Default Title - ABDUL JALAL (...

By Ayshercool7724

56.1K 2.5K 216

Labarin wani matashi daya riga ya gurbata rayuwarsa da shaye2 da raina iyayensa, tareda wata matashiyar yarin... More

Abdul Jalal(2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 7
ABDUL JALAL (2020) 8
ABDUL JALAL (2020) 9
ABDUL JALAL (2020) 10
ABDUL JALAL (2020) 11
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 15
ABDUL JALAL (2020) 16
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 19
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 21
ABDUL JALAL (2020) 22
ABDUL JALAL (2020) 25
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 27
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 30
ABDUL JALAL (2020) 31
ABDUL JALAL (2020) 32
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 35
ABDUL JALAL (2020) 35
ABDUL JALAL (2020) 36
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 38
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 43
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 43
ABDUL JALAL (2020) 44
ABDUL JALAL (2020) 45
ABDUL JALAL (2020) 46
ABDUL JALAL (2020) 48
ABDUL JALAL (2020) 48
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 50
ABDUL JALAL (2020) 51
.ABDUL JALAL (2020) 53
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL part 2
part 2 55
ABDUL JALAL (2020) 56
ABDUL JALAL 57
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 59
ABDUL JALAL 60
ABDUL JALAL 61
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 63
ABDUL JALAL 64
ABDUL JALAL 65
ABDUL JALAL 66
ABDUL JALAL 67
ABDUL JALAL 68
ABDUL JALAL 69
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 72
ABDUL JALAL 73
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 74..
ABDUL JALAL 75
ABDUL JALAL 76
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 78
ABDUL JALAL 79
ABDUL JALAL 80
ABDUL JALAL 81
ABDUL JALAL 82
ABDUL JALAL 83
ABDUL JALAL 84
ABDUL JALAL 85
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 88
ABDUL JALAL (2020) 89
ABDUL JALAL 91
ABDUL JALAL 92
ABDUL JALAL 93
ABDUL JALAL 94
ABDUL JALAL 95
ABDUL JALAL 96
ABDUL JALAL 97
ABDUL JALAL 98
ABDUL JALAL 99
ABDUL JALAL 100
ABDUL JALAL 101
ABDUL JALAL 102
ABDUL JALAL 103
ABDUL JALAL 104
ABDUL JALAL 105
ABDUL JALAL 106
ABDUL JALAL 107
ABDUL JALAL 108
ABDUL JALAL 109
ABDUL JALAL 110
ABDUL JALAL 111
ABDUL JALAL 112
ABDUL JALAL 113
ABDUL JALAL 114
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL

ABDUL JALAL 90

398 23 3
By Ayshercool7724

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 3️⃣7️⃣90

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com




_MY FIRST NOVEL _

"wakenan?" ya tambayi Mummy yana kallonta

"eh da ita yarinyar daka dawo dan ita mana, tunda tana maka abunda bana maka, wallahi kaji tsoron Allah, ba irin Magiyar da banyi maka ba, Amma kayi biris amma yanzu dayake tafini ai gashi kadawo"

Tsyawa yayi ya zubawa Mummy ido tagama masifarta, seda tagama, Yayi tsaki ya tashi ya fice yana masifa.

Haka yakoma dakinsa yana mita yana tunanin meyasa ma yaje inda take, Mummynsa bazata canza hali ba, Jalila tana matukar girmama ta, amma ta rufe ido se masifa takeyi, shiyasa bayason rabar Mummynsa.

Jalila tanata lissafi gobe su Abba zasu dawo, dan haka ta tsananta Addu'a Allah yabata sa'a yasa Abba ya janye batun Aurawa Jawwad Naja.

Yauma Jalila taje school, sun kammala lectures, sunfi to itada Zahra, Zahra tace

"Yawwa nikam Jalila naji Wata suna hira tace wai jiya wani hadadden gaye yazo yasaki a mota ya tafi dake, amma wai dagani dan shaye2 ne dan wuyansa hada sarka, ga wani irin Aski akansa, ina fatan lafiya ba wata matsalar bace?"

Dan karamin tsaki Jalila tayi aranta tace"
dan jaraba da masifar mutane komai kayi idonsu akanka
"Eh haka akayi, seme kuma?"

"A'a ba komai dama nayi tunanin ko mutanen baban Saleema ne"

"to basu bane, Yayana ne"
Jalila tabata amsa a takaice, Dan zare Ido Zahra tayi

Zahra tace "dama kinada yaya dayake shaye2, na zata Yaya Jawwad ne kawai Yayanki"

"Akwai wani to, kuma akansa nayiwa Alhaji Kabiru baban Saleema, abunda yanzu yana daf da zuwa prison shida 'yan tawagarsa"

"Amma Jali....

" Ke zahra kin isheni wallahi, nagaji ga yunwa ina ji se faman tambayoyi kikemin, sekace wata likita, haba se Allah ya kaimu gobe"

Inda sabo Zahra tasaba da halin Jalila, tanada saukin kai Amma tanada tsari a komai nata, in bakasan halinta ba zakace batada kirki ne kawai, bata da san yawan tambaya.

Mummy ta bawa Ilham kudi tace ta kaiwa Nana ta ajiyewa Maama in ta dawo a bata, Ilham ta karba harta shiga gidansu Nana wani tunani ya fado mata a rai, dan haka tayi murmushin mugunta tashiga gidan. Ilham Tana fitowa hakan yayi dai2 da dawowar Jalila daga makaranta sukayi karo a kofar gida. Ilham ta tsare Jalila da ido tana mata kallon zaki gamu dani ne.

Jalila tace "Ilham wai kin manta maganar danayi mikine? Ki dawomin da Al'qur'anina tun muna sheda juna dake?"

Ilham ta rike kugu ta kalli Jalila "idan naki fa? Me zakiyi?"

"Aimeyi baya fada se dai kigani a aikace, zakiga matakin dazan dauka, ki kawomin abina na gayamiki"

"ina jiran ganin matakin dazaki dauka din, amma kafin ki dauka ni ki saurari nawa"

Jalila tace "banida lokacin saurarar duk wani shirmenki, ba abunda kika isa kiyi min, nagama magana Ilham"
Jalila tasa kaii ta shige gida.

Kwana hudu kenan basu kara haduwa da Jalal ba, haka nan yaji yana kewarta sosai. Koba komai yayi missing neman maganar ta.
Sannan tunda abun nan yafaru tsakanin sa da Mummy be kuma shiga cikin gidan ba. Mikewa yayi yafito zetafi gidansu Jawwad.

Yana kokarin fitowa daga part dinsa Ya hango Ilham a jikin mota tanata boye kudi a jikinta, yana ganin haka yasan bata da gaskiya amma bebi takanta ba ya fice.

Jalila tana zuwa ta dire Jakarta ta shiga tayi wanka, ta fito tayi sallar Azahar ta kwanta bacci, se la'asar ta tashi, tayi sallar la'asar sannan taji tana jin yunwa.

Jalila tana zaune akan dadduma kafin tabar kan daddumar ta, Ahmad ya kirata suka dinga hira har kusan 40 minutes, Nana kallon ta kawai takeyi seda tabari tagama sannan tace

"Jalila wai dan Allah ina kika samo wannan Ahmad din, iya sanina ba kya son duguwar waya amma kalli yadda kika zage kina waya"

Jalila tayi murmushi sanna tace
"Nana a Bauchi na samo shi, yanada kirki sosai"
"kinga niba wannan ba magana nakeso muyi masu mahimmanci"
"inajinki amma ki hanzarta inajin yunwa"
"bawani in hanazarta, ki zauna kigama wayar se yanzu zakiji yunwa?
Jalila dan Allah ki gayamin hakikanin meke tsakanin ki da Yaya Jalal?"

Jin maganar tayi wani banbarakwai, batayi zaton jin wannan tambayar ba

"kamar yaya? Kinga wani abune da baki yadda dashi ba? Meyasa kikamin wannan tambayar"

"Jalila ruwa baya tsami banza yadda Ilham ke takura tsanarki tabbas wani abun tagani, tana claiming kuna soyayya ne, nima da nayi wani nazari zancenta yana kusada gaskiya"

"Mtseww niban san yakuke so inyi ba, da muna fada da shi, ance banida kunya inamasa rashin kunya, yanzu na dena ance ina sonsa to ya zanyi, Nana niba son Jalal nakeba, ina tausayinsa ne musamman danaji labarin waye shi, Nana a baya nikaina nasan na bata masa rai dayawa, yadda nake masa rashin mutunci da bakaken maganganu, naga ban kyauta ba sannam ba'a gyara da barna, muddin kanaso ka temaki mutum ya dena aikata laifi indai zakayi masa hayaniya baze dena ba, zaka kara tinzira shine, na fuskance shi yanada mataukar saukin kai, na gane hakanne a zuwan dasu Hanan suka danyi, Hanan gashi sa'ata ce, tafini tsiwa amma yana sakarmata fuska har yayi mata wasa, ita bata masa rashin mutunci kamar ni, shiyasa nima na sassauta yi masa wulakanci,
Amma babu soyayya tsakanin mu, ina fatan kin gane"

Mikewa tsaye Nana tayi tana shirin fita ta waigo tace

"Naji amma ban yadda ba" Nana ta fice daga dakin, tunani Jalila ta dingayi kozata gano wani dalili ne yasa ake kallon soyayya ce tsakanin ta da Jalal amma bata ganiba share wannan tunanin tayi ta mike ta fito itama domin neman abunda zataci dan ba karamin yunwa takeji ba.
Koda ta duba kitchen ba'ayi girki ba bakomai tayi tsaki ta fito daga kitchen din.

Daki takoma ta hado goldenmorn dinta ta fito farfajiyar gidan domin shan iska, tasamu kujera ta zauna tana cin Abincinta, Abba takira a waya yakara tabattar mata da gobe Insha Allah ze dawo, ji take kaman ta Jawo gobe Abba yadawo dan ta kagu ta dau mataki akan Naja.

Tanata wannan tunanin aka kira wayarta, A zatonta Ahmad ne amma se taga bakuwar lamba dagawa tayi tasaka a kunnenta tareda yin Sallama
Caraf taji matar ta Ambaci sunan ta

"Jalila yakike ya gida?"

"lafiya kalau Alhamdilillah"
"Antyn Jalal ce, nasan baki gane me maganar ba"
Murmushi Jalila tayi tace
"yi hakuri Anty ban dau muryarki bane, ya gida ya kukaje gida ranar"
"lafiya kalau nasan baki dauki muryata bane, Jawwad nakira nace ya turomin lambarki mudinga gaisawa, ya mutan gidan naku?"
"lafiya kalau Anty, yasu Mahmud?"
"Ahha Mahmud Nana zaki tambaya shi, muntafi da kwana uku yakoma U.K"
"Allah sarki, aikam kullum suna tareda Nana a waya"
"Aikam naga shi can nasa hankalin ya karkata, se fatan Allah ya tabattar da alkhairi"
"Hakane Ameen ya Allah"
"Jalila ya Amanata dana bar miki?"
Dan murmushi Jalila tayi tace
"Yana nan Anty"
"Kundena fadan dai ko?"
Murmushi Jalila takumayi tace "Anty kenan"
"Au kunya na baki? Jalila bamuda kalaman dazamuyi Amfani dasu gurin gode miki akan namijin kokarin da kikeyi keda Jawwad akan Dan uwanmu mungode Allah yasaka maki da Alkhairi"
"Haba Anty meye wani abun godiya kuma? Ni banga wani abu da nakeyi ba"
"inke baki ganiba mu mungani ai, ko iya yanzu kin taka rawa gurin canza abubuwa dayawa a tareda shi, munyi waya dashi yacemin daze bar kasar nan kika hanashi"
"hmm sa'a kawai nayi, nazata ma ze min duka, Allah yakara shirya shi, nima nagani ya rage Abubuwa sosai"

"Ameen Jalila, haba baze iya dukanki ba ai, he respect you fiye da yadda kike tunani, ki kulamin da amanata Jalila, inaji a jikina abubuwan da Jalal yake zezama tarihi sanadinki"

"Allah yasa, Munagodiya Jalila, Allah ya jikan magabatanki"

Jalila ita bataga me tayi ake mata wannan godiyar ba, Jalal din da banda fada ba abunda ke hadasu, dan haka Tace

"Anty yaushe zanzo abani turaren maiduguri ne? "
"Kibari in Aurenki yazo har kano zanzo in hadaki, kamshi sekin gaji, Allah ya nunamin Aurenki"
Dariya Jalila tayi ta kashe wayar, Antynsa tanada saukin kai, gata da abun dariya, Amma ita bataga me tayiba daza'ayita yimata wannan godiyar ba.

Washegari da safe Jalila bata tafi makaranta ba, seda tagama gyara gidan dan kusan kwana biyu Naja bata gidan, Halima dama Maama ta dade da sallamarta, Manu direba be dawo daga kai Nana ba, tunda ita Nana da wuri ta tafi school yau,
Taita gyaran gida, da kokarin dora girki saboda dawowar su Abba, be kamata abar gidan bakowa ba gashi ba'ayi girki ba.

ta fito ta leka part din Jawwad, taga inya tashi ta kaimasa Abinci, Amma ta hango Jalal yana shan sigari, Jawwad kuma baya palourn, da niyyarta ta fadawa Jalal bakar magana amma tafasa ta shiga palourn.

Batayi sallama ba unexpected ya daga kai ya ga Jalila, hade rai tayi sosai taki kulashi shima be kulata ba, ta duba ta kalleshi tace
"Ina Yaya Jawwad?"
"ki duba mana" yabata amsa a takaice
"Ina zan duba?" ta tambayeshi a ransa yace "lallai yarinyar nan kyaleta yayi bekuma kulata ba yanata shan sigarinsa, tambayarsa takuma yi
" wai yana ina? " takuma tambayarsa
"Zoki duba rigata kona sashi a ciki"

Bude baki tayi tana kallon sa, Jalal dan rainin hankali ne, amma ta shareshi ta dakko wayarta takira Jawwad be dauka ba, tsaki ta danyi taje tayi knocking kofar bedroom din Jawwad amma ta tarar yana bacci.

Mayarwa tayi ta rufe ta juyo zata fita, Amma Jalal bashida niyyar dena shan taba, gashi yana kallon boom TV ne music ne kawai yake tashi, yana shan sigarinsa yana lumshe ido, ya jingina a jikin kujera.

Dan girgiza kai tayi tazo gabansa ta tsaya ta dauki remote ta mayar saudi qur'an, bude ido yayi ya kalleta sannan yace

"Meye haka?"

"Abunda ka gani" ta bashi amsa

"mayarmin inda take da farko"

"Bazan mayar ba" dago Jan idonsa yayi yana kallon ta, wani tunani tayi a ranta, ta fuskanci fitsarar da take masa baya sashi dena abunda yakeyi, dan haka tace

"Ka karyane? Da safiyar nan kake shan sigari, kamanta me likita yace maka ne? Kobaka son lafiyar kane?"
Shiru yayi ya dauke kai, ba karamin haushi takeji tana masa magana ya mata banza ba amma ta dake tace

"Am talking to you, kamanta you said you want change, and i promise to help you out, please badanni ba a kashe sigarin nan please, na zata dena mu'amalarka da wannan jakin Jejen zesa ka canza kadena shaye2, amma meyasa har yanzu baka dena ba?"
Juyowa yayi yana kallonta, tayi kalar magiya, a hankali yace

"ba lokaci daya nafara shaye2 ba, don't expect me to stop it at once, Jeje ya dade yana cutar dani, na dade ina shaye2 bazan iya dena wa lokaci daya ba"
Tausayinsa ne yakamata, dan haka tace "I understand, kadena sha dayawa, a hankali zakaga ka dena" gyada mata kai kawai yayi, ta dan kalleshi maganar zahra ta tuna, da tace

"wani handsome guy, dan shaye2"
Ba karya Jalal yanada kyau, inama ba ya wannan shaye2, da seyafi haka kyau, Amma tana fatan Allah yasa abunda ta shirya akansa yayi tasiri ya dena shaye2.

"inaso kamin wata Alfarma"
"fade ta Allah yasa zan iya"
"zama ka iya, ba me wuya bace ba"
"inajinki"
"Dan Allah kadena saka sarkan nan, you are Muslim, bekamata ace kana yawo da itaba, da dinma nasan saboda Jeje ne kaima ka kwaikwaya please ka cireta"
Kallonta yakeyi amma bece komai ba, can kuma ba tareda ya cire sarkar ba yace
"meyasa idan aka kirani da dan shaye2 kike jin haushi bayan kema kina gayamin? Dan shaye2 mara tarbiyya wanda ya raina iyayensa, idan wani ya gayamin kinajin haushi, Amma kekina gayamin?"

Gaba daya taji jikinta yayi sanyi, har bataso ta tuna irin bakaken maganganun datake masa abaya, musamman idan ta tuna labarin Rayuwarsa tabbas tayi wauta, amma tace
"Waye ya kiraka da dan shaye2 naji haushi?"
"mutane dayawa, bari in tuna miki daya, Oga KB mahaifin Faruk, ban taba tunanin yadda kika tsaneni a wannan lokacin ranki ze baci dan anci zarafina baa"

Jalila tace "har yanzu kanajin haushin abunda nayi maka abaya ko?

" ko kadan gaskiya kika fada ai, banida tarbiyya, ban cancanci zama
Abokin yayanki ba kaddararsa ce tareda tawa shi.......

"Enough dan Allah, wannan abune daya riga ya wuce please"

Kallonta ya kumayi sannan yasa hannu ya cire sarkar wuyansa yace "Insha Allah nayi alkawarin bazan kuma saka sarka a wuyana ba"

Murmushi tayi "Are you serious"
"dagaske nake miki"
"kai gaskiya na yadda you want change, Allah ya shirye ka da gaggawa" murmushi yayi yace
"Ameen ya Allah"
daga nan ta mike tayi waje a ranta tace
"da haka Insha Allah kafin inyi Aure seka dena shaye2 in Allah ya yarda"

Yau fasa zuwa school tayi ta zauna ta shirya Abinci saboda dawowar su Mummy, bayan tagama ta kaiwa Jawwad nasu, ta gyra ko ina a gidan se kamshi yakeyi.
Bayan tagama komai ta zauna tana tilawar Alqur'ani, wajen karfe daya Abba suka dawo gida, ta dinga murna tana musu barka da hanya, duk hassadar mutum yasan gidan nan ya sha gyara amma Abba ne kawai ya yaba, Maama nunawa tayi bataga ma me akayi ba.

Bayan sunyi salla ta kawo musu Abinci. Takoma dakin su.
se la'asar Nana ta dawo daga school nan ta dinga murna su Maama sun dawo, Jawwad seda magariba ya shigo cikin gidan yayiwa Su Abba barka da dawowa, wannan karon kamar kullum Abba yarabawa kowa tsaraba sunata murna, sun hadu a palour ana hira.
Abba yace
"Jawwad ranar Asabar Insha Allah za'akai kudin Aurenka kamar yadda Maamanka ta bukata, inda wani shiri da kake ganin zakayi to kaje kayi, Jalal yagama komai next month Insha Allah zakafara zuwa gurin Aikinka"
Wani irin gumi ya dinga tsatstafowa Jawwad, yariga yagama karaya, sannan yana jin matukar kunya da nauyin ya bude baki yagayawa mahaifinsa baya son zabin da mahaifiyarsa tayi masa, Jalila ta kurawa Abba ido alamar bata gamsu da abunda yafada ba, Abba ya kalleta yace "ya dai 'yar Baba? Kokinada magana ne?"
Juyawa tayi ta kalli Maama data tsareta da ido, magana kam akwaita a bakinta amma ba' a gaban Maama ba, girgiza kai tayi alamar A'a, ta mike ta tafi dakinsu tanata safa da marwa, tana tunanin ta ina zata fara yiwa Abba bayani, tasan kotayi Maama karyata ta zatayi.
Gajiya tayi da sintirin datake taje ta bude wardrobe zata dau towel tayi wanka, ta bige wata jakar Naja ta fado bata saniba kayan ciki suka zubo dayake bata zugeta ba, a sama inner wears dinta ta dora a kai, amma kwayoyi ne da kwalaban syrup a cikin jakar, binsu da ido Jalila ta dingayi ganin yadda kayan suka tarwatse yayinda tayi mutuwar tsaye.

Ie
Da sauri ta durkusa ta tattare mata su ta mayar mata da jakarta yadda ta ganta, nan tunani yakara yiwa Jalila yawa bazata taba bari a Aurawa namiji kamar Jawwad wannan tanbadadiyar ba,ko Nana bata gayawa abunda ta gani ba, tayi shiru da bakinta.

Wasa2 duk yadda Jalila taso ganin Abba personally Maama ta kankane, ta tattare a part dinsa bata matsawa ko nan da can, seda aka kai kudin Auren nan, naira dubu dari Abba yaje ya kaimusu, su Yaya mairo hada kira wayar Maama tana mita wai duk Arzikin da Allah yayi musu amma ace kudin Aure akawo dubu dari, mecece dubu dari a kudin da suke dashi, Maama taita lallabata tace tayi hakuri zasu hade a kayan lefe.

Yayinda gefe abun duniya ya damu Jawwad, begayawa Hanan halin dayake ciki ba, ko Abinci baya iyaci, duk ya rame. Jalila da kanta taje ta dinga bashi kwarin gwiwar yacigaba da Addu'a komai zeyi dai2.

shikansa Jalal abun ya dameshi, meyasa za'ayiwa namiji Auren dole, ko mace be kamata ayiwa ba balle Namiji, shima Jawwad saboda nusaranci da kunya baze iya cewa baya sonta ba, wani lokacin kawaicin Jawwad yana batawa Jalal rai.

Jalal yanata tunanin wani taimako ze iyayiwa Jawwad, dan shima baze bari ayi wannan Auren ba, tunda Jawwad baze iyaba zeje yasamu Abba da kansa yagaya masa Jawwad baya son yarinyar nan, yana wannan tunanin yaji message ya shigo wayarsa,
Koda ya karanta, tsayawa yayi yanata juya message din shidai yasan tabass wannan message bana sa bane saba lamba akayi, dan haka ya barshi a matsayin anyi missing number ne aka turo masa, dan hukumar dasuka turo message din da sun san wayeshi sun san laifin dayake aikatawa da basu turomasa abunda suka turoba.

Jalila ta yanke hukuncin yau zata samu Abba ko agaban waye, zata nuna masa illar abunda yake shirin yi
Kai tsaye part din Abba taje, ta shiga da sallama a bakinta, ya amsa sallama sannan yace

"dama ina son ganinki, Baby ankaiwa yayanki kudi ze Auri 'yar uwassa, kune' yan mata kunfi sanin menene kuke so, kuma kuna tareda ita, maybe a kayan lefe akwai abunda takeso maybe ku tayi hirar daku, ba lallai tagayawa iyayen ta ba, dan haka inda wani abu da take bukata kokune tagayawa kota rubuto, saboda asan me za'a samata a kayan lefe"

"Abba wannan Auren fa bame yuwuwa bane?" mamakine ya kamashi yace "meyasa Jalila?"

"Baya sonta fa" Jalila ta faɗa kaman tayi kuka

Abba yace "Amma na kirashi na tambayeshi yace min ya yadda"

"Haba Abba zuwa yanzu yakamata kagane halin Yaya Jawwad, tunda kake ka taba nuna kana son Abu yace bayaso? Wallahi Abba Auren nan tamkar kasa hannune da kanka ka rusa doguwar tsaftataciyar katangar rayuwar Yaya Jawwad ne, Abba please kayi bincike"

"karya kikeyi bakar munafuka, ba wani bincike daza'ayi, yarinya 'yar dangice, me tarbiyya da sanin yakamata suna son junansu, Amma dan munafunci shine kike bata mata suna a gurin sirikinta, kedai Azzaluma ce, ni ina kudina ma da Mummy ta bayar akawomin? Ilham tace tabaki amma dan son zuciya baki baniba seda na buga waya aka gayamin ke aka bawa"

Daga Abba har Jalila tsayawa sukayi suna kallon Maama, Jalila takasa gane inda Maama ta dosa

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
What's app only 07063065680.
Follow me on watpad @Ayshercool7724

Continue Reading

You'll Also Like

7.1K 517 52
Labari mai saka rauni a zuciya bisa yarda aka yi watsi da zumunci aka martaba ku'di fiye da zumunci ta yarda ake gudun 'dan uwa makusanci a fi son ha...
27.8K 544 33
"I thought we were friends, Azriel. I was caught off-guard but you have to know it was forgiven the day it happened." The priestess looked back up to...
209K 1.5K 54
Sa muling pagkakataon subaybayan natin si Jude sa Malibog nyang kwento.At ang nga masasaya,malulungkot at nakakaiyak nyang karanasan. This story c...
278K 8K 135
"𝑻𝒉𝒆𝒓𝒆'𝒔 𝒓𝒆𝒂𝒍𝒍𝒚 𝒏𝒐 𝒘𝒂𝒚 𝒐𝒇 𝒘𝒊𝒏𝒏𝒊𝒏𝒈 𝒊𝒇 𝒊𝒏 𝒕𝒉𝒆𝒊𝒓 𝒆𝒚𝒆𝒔 𝒚𝒐𝒖'𝒍𝒍 𝒂𝒍𝒘𝒂𝒚𝒔 𝒃𝒆 𝒂 𝒅𝒖𝒎𝒃 𝒃𝒍𝒐𝒏𝒅𝒆."