Default Title - ABDUL JALAL (...

Av Ayshercool7724

56.5K 2.5K 216

Labarin wani matashi daya riga ya gurbata rayuwarsa da shaye2 da raina iyayensa, tareda wata matashiyar yarin... Mer

Abdul Jalal(2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 7
ABDUL JALAL (2020) 8
ABDUL JALAL (2020) 9
ABDUL JALAL (2020) 10
ABDUL JALAL (2020) 11
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 15
ABDUL JALAL (2020) 16
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 19
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 21
ABDUL JALAL (2020) 22
ABDUL JALAL (2020) 25
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 27
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 30
ABDUL JALAL (2020) 31
ABDUL JALAL (2020) 32
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 35
ABDUL JALAL (2020) 35
ABDUL JALAL (2020) 36
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 38
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 43
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 43
ABDUL JALAL (2020) 44
ABDUL JALAL (2020) 45
ABDUL JALAL (2020) 46
ABDUL JALAL (2020) 48
ABDUL JALAL (2020) 48
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 50
ABDUL JALAL (2020) 51
.ABDUL JALAL (2020) 53
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL part 2
part 2 55
ABDUL JALAL (2020) 56
ABDUL JALAL 57
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 59
ABDUL JALAL 60
ABDUL JALAL 61
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 63
ABDUL JALAL 64
ABDUL JALAL 65
ABDUL JALAL 66
ABDUL JALAL 67
ABDUL JALAL 68
ABDUL JALAL 69
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 72
ABDUL JALAL 73
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 74..
ABDUL JALAL 75
ABDUL JALAL 76
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 78
ABDUL JALAL 80
ABDUL JALAL 81
ABDUL JALAL 82
ABDUL JALAL 83
ABDUL JALAL 84
ABDUL JALAL 85
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 88
ABDUL JALAL (2020) 89
ABDUL JALAL 90
ABDUL JALAL 91
ABDUL JALAL 92
ABDUL JALAL 93
ABDUL JALAL 94
ABDUL JALAL 95
ABDUL JALAL 96
ABDUL JALAL 97
ABDUL JALAL 98
ABDUL JALAL 99
ABDUL JALAL 100
ABDUL JALAL 101
ABDUL JALAL 102
ABDUL JALAL 103
ABDUL JALAL 104
ABDUL JALAL 105
ABDUL JALAL 106
ABDUL JALAL 107
ABDUL JALAL 108
ABDUL JALAL 109
ABDUL JALAL 110
ABDUL JALAL 111
ABDUL JALAL 112
ABDUL JALAL 113
ABDUL JALAL 114
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL

ABDUL JALAL 79

353 19 2
Av Ayshercool7724

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 2️⃣6️⃣79

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com



_MY FIRST NOVEL_

Da sauri ta bude kofar ta shiga, yana tsaye yana kaiwa yana komowa, idonsa yazama abun tsoro saboda ja, ga jijiyoyin kansa duk sunfito sun mimmike, gashi da kyar yake sauke numfashi, se faman runtse ido yake, da Sauri Jalila takarasa tace "Jalal meya sameka? Wani abun yafarune? Ko jikinne?"

Banza yai mata ya juya mata baya, da sauri ta zagaya gabansa tana kokarin kallon fuskar sa, amma yasa hannu ya hankade ta, bige hannu tayi ajikin center ta rike gurin tana dan cije lebe tareda ya mutsa fuska alamun taji zafi, ta bugu sosai a hannun, mikewa tayi takuma komawa inda yake, a hankali ta ga ya sulale ya zauna yana motsa bakinsa alamun yanaso yai magana amma yakasa, kawai ya lumshe ido hawaye na fitaa a gefen idonsa, gaba daya yanzu Jalila tausayinsa takeji, tabbas Jalal na cikin kaddarar rayuwa amma hanyar daya dauka ba itace mafita ba. Taje gabansa ta zauna ta dan kura masa ido na wasu mintuna sannan tafara magana cikin nutsuwa da kwantar da harshe

"dukkan dan adam ba abarinsa ba tareda jarabbawa ba, Kowa da kalar tasa kaddarar, inkaji ta wani sekaga taka ba komai bace, Annabi Ibrahim alaihi salam, Annabin Allah ne, ya kira mutanensa akan bautar Allah shikadai, amma Mahaifinsa be musulinta ba, hakan besa ya saba masa a matsayinsa na mahaifinsa ba, karshe ma har wuta aka hada domin a kasheshi amma Allah ya tsallakar dashi.
Annabi Yusuf alaihi salam, Mahaifinsa na matukar Kaunarsa amma se aka Jarrabeshi akan Yan uwansa, suna masa hassada da kaunar da mahifinsu kemasa kaga matsayin sa na Annabin Allah amma har kurkuku yayi, amma daga karshe kaga daukakar daya samu.
Annabi musa alaihi salam shima yayi gwagwar maya, bayan Allah ya tsalakka dashi daga sharrin fir'auna, kalli butulcin da mutanensa sukayi masa, kowane Annabi da kalar jarrabawar da Allah yai masa. Annabawa kenan ina gamu daba kowan kowa ba, wasu na Kabari, wasu na Asibiti se an kwantar an tayar, wasu na prison basu ba kara shakar iskar yanci, wasu na gidan masu rangwamen hankali, wasu na gidan marayu ana musu kallon shegu, wasu guragu ne, suna maula a gefen hanya, wasu yaki yasa sun rabu da iyalansu da yan uwansu, duk cikin wannan ba wanda Allah ya jarabceka dashi, karka zama me butulci da Ni'imomin ubangiji no matter how worst the situation is kazama me gode masa, kanada dama, kanada lokaci kayi kokari ka gyara barnar dakayi a baya, ka yafewa mahaifiyarka inka yafe mata se Allah ya shiga cikin lamarin ka. Anyway for now don't try to kill yourself without changing your life style. Yai shiru idonsa a lumshe amma nasihar Jalila yaji tana tasirir a zuciyarsa a zuciyarsa ya shiga Fadin Astagfirullah wa atubu ilaihi, amma deep into his heart in ya tuna yadda take masa rashin mutunci se haushinta yakama shi, a fili ya bude idonsa yace

"Tashi kibani guri bana son ganinki a inda nake, kinadaga cikin mutanen dasuka kara saka zuciyata cikin garari, da tashin hankali, kinsan yadda nakeji inkika jefeni da kalmar mara tarbiyya, kin dade kina gayamin maganganu masu kona zuciya, a maimakon kalaman kwarin gwiwa, ki tashi kibani guri karki kara zuwa inda nake, nasan da Umminki tana nan nasan komai munin halina bazata taba kyamata ko tagayamin bakar magana ba, bazata taba zama cikin masu kyamata ba, ta nunamin so da kauna, kuma batun yafiya tsakanina da mahaifiyata wannan abunda ya shafeni ne, i never expect such type of behavior from you, why? Why do you hate me before, baki taba tunanin me ya jawomin nake irin wannan rayuwar ba, Never judge book by it's cover, please dismiss from here, in ina ganinki kina kara batamin rai" Idon Jalila kyar akansa bata ko kyaftawa har yayi gama yana huci,
"Naji zan tashi, Nagode sosai, karka manta da kashedin likita, kaci Abinci kasha magani, sannan ka rage shaye2"
"bazan ba uwatace ke dazaki dinga min kashedi haka? Wai ina ruwanki dani ne, meya shafeki da inyi lafiya ko kar inyi"

"A'a ba daya, in kayi inma bakayi ba kanka kayiwa ba Jalila ba, Amma kaji tsoron Allah, kakiyaye dokokinsa sannan ka kulada ibada" ta mike jiki a sanyaye ta fito waje, maganganun da Jalal ya gayamata babkaramin bata mata rai sukayi ba, dukda taji zafin maganganun da Jalal yagaya mata, amma idan ta tuna itama abubuwan data dinga masa abaya setaga bata kyauta ba.

Daddy ya kalli Jawwad yace "Jawwad Abbanka kuwa yana gari ina son ganinsa" Jawwad yace "A'a Daddy be dawo ba tukuna yana lagos amma a satin nan ze dawo Insha Allah" daddy yace "Allah yadawo da shi lafiya, Yaww Jawwad naji Jalal yacemin ka kamalla Masters dinka last Couple of months ko?" Jawwad yace "Eh Daddy Alhamdilillah na kamalla, ina jiran sakamakone, atayamu da Addu'a" daddy yai murmushi yace "Kullum cikin yi muku nake? Kuma nasan da sakamako me kyau zaka fita Insha Allah, nasan yarona akwai himma ai, dama vacancy na samu, federal zata dauki ma'aikata a farkon sabon shekara anbani vacancy na mutum daya a babban branch din NNPC na Abuja, shine nace ka turomin CV dinka ta Email dina, inkuma zaka karo karatune kuma to, semuga yadda za'ayi kaje ko England ne can wajensu Mahmud ka karasa" shiru Jawwad yayi ya sunkuyar da kai yakasa cewa uffan daddy yace "Jawwad kona bata maka raine?" Jawwad ya girgigiza kai yace
"Daddy banida bakin yi maka godiya, tun ina karami kake dawainiya dani, amma ina tunanin dan uwana, daddy Jalal shifa me za'ayi wands za'a tallafawa Rayuwarsa" daddy yai ajiyar Zuciya yace
"Jawwad bana tunanin koda Jalal yanada dan uwa ciki daya ze nuna masa kaunar da kake masa, Amma Jawwad ba yadda zanyi ina za'adauki Jalal aiki a wannan halin da yake ciki, yana shaye2 baya son mutane, ga zafin zuciya kana gani ko mahaifiyarsa baya raga mata, anyi2 yakoma makaranta yaki " Inda na godewa Allah ko bayan raina Jalal yanada kadarorin da in ya tattala ze iya rike kansa, inkuma yabarnatar shikenan" Jawwad yace

"Daddy bazanyi musu da hukuncin ka ba, amma inaso Jalal ya samu makoma shima, koya koma karatu koya samu aiki, amma idan na tafi Aiki na barshi a wannan halin senake ga kaman banyi masa halacci ba, kuma shaye2 munmasa addu'a muna fatan ze dena very soon, tunda ya rage ba kaman da ba" shiru daddy yayi yana kallon Jawwad dayake magana idonsa taf Hawaye dake nuna hakikanin gaskiyar abunda yake fada har zuciyarsa.

"Jawwad kenan Allah ya dawwamar da haske a cikin Rayuwarka, gwagwarmaya da kaunar dakake wa dana banida abun biyanka, Allah yatemakeka ya baka abunda kake nema duniya da lahira"
"Ameen daddy" daga haka ya tashi ya fita.

Oga KB yana zaune yatasa Samira da wata katuwar bulala, da alamu jibgarta yagama yi, jikinta duk a kumbure dan fuskarta a kumbure gefen idonta yana zubar da jini, Oga KB yace
"Tun tsawon wani lokaci kike tareda Jeje?"
Cikin kuka tace "Ranar muka fara haduwa da shi" kafin ta rufe baki yakuma zuba mata bulala tareda fadin
"Karya kikeyi, munafuka zaki gayamin ko sena takeki na kasheki, matsiyaciya yanzu shikenan Sunana yagama lalacewa a idon duniya, nida 'yata a gidan karuwai, dana san irinki za' a haifamin da tun a ciki sena zubar dake, Wallahi idan Nagano wanda ya shirya min wannan manakisar sena kasheshi kowaye, ki gayamin tun yaushe kuke tare?"kokuma yanzu inkasheki da poison na kashe banza shedaniya"

Cikin kuka tace "Shekararmu biyar Tare dashi" zaro ido yayi "Shekara biyar amma bansaniba, Cigaba ina jinki se akayi yaya?"
"tun ina secondary muke tareda shi, bayan haduwa ta da Saleema, nasanshi ne ta hanyarta, daga baya yake nunamin yasanka, Yaronka ne akwai aikin dayake maka, duk lokacin danazo maka da bukata baka damuwa da bukatuna, kafi son faruk dani, kana cewa bazaka kara yadda da mace ba koda yar cikinka ce, nikuma bukatuna bakamin, umma ma bayimata kake ba, balle nima ina sa rai, shine Jeje yajani a jiki shine ya koyamin bin maza, yana baani kudi masu yawa sannan ya hadani da masu kudi Shida Saleema, Sau biyar ina zubar da ciki biyu duk nasane"

Wata irin zuface ta shiga tsatstsafowa Alhaji Kabiru mikewa yayi ya shake Samira yana fadin
"Samira anya kuwa nine Ubanki, kodayake a rina barewa bata gudu danta yai rarrrafe uwarkima karuwanci tayi ta tuba na Aureta, watakila bayan na Auretanma bata tuba ba"

Mahaifiyar Samira ta fito a fusace tace
"Sakarmin 'yata wallahi bazaka kasheta ba, tun dazu inamaka kawaici shiru kawai nake, tunda abun naka yazoda cin fuska bari in tunamaka, kana tunanin hakkin uwarka ze kyaleka ne,? kokuma shi yaron dakasa aka lalata ba dan wasu bane? Yaronne yai maka laifi? Kokuwa uban me ya kaika gidan karuwai? Duk nasan abunda ka keyi kyaleka kawai nakeyi dan haka sakarmin yarinya ni Addu'a nake Allah ya shirya yaran musulmi amma wannan bakar zuciyarta ka me cike da sharri dole kaima kaga sharri akan yaranka".

A fusace yayo kan mahaifiyar Samira, amma Samira ta rike rigarsa cikin ihu da kuka take cewa
"Wallahi karka sake ka tabamin uwa, nidin dai ko kasheni kayi nasam baka da asara, ai a ranar da aka kamamu a gabaana zizo yace kaima ana kaimaka karuwai gidan hutawarka, tunda na taso katsaneni saboda kawai ni macece ka fifita soyayyar danka namiji akaina, gaka da kudi amma baka moramin komai danme yasa bazan nemawa kaina mafita ba"

jin hayaniya yasa tuni mutane suka fara shigowa dan ganin meyake faruwa, Alhaji Kabiru yasa hannu yai wurgi da Samira, take ta fafi bata ko motsi, nan da nan mutane sukayi kanta amma ana dagata sega Jina nata zuba daga jikinta.

Shikam Alhaji Kabiru motarsa ya dauka ya fice daga gidan be zame ko ina ba se gidan Jeje, Yana zuwa Jeje baya nan, dan haka ya tafi Club din dayasan lallai ze same shi a can Jeje yana nan, yanata shaye2 shida wasu mata, tareda wasu abokansu.

A fusace ya daka musu tsawa yace su basu guri, daya ta kalleshi cike da maye tace "Wollahi ba inda zamuje, ji mutum kazo kasamemu sannan kace mufita
"Jeje yace "Am sorry Guys don't mind him" Jeje ya dawo da dubansa kan Alhaji Kabiru yace
"I thinks you said it's over between me and you ba, bayan tsawon lokaci dana dauka inamaka aiki, inamaka bauta dan ka kamani da 'yarka,' yan sanda sunkamamu, shine kacimin mutunci kamanta halaccin danayi maka"

"Shut up!!!" yayi wa Jeje tsawa
"Duk wahalar danayi maka A rayuwa, tun kana karamin dan isaka na daukeka naimaka gata, na dinga yimaka wahala tsawon shekaru, baka cikamin burina na ganin ankai Jalal kurku a kaskance uwarsa da ubansa na kuka ba, memakon ka maida hankali akan aikin dana saka, sema komawa da kai kana cin amanata, yar cikina kake lalata da ita, kakoya mata bin maza, ga shaye2 ta tabattarmin da sau biyar tana zubar da ciki biyu daga ciki kuma nakane, Ka saurari abunda ze biyo baya, hukuma ce zata rabani da kai"
Jeje yace "Kafin ka kaini gaban hukuma yakamata ka amsawa kanka wannan tambayoyin? Kai yara mata nawa ka lalata?
Ko agaban Allah wace hujja zaka bayar na bada kwangilar lalata Rayuwar ABDUL JALAL da sunan daukar fansa?
Uwa uba karka manta da babbar haramtacciyar harkallar da mukeyi na saida makamai da miyagun kwayoyi"
cak Oga KB ya tsaya yayinda Jeje ya kyalkyale da dariya yace
"Ramin mugunta kenan inzaka gina, gina shi gajere dan kila kai zaka fada"
Wani mugun bakin ciki da bacin raine yakama Oga KB ya juya ya shako wuyan Jeje yafara bugashi akan tebur, dayake a buge yake sam jikinsa babu kwari, nan take matasan dake gurin su taso sukayi kan Oga KB, dan har jini yafara fita daga hancin Jeje, Oga KB na juyawa ya rarumo wata kwalbar giya ya bugawa Jeje a goshi nan take Jeje yafara zubar da jini hakan be isheshi ba seda yakuma soka masa kwalbar nan a kafada, Jini ya dinga fita a jikinsa nan take jiri ya kwashe Jeje ya fadi kasa sumamme, da kyar security din gurin suka rike Oga KB suka tafi dashi suka kuma mikawa 'yan sanda shi. Sannan aka dauki Jeje zuwa Asibiti rai a hannun Allah.

Ita kuwa Samira da aka kaita Asibiti ta galabaita ashe wani cikinne a jikinta bata saniba, da kyar aka ceto ranta sedai an tabattar da mahifarta ta lalace bazata kara daukar ciki ba har abada.

Jawwad yakoma gida ya tarar da Jalal a part dinsa, a zaune a akan kujera, Jawwad yaje kusada shi ya zauna, ya dinga masa nasiha tareda rarrashi akan abubuwan dayakewa mahaifiyarsa, Jalal yai shiru yaki kula Jawwad har yai surutansa yagama dan babu alamar Jalal ya dau Nasihar Jawwad, seda ya bari Jawwad yagama tsaf sannan yace
"inka gama bani aron key din motarka"
"ina zakaje?"
"In tuhumata zakayi bar abunka"
"A'a ni na isa, gashi amma kabi a hankali kasan bakada lafiya kayi driving a hankali" Jalal bece komai ba yasa hannu ya karbi key yafita.

Jawwad ya nemi guri ya kwanta ya dan huta yana tunanin karamcin da daddy yake nuna masa. Jawwad yasamu yayi bacci, se bayan la'asar ya farka, yaje yai wanka yai salla yana kokarin neman Abunda zeci ya tuna dakin Jalal yana nan kaca2 da kwalaben da ya fasa yasan inba sa'a akai an gyara ba Jalal baze gyaraba ko dakin ze shekara ahaka, kuma ze iya zuwa yayi shaye shayensa yace ze shiga ya kwanta ga kwalabe da ya farfasa a zube a dakin, Jawwad ya mike ya fita, yana fitowa kafin ya kaiga bakin gate yaji muryar Naja ta kashe murya tana masa magana

"Yayana dan Allah inbazaka damuba sonake ka rakani unguwa" Jawwad ya kakalo murmushin dole yace"

"Eyya am very sorry, kinga aiki zanyi ne yanzu na gaggawa dan Allah kiyi hakuri"
yana gamawa bejira mezatace ba ya fice daga gidan, tsayawa tayi turus tarasa me zatace. Haka ta juya takoma cikin gida tana cizon yatsa, tana komawa daki ta tararda Jalila tana gyara gashin ta agaban mudubi, ta dinga tsaki tana aikin banza, ita dai Jalila bata kulata ba, seda tagama tsaf ta dauki mayafi ta daure kanta ta dau wayarta ta fice, tana bukatar yin waya domin jin inda harkalarta ta kwana.

Jawwad yana zuwa yafara tattarre Kwalaben dakin yana sakasu a dustbin yana bawa megadi yana fita dashi, Jawwad ya duba bega tsintsiya ba dan haka yakoma gida don ya dakko, yana zuwa ya hangota tana waya, kallo daya tayi masa tai murmushi ta sauke wayar tace "Ya dai naga kayi gumi haka? Meyafaru?"
Murmushi yayi yace
"Wallahi Jalal nake gyarawa daki, yayi fata2 da komai, kuma in ban gyara masa ba a haka ze barshi, kar inje ya bugu yace ze shiga dakin ya kwanta a haka" Jalila tai murmushi tace
"Allah ya sadaka da dukkanin wani alkhairi na duniya da lahira hakika ka cancanci yabo, Yaya Aliyu Jawwad sha gwagwarmaya, amma meyasa sekai zaka gyara masa?"

Jawwad yace

"Kinsan halin dan uwan nawa, bakowa yake so yashigar masa daki ba, baya son sa ido"

"Hakane muje in tayaka"
"Anya kar in takura miki fa"
"Bawani takura gyaran gida aina matane" ta rakashi suka dakko tsintsiya suka fito akan idon Naja suka fita tare aikuwa tasaki Ashar, Da sauri Nana ta kalleta "Lafiya kike mana Ashar haka sekace ba musulma ba"
"Dalla rabu dani yanzu nacewa Jawwad ya rakani unguwa yace bazashi ba yanada abunyi, amma kalli sunfi ta tare da wannan jakar yarinyar, zasu gane kurensu bari Maaman ta dawo" Nana ta tabe baki tace
"Wallahi Naja duk inda kikaje sekinja masifa, muna zamanmu lafiya amma kinzo zaki tayar mana da hankali Aikin banza kawai" Nana ta mike ta fice tabar mata dakin.

Jalila ta dinga taya Jawwad suna kwashe kayan daya fasa suna fita dashi a hankali dakin yafara hankali kula tayi kaman Jawwad yagaji sosai tace
"Yayan Baby what's wrong?" yace "Baby yunwa nakeji sosai, ga Jalal yafice ban san inda ya tafiba koya ci Abinci oho"
"Allah sarki jekaci kadawo ina jiranka, Abincin yana nan a kitchen"
"God bless you my dear, yanzu zan dawo Insha Allah".

Sosai Jalila tacigaba da aikin dakin, bedroom din zuwa palour ta gyara komai, taje tana goge kan fridge kawai ta bude, kwalabene manya da kanana, tanagani tasan giyace ga kwalayen sigari nan duk ya shiryasu a ciki sekuma kwalayen madara da Apple a ciki amma kwalaban giya sunfi yawa, fito dasu ta dingayi daya bayan daya ta taresu agabanta ta girgigiza kai, ta tattaresu guri daya tadinga bude kwalbar tana tsiyaye giyar a cikin dustbin, ta zazzage tabar nan a cikin shara, tacewa megadi yafita da ita ya ƙona. Ta koma dakin ta juya baya tanata mopping taji an rikota ta baya..

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
What's app only 07063065680.

Fortsett å les

You'll Also Like

282K 8.1K 136
"𝑻𝒉𝒆𝒓𝒆'𝒔 𝒓𝒆𝒂𝒍𝒍𝒚 𝒏𝒐 𝒘𝒂𝒚 𝒐𝒇 𝒘𝒊𝒏𝒏𝒊𝒏𝒈 𝒊𝒇 𝒊𝒏 𝒕𝒉𝒆𝒊𝒓 𝒆𝒚𝒆𝒔 𝒚𝒐𝒖'𝒍𝒍 𝒂𝒍𝒘𝒂𝒚𝒔 𝒃𝒆 𝒂 𝒅𝒖𝒎𝒃 𝒃𝒍𝒐𝒏𝒅𝒆."
251K 20.3K 61
"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin w...
156K 10K 40
WANNAN LABARI NE DA WASU BANGARE YA FARU A GASKE. BAN CANJA SHEKARUN YARINYAR BA KO ALAKA BA,AMMA NA CANJA SUNA, SANNAN BABU SUNAN GARI DA KUMA ANGU...
59.6K 2.7K 19
Wanan labari ne akan jarabawan ubangiji, yanason wata baiwar Allah mai suna Aisha ranan bikinsu ta mutu, bayan wani lokaci mai tsawo saiya hadu damai...