Default Title - ABDUL JALAL (...

By Ayshercool7724

56.5K 2.5K 216

Labarin wani matashi daya riga ya gurbata rayuwarsa da shaye2 da raina iyayensa, tareda wata matashiyar yarin... More

Abdul Jalal(2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 7
ABDUL JALAL (2020) 8
ABDUL JALAL (2020) 9
ABDUL JALAL (2020) 10
ABDUL JALAL (2020) 11
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 15
ABDUL JALAL (2020) 16
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 19
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 21
ABDUL JALAL (2020) 22
ABDUL JALAL (2020) 25
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 27
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 30
ABDUL JALAL (2020) 31
ABDUL JALAL (2020) 32
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 35
ABDUL JALAL (2020) 35
ABDUL JALAL (2020) 36
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 38
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 43
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 43
ABDUL JALAL (2020) 44
ABDUL JALAL (2020) 45
ABDUL JALAL (2020) 46
ABDUL JALAL (2020) 48
ABDUL JALAL (2020) 48
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 50
ABDUL JALAL (2020) 51
.ABDUL JALAL (2020) 53
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL part 2
part 2 55
ABDUL JALAL (2020) 56
ABDUL JALAL 57
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 59
ABDUL JALAL 60
ABDUL JALAL 61
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 63
ABDUL JALAL 64
ABDUL JALAL 65
ABDUL JALAL 66
ABDUL JALAL 67
ABDUL JALAL 68
ABDUL JALAL 69
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 72
ABDUL JALAL 73
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 74..
ABDUL JALAL 75
ABDUL JALAL 76
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 78
ABDUL JALAL 79
ABDUL JALAL 80
ABDUL JALAL 81
ABDUL JALAL 82
ABDUL JALAL 83
ABDUL JALAL 84
ABDUL JALAL 85
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 88
ABDUL JALAL (2020) 89
ABDUL JALAL 90
ABDUL JALAL 91
ABDUL JALAL 92
ABDUL JALAL 93
ABDUL JALAL 94
ABDUL JALAL 95
ABDUL JALAL 96
ABDUL JALAL 97
ABDUL JALAL 98
ABDUL JALAL 99
ABDUL JALAL 100
ABDUL JALAL 101
ABDUL JALAL 102
ABDUL JALAL 103
ABDUL JALAL 104
ABDUL JALAL 105
ABDUL JALAL 106
ABDUL JALAL 107
ABDUL JALAL 108
ABDUL JALAL 109
ABDUL JALAL 110
ABDUL JALAL 111
ABDUL JALAL 112
ABDUL JALAL 113
ABDUL JALAL 114
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL

ABDUL JALAL

334 20 3
By Ayshercool7724

. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

              _ABDUL JALAL (2020)_

       _Story and written by_
      AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
        
   PART 2        
                          _PAGE  3️⃣3️⃣86

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com

     
          
         

   
          _MY FIRST NOVEL _

Kara hade rai yayi ya shiga palourn ya zauna becewa kowa komai ba ya zauna, daddy ya kalleshi yace
"son ka tashi lafiya"
"Alhamdilillah" daddy yai murmushi yace
"Masha Allah, kayi breakfast ne?"
"A'a ina jiran Jawwad ne kuma bezoba"

"bari a hada maka anan kaci" daddy ya kalli Ilham yace
"Ilham hadawa yayanki Abinci mana"
Jiki na rawa ta mike ta nufi dining din daddy ta hado masa kayan breakfast ta kawo ta ajiye, shidai be kulata ba ya zauna yafara cin Abincin sa, daddy suka cigaba da hirarsu shidasu Mummy, shidai Jalal bece musu uffan ba, yana kammala cin Abincin sa ya mike ze fita, daddy ya dakatar dashi ta hanyar cewa
"Ina kuma zakaje? Zamuyi magana ne ai"
Dawowa yayi ya zauna yana kallon daddy, daddy yace

"Jalal kaga zamanka haka baze yuwu ba, tunda ansamu degree daya da kyar, kaga shekarunka sun fara Ja daga kai har Jawwad zuwa yanzu yakamata ace ansama maka abokiyar rayuwa a matsayinka na namiji, amma bantaba jin kacemin ga budurwarka ba, ko akwai wata bansaniba "

Wani irin kallo Jalal yayiwa daddy sannan yace
" dan Allah adena wannan zancen, in lokacin Auren yazo za'ayi, amma dan Allah for now a kyaleni"

"A'a Jalal babu batun a kyaleka, banason cigaba da ganinka a haka ba Aure, bakasan Aure shine cikar mutum ba, inma baka da budurwa ne ga Ilham tace taji ta gani tana sonka a haka, meye laifin Ilham? Dan haka nakiraka tunda kaida Ilham duk dayane"

"A zato na a baya munyi wannan Maganar ta wuce? Wannan tamkar maida hannun agogo bayane, nace bana sonta, bana sonta akan me za'a takuramin, kuma ai naga Aure ba wajibi bane, balle ace in banyiba nayi laifi, dan haka a kyaleni bana sonta bazan Aureta ba"

A fusace Mummy tace

"Baka isa ba wallahi, da abun kunyar da kake shirin jawomana gara aimaka Aure, kokana so ko ba kaso Aure se anyi shi"

Jalal yace "Abun kunya na nawa kuma? Koke har yanzu abubuwan da nakeyi basu isheki kunya ba? Nagama magana ba wanda ya isa yamin Auren dole wallahi, duk duniya natasani wannan yarinyar natsani duk wani abu da yashafeta, Aurene bazan Aureta ba"

Ilham ta rushe da kuka tace "Nashiga uku Mummy, menayiwa Yaya Jalal haka?"
Mummy tace
"rabu dashi, Aurene babu fashi, tunda yasan yafara biye biyen mata, har karuwai sufara biyoshi gida, rashin mutuncin sa ya wuce yaje ya samesu a can, se yafara kawosu gida, ai dole a dau mataki akansa"
daddyn Jalal yaso ya hana Mummy karasa maganar amma seda ta karasa, Jalal dake shirin fita ya tsaya cak ya juyo

"Niza kiyiwa sharri dan nace bana son wannan shashashar, Nine nake bin mata, kirasa dame zaki alakanta ni se wannan mummunan Aiki, to wallahi da in Auri Ilham gara a dauramin Aure da Akuya, Nagode da sharrin da kika yimin a matsayinki na uwata"

"Ba sharri tayi maka ba Jalal, gaskiyane" juyowa yayi inda daddy ke magana, nan da nan idonsa ya canza ya harzuka matuka yace

"daddy da bakinka? Kaima ka yadda zannemi matan banza? Ka yadda ni Jalal zan kawo karuwa cikin gidan nan? Ka yadda ni Jalal ina neman matan banza, lalacewata bata kai haka ba" daddy yace

"Ya isa Jalal, ba sharri akayi maka ba, ni yarinyar tasamu a waje tace gurinka tazo, ita tacemin Akwai alakar dake tsakaninku wadda bata kamata inji ba, kuma lallai insaka Aureta shine kawai hanyar tsira da mutuncinta da naka, ka gayamin meye hakan inba neman mata kake ba?"

Shiruu Jalal yayi ya marasa meze ce, mamaki gaba daya ya kamashi, a iya tunaninsa babu wadda zatayi masa haka, su Jeje ne kuma zuwa yanzu suna hannu kodai duk shirin Mummy ne haka? Amma a tunanin sa be cancanci daddy yayi masa wannan mummunan zargin ba, ba tareda yayi bincike ba ana alakanta shi da dabi'ar dayafi tsana a rayuwarsa wato zina.

"Shikenan daddy naji na gode, Jalal danka mashayi kuma manemin mata,
Daddy da ina neman matan banza da lalacewar da zanyi tafi haka, da ba tun yanzu ba matan banza sun dade suna zarya a gidan nan, dukda Jawwad yana rufamin asiri a abubuwa da dama bana tunanin ze yadda ya zauna da mazinaci, shikenan nagode amma kusani Wallahi bazan Auri wannaan shedaniyar yarinyar ba"

Mummy tace

"dalla rufemin baki, kai har kanada bakin dazakace bakason Ilham? Ba rufamaka asiri zatayi ba, kanada bakin kiranta shedaniya ka.....

"Enough Mummy!!! Karki kara zagina waye silar komai, natsani Ilham natsani me sonta" yakarasa yana Zazzare ido, daddy yace
"Jalal ya isheka haka, danme zaka dinga cewa ka tasani yarinya metayi maka haka? Lokaci yayi da yakamata kadinga dagawa mahaifiyarka kafa"

Jalal yace "Daddy kayanke min hukunci bakayi bincike ba, kasan bana maka karya, nidai fatana kayi bincike kadena zargina, daddy kanamin uzuri a abubuwa da dama ban taba zaton haka daga gareka ba, sannan maganar Ilham wani abune daba lallai in gaya maka meyasa nace bana sonta ba, duk ku kwantar da hankalinku Insha Allah a satin nan zanbar muku gidanku, in bar muku kasarma gaba daya ku huta"

Ya juya a mugun fusace yafito daga part din daddy, gaba daya jikin daddy yayi sanyi tausayin Jalal ya kamashi, ya juya ya kalli Ilham yace "Ilham mekika yiwa Jalal ne yake miki haka?"
Ilham cikin kuka tace "daddy ni bansan menayi masa ba, yakemin wannan muguwar kiyayya"
Mummy ta dinga rarrashin Ilham.

Jalal kam tunda yafito yaji wani abu ya tokare masa kirji, dakin Jawwad ya tafi yana zuwa yatarar da Jawwad kwance akan gado ido a rufe, Jawwad yana kwancene zuciyarsa ba dadi yarasa yadda zeyi da matsalar ke damunsa, jin Jalal ya shigo ne yasa Jawwad ya bude ido, ya tashi zaune ya dake ya boye tasa damuwar ya kalli Jalal yace "Lafiya kuwa naganka haka meya farune?"

Kasa magana Jalal yayi, sedai jijiyoyin kansa da suka mimmike idonsa jawur, se huci yakeyi kai dagani kasan akwai damuwa sosai.
Jawwad yace
"ka gayamin mana meke faruwa?"

"Jawwad zan nemi visa, dole zan bar Nigeria a satin nan, kuma wallahi na tafi bazasu kara ganina ba"

"meyasa Jalal, meyasa zakace haka?"

"Jawwad nagama yanke hukunci, wannan karon karka cemin komai dan mutuwa ce kawai zata hanani tafiyar nan, zan bar Nigeria idan na tafi wallahi bazan kuma dawowa  ba".

A kwanakin nan sam Jawwad be gayawa Jalal shikuma tasa damuwar ba, sedai kokarin lallaba Jalal dayake yayi hakuri ammma fafur yaki se shirinsa yakeyi, sannan sam yadena shiga gidansu ya kashe wayoyinsa dan karma anemeshi.

Hanan da Jalila suna zaune suna hira da Inna a dakinta, Hanan tanata chatting ta dan dago ta kalli Jalila tace

"queen Haidar baya daga waya lafiya kuwa?" tai maganar a shagwabe
Jalila tace
"kunfi kusa ai, nima bamuyi waya ba"

"nifa duk na damu a satin nan sam banji muryarsa "

Inna tace

"waye kuma haidar, da kike kula dashi haka"?

Hanan tace "Sirikinki ne, kwanan nan zezo kiganshi kyakyawa dashi in gayamiki yafi mijinki Alhaji kyau, kai kaf family dinku babu me kyansa"

Inna tace "ke tafi can, anya akwai me kyan mijina, ai Imamu mijin Mairona ce kawai na yadda yafi mijina kyau"
Jalila da sauri tace
"Imamu kuma, shine mijin kanwartaki?"
"Eh shine shima dan uwanane, dan Autan su Imamu shine baban Hanan"
Jalila tace "Inna to wai ina suke yanzu ita kanwartaki?"
Inna ta danyi shiru tace

"bari yarinya ta, Mu ukune a gurin babanmu nida mairo da yayanmu magaji, ni na Auri Alhaji dan yayar Innar mune , itakuma mairo ta Auri Imamu, dan kanin babanmu ne, yana son mairo sosai, 'yan fashine suka addabi garinmu, watarana suka shigo suka harbi wasu, sukayi Garkuwa da wasu, akayiwa wasu daga cikin matan fyade aka kora dabbobinmu sannan aka sakawa bukkokinmu wuta, kafin hakan tafaru yayanmu magaji ya saida  wasu daga dabbobin gadonmu nida mairo yarabamana kudin, to lokacin da 'yan fashi suka shigo garin mairo da mijinta basu dawo daga kiwo ba, A wannan harin aka kashe yaya magaji, nida Alhaji da matar Yaya magaji, da yaranta da nawa yaran muka gudu abun be ritsa damu ba, haka muka baro garinmu muka taho nan bauchi, lokacin duniya na kwance akabamu masauki, muka cigaba da rainon yaranmu, bayan wasu shekaru A hankali bayan wasu shekaru muka dinga haduwa da wasu daga cikin  'yan uwanmu, duk inda mukaa hadu sesu sedawo nan gurin mu su zauna, a haka har mukayi wannan yawan, Amma har yanzu danake miki wannan zancen bansan inda mairo da imamu suke ba, ni ko bangansu ba inga zuri'arsu, Hanan tana matukar kama da ita, amma dana ganki senaga kunfi kama da ita, komai naki irin natane, Allah yasa ke irin zuri'arta ce" Inna ta fashe da kuka,
Jalila tace "Allah sarki inna, kiyi hakuri kinji Insha Allah zaki ganta ko 'ya' yanta, amma ni ban san kakannina ba inada kanan shekaru suka rasu, maybe da Yaya Jawwad ne ze iya sanin wani abun amma ni bansan komai akansu ba"

Suna cikin maganar Yusuf yayi sallama ya shigo, su Jalila suka gaiasheshi ya amsa, ya nemi guri ya zauna ya kalli Jalila yace
"'yar Baba kije palourn kasa, second floor kinada bako" gaban Jalila ne yai mummunar faduwa da sauri Hanan ta mike zaune tace
"Bako kuma?"
"Kece Jalila?" Yusuf ya tambayeta shiru Hanan tayi tana tunanin waye wannan kuma, ya biyo takan Yaya Yusuf, jiki a sanyaye Jalila ta mike, Hanan ma mikewa tayi zata biyo Jalila, Yusuf yace
"ke dawo nan ki zauna, koke nace kije?"
Hanan tadawo ta zauna ta zumbura baki, tana nazarin waye kuwa wannan?"
Jalila taje daki ta dakko hijjabinta har kasa tasaka, ta tafi a hankali ta tura kofar palourn ta shiga kanta a sunkuye tayi sallama.

"wa'alaikum salam warahmatullah" dan daga kai tayi ta kalleshi ido hudu sukayi tai sauri sunkuyar da kanta
Yace
"karaso mana queen" Jalila a ranta tace too queen kuma iyayi, ta karaso ta zauna a kujerar da take facing dinsa,
"barka da dare"
"yawwa barkanki dai my queen fatan kina lafiya?"
"Am not queen Jalila sunana"
Murmushi yayi yace

"to ai duk daya, koba haka Hanan take ce miki ba, kuma aini ya cancanta in fadi wannan sunan koba hakaba?"
Shiru Jalila tayi,
"to ya gajiyar biki?"
"Gajiya tabi lafiya Alhamdilillah"
"Masha Allah, ni sunana Ahmad nasan kinganni a bikin Yusuf, kobaki ganni ba nina ganki kuma kinyimin Jalila, nagayawa Yusuf ya nemamin izinin zuwa gurin ki a gurin daddy, daddy yabani damar inzo, sannan yace inmuka cika wasu sharuda sannan kin amince ze bani ke" ya danyi shiru sannan yace

"Jalila harga Allah kinyimin inasonki Aurenki nakeson yi tsakanina da Allah, amma bazan miki doleba se abunda kikace"
Shiru Jalila tayi tana wasa da yatsun hannunta
"queen kice wani abu mana
" still shiru tayi
"ko banyi miki bane? Ki gayamin ba komai, bazan miki dole ba"
Girgiza kai tayi alamar A'a yace
"to gayamin abunda ke ranki"
Fafur Jalila taki magana yai murmushi yace
"dago ki kalleni"
Noke masa kafada tayi kaman yanda yara sukeyi sannan tace "to ni me zance?"
"wow muryar ki da dadi Jalila, gaki shagwababbiya" murmushi ta danyi
Wayartace tafara ringing, ya kalleta yace
"daga wayar mana"
Ta daga wayar tasaka a kunne Nanace tace
"Baby ya kike dan Allah yaushe zaki dawo"?
"kai Nana wai yaushe zan dawo ba rana sena gama hutawa" Nana tace
"department dinku sukoma tun last week, nai shiru ban fadawa Abba kun koma ba, karyayi miki fada, sannan an kafe exams dinku yau"
"dagaske menasamu?"
"nidai nasamu upper credit, but Baby wallahi you are the most luckiest girl i ever seen in my life, kaf department dinku babu me points dinki, se zancenki ake, wasu sun sanki wasu basu sanki ba, lectures sunata a nuna musu ke"
"Alhamdilillah yanzu ina Yaya Jawwad kwana biyu baya daga waya?"
"Baby da banyi niyyar gayamiki ba, shiyasa naketa damunki ki dawo, Abba ya yadda Naja ta Auri yaya Jawwad, memakon yaya Jawwad yace masa bayasonta amma yayi shiru kinsan halinsa nan da kwana tara za'a kai kudin Auren sa gidansu Naja"

Jalila ta manta da wani Ahmad a gurin a razane tace "What, Nana dagaske kike dan Allah"

"Wallahi Baby dagaske nake, gashi yanata fama da Yaya Jalal shima wai ranar Asabar ze bar kasar nan, da se wani satin ze tafi, amma wani abun akayi masa a gidansu, yace wallahi inya tafi bazasu kuma ganinsa ba, ke yaya Jawwad yana cikin damuwa, gashi kusan kullum se Naja tasa anyi masa fada"

Mikewa Jalila tayi ta dafe goshinta tace
"Nana am coming back this week Insha Allah, Idan har Abba yabari akayi Auren nan an rusa Rayuwar Yaya Jawwad gaba daya, kuma ina tausayin Hanan, zan dawo a satin nan Insha Allah, dole afasa Auren nan"
Sukayi sallama da Nana ta mike zata koma cikin gida Ahmad yace
"Jalila lafiya kuwa? Naga kin shiga wani yanayi ko akwai damuwa ne?"
"A'a bakomai"
"Bari in kyaleki, nadawo na karbi lambarki zamuyi waya" gyada masa kai tayi ta fice da sauri.

Jalila na zuwa Hanan tafara yimata tambayoyi "Jalila wai waye Yaya Yusuf yace kinyi bako?"
"ke kyaleni dan Allah wani ne nina manta sunansa ma, Hanan satin nan, maybe nan da kwana uku zankoma Kano"
"Jalila meyasa? Saboda Yaya Yusuf?"
"A'a Hanan Akwai matsala ne, dole inkoma"
"Matsalar mene haka? Jalila kar mutan gidan nan su zargi ko wani lefi sukayi miki"
"bahaka baneba Hanan, Ankoma makaranta sannan ina bukatar zuwa gida"
Hanan tace "hmm ko dai saboda Jalal ne? Gayamin wani abune yafaru dashi ne?"
Cikin damuwa Jalila tace "Hanan dagaske Jalal yake in yabar kasar nan baze dawo ba, wai anyi masa wani abu a gidansu, fitarsa kasar waje hatsari ne" Jalila ta boyewa Hanan batun kai kudin Auren Jawwad kar Hanan ta damu.
Hanan taso ta tsokani Jalila amma ganin ta in serious mood yasa ta fasa tace "gaskiya yakamata kikoma bari daddy ya dawo se muyi masa magana"
Yusuf ne yayi knocking kofar dakin nasu sannan ya shigo da sallama ya kalli Jalila yace "Jalila yaya kun gaisa da Captain Ahmad?"
"Eh yaya Mungaisa"
"to bazamuyi miki dole ba, kigaya masa abunda ke ranki, inkinada wanda kikeso kigaya masa tun wuri"
"tana da wanda takeso fa, tana jin nauyin kane bata fada ba"
Yusuf yace
"inkika kuma magana sekinyi tsallen kwado sau sittin a gurin nan, dake nake magana?"
Shiru Hanan tayi, yacigaba da cewa

"Jalila banason mu cutar dake gidan nan ba'ayi wa kowa dole, nayiwa daddy maganar, in ba kyasonsa ki gaya masa kinji"
Jalila ta gyada kai, yace to seda safenku.
Yusuf na fita Hanan tace
"ke Jalila captain Ahmad ne dama, to tun wuri kice masa bakya sansa, har sunkai magana gurin daddy Yaya Yusuf baya wasa, wallahi dagaske suke, in Baba ya tambayeki kice be mikiba ba kya sonsa, kinada wanda kike so"
Jalila tace "Haka nace miki bana sonsa? Wanake dashi a yanzu danake so? To ni yayi min"
"karya kikeyi wallahi, Jalal shine kike so, ba wani aranki seshi"



Ina yinku ABDUL JALAL group irin sosai din nan fa 😍😍😍 inajin dadin Comments dinku, kuna Comments kana karamin kaimi typing duk bayan kwana biyu, kuna bari ina lalaci posting duk sati 😜😜😜

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
What's app only 07063065680.

Continue Reading

You'll Also Like

220K 11.1K 90
Being flat broke is hard. To overcome these hardships sometimes take extreme measures, such as choosing to become a manager for the worst team in Blu...
27.9K 544 33
"I thought we were friends, Azriel. I was caught off-guard but you have to know it was forgiven the day it happened." The priestess looked back up to...
59.7K 2.7K 19
Wanan labari ne akan jarabawan ubangiji, yanason wata baiwar Allah mai suna Aisha ranan bikinsu ta mutu, bayan wani lokaci mai tsawo saiya hadu damai...