, itama Mummy bata ni take ba, kawai burinta ta raba Auren"

Yaseera tace "to mafita daya ce a yanzu, Amma ban san yazaki kalli abun ba"

"nidai gayamin koma meye zanyi"

"kin san da bakinki kika gayamin asiri baya tasiri akanta, sannan tunda Jalal ya riga ya aure ta nasan sun hada shimfida, abu daya zuwa biyu zakiyi yanzu, ki cigaba da hakuri kiyi duk yadda zakiyi ki tabattar babarsa ta raba auren nan, sannan kije ki karya sihirin da kukayi masa, idan har ya karye zeji maganar mahaifiyarsa, in yaso se kiyi kokarin kiyi wani asirin da duk yadda zakiyi mahaifiyarsa ta tirsasashi ya aureki "

Murmushi Ilham tayi tace

"kin kawo shawara Yaseera nagode sosai"

"Amma kije kiyi magana da Umman kiji me zata ce"

Dan zare ido Ilham tayi tace

"wace Umman, wallahi bazata yadda ba tabdijan, tunda naga kowa kansa ya sani nima kaina zanwa fafutuka, ta taba bani labarin inda taje akayi asirin, zan Lalla bata ta kara gayamin yadda abun yake, sena karya asirin dan burina ya cika, nagode sosai yaseera"

Yaseera tace "shikenan Allah ya temaka" daga nan Ilham ta samu relief ta saki jiki suka sha hira.

Kiran sallar Asuba da'akayi ne yasa Jalila ta farka, Addu'a tareda fatan Allah yasa ba mafarki bane, Allah yasa Ummi ce da gaske, ta bude idonta ta juya, kamar yadda ta saba gani wasu shekaru da suka shude,
Da gudu ta sakko daga kan gadon dukda ciwo da kanta yake ta rungume Ummi gam.

Cikin kuka take cewa

"Allah yasa ba mafarki nake ba, Allah in bacci nake Allah kasa in dawwama inayinsa, Allah kasa a jikin Ummina nake, Ya Allah.. Ya Allah...

Ummi tasa hannu ta dago ta, dukda Ummi hawaye take sharewa tace
" Haba Babyna, ba bacci kike ba, nice Ummin kice, kalleni nice"

Kara rungume Ummi tayi dan ji take kaman in tayi wasa Ummi zata kuma tafiya ta batta.

Dakyar Ummi ta lallaba Jalila tayi salla tana idarwa ta kuma kwanciya a jikin Ummi tace

"Ummi meyasa kikaki ki bari in san inda kike, inyu jinyarki da kaina? Na shiga damuwa na shiga kunci, Nayi kuka a lokacin da babu me rarrashi na Ummi, meyasa Ummi?"

Ummi ta numfasa tace "Jalila a lokacin da nake jinya ko kinzo bazan ganeki ba, i partially loose my memory"

Mikewa zaune Jalila tayi tana kallon Ummi, Ummi ta jinjina kai tace
"tabbas Jalila na manta da abubuwa da yawa a wannan lokacin, But Alhamdilillah idan bani na fada ba, babu me gane hakan se su Jalal da suka san nayi, da Mahmud tunda a gidansu nayi jinya"

"yanzu Ummi Yaya Mahmoud ma yasan inda kike amma aka rufeni, shiyasa ranar da ya fara ganina yace nice Jalila?"

"sosai makuwa, sannan duk iya shegen da kika dinga yiwa dana nasani, Inda Allah ya temakeki kema kinyi rawar gani gurin sauya rayuwarsa, Tun kuna kanana na fuskanci Jalal yana matukar sonki, Har Abeenki yace Insha Allah in dai yana raye in har kina son Jalal ze bashi, Abun Allah, Allah ya kaddara ke rabonsa ce, Jalila duk mutumin daze soka tun baka san kanka ba wannan shine masoyi na gaskiya, babu abunda ze sameki ya guje ki"

"Amma Ummi me yasa baki gayamin a baya ba?"

"ta yaya zan gaya miki? Kina fama da rashin ji da tsiwa, a lokacin ma ga abunda kike masa inaga na fada miki, Jalila hatta mafarkin da kike da Jalal nasani, kiyi ta surutai cikin bacci, nidai na dage muku da Addu'a ne"

Dan murmushi Jalila tayi
"tabbas Ummi Addu'a ki bata fadi kasa ba, Amma Ummi na sha wahala wallahi, naga kalubale daban2"

Nan ta labartawa Ummi wasu daga cikin gwagwarmayar da tayi, daga karshe tace

"Ummi da muna mutunci da Mummy sosai, Amma tunda Jalal yafara nuna yana sona ta tsaneni Ummi, kinga cin mutuncin da takemin kuwa?"

"Jalila Kamar yadda Allah ya tsamoki daga cikin kaddara daban2, karkiyi tunanin shikenan, dole ki fuskanci wata kaddarar, Allah yana jarabtar bayinsa da yake sone dan haka ki gode Allah kiyi fatan Allah yasa ki cinye dukkan jarrabawar ki.
Sannan ba abun mamaki bane dan bata sonki, tunda inkika tuna abunda tayiwa kanwarta da suke uba daya, ke a wa daba zatayi miki ba? Tsoronta daya kar a mallake mata da, shiyasa take ganin ke matsala ce a rayuwar danta, duk kirkinki Jalila baze taba yuwuwa kowa ya soki ba, dole wani seya kiki, karki taba tunanin kowa seya soki, wani ze nuna a fuska yana kaunarki, Amma zuciyar sa babu wadda ya tsana kamar ke, sedai Jalila kiji tsoron Allah, yadda kika dauki aniyar sauya rayuwar Jalal karki sa ya kauce hanya, kar son da yake miki yasa kisa yaci gaba da fito na fito da mahaifiyarsa dan bata sonki, ki rike mijinki Jalila, Shi Aure idan ka samu wanda kake so ka iya tafiyar da shi yadda shari'a ta koyar, babu abunda ya kaishi dadi, shiyasa har gobe bazan manta Aliyuna ba"

"kai Ummi ko kunya ta ba kyaji?"
Ummi murmushi tayi tana girgiza kai,.
Jalila ta dan bata rai tace

"ummi Jalal tun kan ya tafi Lagos yace kar in kirashi har sati biyu wai bazata shiga ba, ashe abunda ya shiryamin kenan, dan Allah ki kiramin shi a waya, nasan ke ze daga naki Kiran"

Ummi tace

"A'a abunda yake so shi nake so, dan haka se kiyi hakuri se lokacin da yace, ai gara ya rama shima"

Jalila ta dan sunkuyar da kai tace "Ummi ina son ine nemi afuwar Jalal, tun kafin in san dawainiyar da yayi min dake, ina jin nauyinsa idan na tuna abunda na dinga yi masa a baya, dan ma wani abun baki sani ba"

Hira ce sosai Ummi da Jalila suka cigaba dayi, wani lokacin suyi kuka, wani lokacin suyi dariya, Ummi na ta kara yiwa Jalila nasiha, har gari ya waye yayi haske har kusan goma suna tare, aka fara shigowa duba Jalila, aka tarar Jalila ta ware tanata hirar ta da Ummi.

Warewa sukayi aka cika dakin suna ta hira da Ummi, Ummi se lallaba Su Hanan takeyi, Jawwad ji yake wani bangare na farincikin iyalansu sun dawo, koba komai Ummi ba abar yarwa bace, dan itace uwar rainonsu shida Jawwad, Amma shi kansa Jawwad ya sha mamakin abunda Jalal yayi.

Jalila tayi2 wayar Jalal ta shiga amma taki shiga, ta tura masa messages amma shima babu response, abun ya fara damun ta sosai, Harta E-mail dinsa ta tura masa sakkonni amma shiru.
Jalal kam yana sane yayi mata haka, in bahaka ba yasan halinta ta dinga tuhumar sa kenan, koma taita koke2 se ya dawo, wani lokacin ya kan bude system dinsa ya duba sakkonin Jalila,

"zaujee pick my calls please, i have a lot to say"

ire iren messages din nan dayawa a Gmail dinsa, murmushi yayi yace

"Baby na sarkin rigima, dama akwai ranar da zatazo kidinga nuna missing dina haka?"
Murmushi ya kara yi yace

"Yarinya se na rama tukuna, gara kema ki dana abunda nake ji"

Ya dauki wata wayar tasa daban ya kira Jawwad, yana kira Jawwad ya dauka, suka gaisa Jalal yace

"Jawwad ina matata ne? Fatan tana lafiya?"

"ban sani ba, ai kafini kusa da ita, ka wani kashe waya kana wahalar min da 'yar uwa"

Jalal yace

"ba ruwanka, kai waya dameka kai da matarka, kawai kuyi kallo, dan Allah Jawwad tana ina me take yi yanzu?"

"Wallahi tana cikin damuwa Jalal, tayi murnar ganin Ummi sosai, Sannan a gaban mutane take kuka tana a baka hakuri, har gurina tazo tana tambaya ta ko ina samunka a waya? Ba yadda na iya ka sanayi mata karya"

Hanan da take gaban Jawwad yana bata Abinci tace

"Jalal ka temaki sister na, ta horu fa, kullum se tayi zancen ka babu Adadi," Allah sarki Jalal dina, ko yaci Abinci? Ko yayi Adhkar dinsa? Da yana nan dai dai yanzu muke cin Abinci, Allah ya dawomin da shi in bashi hakuri" haduwar ta da Ummi be sa ta manta da kai ba, tana kewarka sosai fa"

Ajiyar zuciya yayi yace

"Allah sarki masoyiyyata wallahi nafi missing din ta, banyi haka dan ta shiga damuwa ba, wannan shine burina, Jalila ta hadu Ummi, bayan Ummi ta warke, nasan Jalila tana sona, Kaman yadda Hanan ke fada ne, tana da taurin kai, bata fiye yadda da abunda zuciyar ta tazo mata da shi ba, Hanan dan Allah ki cigaba da rarrashin ta, in dai na daga wayarta nasan kuka zata yi min, nikuma kukan ta yana tabamin zuciya, naji gobe in Allah ya kaimu zaku tafi garin su Ummi, Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya "

Jawwad yace

" Ikon Allah, ji yadda ya wani kashe murya yana gayamin yayi missing din matar sa, kaman ba shine me cewa Mata matsalane, soyayya shirme ce, to yanzu kuma mene? "

Jalal yayi murmushi yace
"a bayan ma duk basaja nakeyi in gaya maka, da zaka tona zuciya ta seka tausayamin, nayi zaton cire soyayya abune me sauki daga zuciya, amma duk lokacin da nayi yunkurin cire son ta a raina, se naji kaman ina kara azabtar da zuciya ne, gashi a lokacin bana ganin komai se kiyayya ta a idon Jalila, se kuma daga baya da Hanan ta nunamin son da Jalila takemin ne yasa take fada da kowa akaina, kishina da take yasa take bani Kariya da dukkan mummunan abun da ya tinkaroni, shiyasa na samu karfin gwiwa na cigaba da kaunar ta, ina son Jalila sosai, kai se anjiman ku, zan fita gurin aiki"

Jawwad yace "har ka gaji da zubar? Da labarin soyayyar taka?"

"ina fa? Ai labarine sakanni, awanni, da wuni, sati, watanni ko shekaru bazasu bada damar gama wannan Labari, me dadi da ban tausayi ba se an jimanku"

Murmushi Jawwad yayi
"A da in aka cemin Jalal yana wannan zazzafar soyayyar zan rantse ince karya ne, yau gashi kunne na yaji min"

Hanan tace "Ain dama tuni nasan yana kaunar ta, kuma itama tana sonshi, shiyasa nai tayi musu Addu'a, nikuma na kafa tawa soyayyar"

Jawwad yayi murmushi yace
"gashi nan an kafa min ita inda ba wanda ya isa ya ganta balle ya taba, mata ta abar Alfahari na, Allah ya rabaki da cikin nan lafiya dake da Nana"

"Ameen my lovely Haidar"

Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️

Continue Reading

You'll Also Like

40.1K 888 90
Continuation of Modesto story who happens to intercourse with friends,mature,classmates,strangers and even family...
1.4M 117K 110
Kalmar QADDARA kalma ce dake rataye bisa wuyan kowanne bawa,haka rayuwa ta gada,tafe take da QADDARORI kala kala,masu zaqi da akasin haka...
215K 1.5K 53
Sa muling pagkakataon subaybayan natin si Jude sa Malibog nyang kwento.At ang nga masasaya,malulungkot at nakakaiyak nyang karanasan. This story c...
7.2K 517 52
Labari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha...