Default Title - ABDUL JALAL (...

By Ayshercool7724

56.1K 2.5K 216

Labarin wani matashi daya riga ya gurbata rayuwarsa da shaye2 da raina iyayensa, tareda wata matashiyar yarin... More

Abdul Jalal(2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 7
ABDUL JALAL (2020) 8
ABDUL JALAL (2020) 9
ABDUL JALAL (2020) 10
ABDUL JALAL (2020) 11
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 15
ABDUL JALAL (2020) 16
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 19
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 21
ABDUL JALAL (2020) 22
ABDUL JALAL (2020) 25
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 27
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 30
ABDUL JALAL (2020) 31
ABDUL JALAL (2020) 32
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 35
ABDUL JALAL (2020) 35
ABDUL JALAL (2020) 36
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 38
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 43
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 43
ABDUL JALAL (2020) 44
ABDUL JALAL (2020) 45
ABDUL JALAL (2020) 46
ABDUL JALAL (2020) 48
ABDUL JALAL (2020) 48
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL (2020) 50
ABDUL JALAL (2020) 51
.ABDUL JALAL (2020) 53
ABDUL JALAL (2020)
ABDUL JALAL part 2
part 2 55
ABDUL JALAL (2020) 56
ABDUL JALAL 57
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 59
ABDUL JALAL 60
ABDUL JALAL 61
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 63
ABDUL JALAL 64
ABDUL JALAL 65
ABDUL JALAL 66
ABDUL JALAL 67
ABDUL JALAL 68
ABDUL JALAL 69
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 72
ABDUL JALAL 73
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 74..
ABDUL JALAL 75
ABDUL JALAL 76
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 79
ABDUL JALAL 80
ABDUL JALAL 81
ABDUL JALAL 82
ABDUL JALAL 83
ABDUL JALAL 84
ABDUL JALAL 85
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL 88
ABDUL JALAL (2020) 89
ABDUL JALAL 90
ABDUL JALAL 91
ABDUL JALAL 92
ABDUL JALAL 93
ABDUL JALAL 94
ABDUL JALAL 95
ABDUL JALAL 96
ABDUL JALAL 97
ABDUL JALAL 98
ABDUL JALAL 99
ABDUL JALAL 100
ABDUL JALAL 101
ABDUL JALAL 102
ABDUL JALAL 103
ABDUL JALAL 104
ABDUL JALAL 105
ABDUL JALAL 106
ABDUL JALAL 107
ABDUL JALAL 108
ABDUL JALAL 109
ABDUL JALAL 110
ABDUL JALAL 111
ABDUL JALAL 112
ABDUL JALAL 113
ABDUL JALAL 114
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL
ABDUL JALAL

ABDUL JALAL 78

355 21 3
By Ayshercool7724

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 2️⃣5️⃣78

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ www.humaira17@gmail.com



_MY FIRST NOVEL_

Jalal Ya dau lokaci yana kallon ta.
cikin rawar murya Jalila tace

"Sannu ya jiki?"
shiru yayi bece komai ba ya lumshe idonsa.
"Ko inkira maka Jawwad?" still shiru yayi bece mata komaiba tamarasa mezatayi, idonsa a lumshe taga hawaye nabin gefen idon Jalal, hankalinta yakara tashi
"Inkira maka likitane?" takarasa maganar tana hawaye, bude idonsa yayi ya juyo yana kallonta a hankali yace
"Kukan mekikeyi? Ko Na kuma yi miki wani laifinne? Nasan bazakiyi kuka dan halin danake ciki ba, zakifiso in mutu saboda yayanki ya huta ba?"

Girgigiza masa kai Jalila ta shigayi amma takasa magana
Ya hade rai yace "kidenamin kuka, nagaya miki kin cikamin kunne"

Cikin muryar kuka tace "Yi hakuri na dena" tasa hannu ta share hawayenta.

Jawwad yashigo da likita suna zuwa kan Jalal ya bude ido, Jawwad ya zauna kusada shi yace "Sannu ya jikin naka?"
"Alhamdilillah naji sauki azo a sallameni"
murmushi likitan yayi sannan yace

"kai Jalal da wuri haka, bazamu sallameka yau ba, se mun tabattar dakabi dokokin dazamu saka maka, bamaso se mun Sallameka akuma dawo da kai Rai a hannun Allah"

Jawwad yace "rabu dashi doctor yi masa abunda yakamata, baza'a sallameshi ba seya warke gaba daya"

Jalal ya tashi zaune, Likita yakara duddubashi, sannan yayi rubuce2 a file din Jalal, ya rubuta wata takadda yace
"Ga wannan Jawwad bamu dasu a pharmacy sekaje cikin sabon gari zaka samoshi"
Sannan likitan ya kalli Jalal yace "Man yakamata ka cire abunda yake ranka, karka kashe kanka da kuruciyarka kana matashinka, kana da kudi kana cikin Ni"'imar ubangiji meze daga maka hankali haka? "

kallonsa Jalal yai ya dauke kai likitan yacigaba da cewa

"Jininka ya hau sosai, dole kadena damuwa sannan u must reduce the amount of cigarette and shisha you take every day (PEOPLE WHO SMOKE ARE ABLE TO DIE YOUNG!!!) so you should be careful, akwai sinadarin dayake saka hawan jini a cikin taba, shanta yana kawo lung cancer ko tuberculosis, and you should reduce Alcohol intake, ka rage shan giya shima, tana saka cututtuka da dama, kaman Ciwon Hanta, ciwon koda, tana kara asassa ciwon sugar akwai kuma nauo'in ciwon ido da take sakawa, dan haka a hankali yakamata ka rage, sannan kadinga cin Abinci kaga Ulcer yana nema yazeme maka chronic "
shiru Jalal yayi ya sunkuyar da kai, Jawwad yace
"Shikenan doctor za'a kiyaye Insha Allah"
"Yawwa masha Allah, Allah yakara sauki" doctor ya juya ya fita, Jawwad ya zagayo ya zauna kusada Jalal yace

"Kaji abunda doctor yace ko? Please and please ka kiyaye dokokin da aka samaka kaji Dan uwa" Jalal dai bece komai ba, ya sunkuyar da kansa, Jawwad ya juya ya kalli Jalila yace

"Baby miko kwandon Abincin nan a hada masa yaci se inje siyo masa maganin"
Ta dakko kwandon, ta zuba kunun gyada cikin wani katon kofi ta zuba dankali ta mikawa Jawwad, Jawwad ya zare ido yace "Kai Baby yazeyi da wannan kunun yayi yawa ai, bakiga bashida lafiya ba, aibaze iya shanye wannan ba"
Jalila ta ɗan tura baki tace "Au haba, ka tuna lokacin dana kwanta a Asibiti cikin katon kofin nan yazare min ido sena shanye, shima ka zare masa ido ya shanye" takarasa maganar tana dan tura baki.
Bakinta Jalal ya tsaya yana kallo shikuwa Dariya Jawwad yai yace "itaku kedashi, kema seki zare masa ido ya shanye, bari inje in siyo maganin" Jawwad ya mike ya fita.

Jawwad na fita Jalal yai kokarin komawa ya kwanta beci Abincin ba da sauri Jalila tace
"Ai bakaci Abincin ba" ya kalleta "Bazanci ba" yakuma kokarin kwanciya Abincin ta dauka ta dora a inda ze kwanta tace "wai meyasa kafiye taurin kaine? Cewa fa akayi kaci Abinci"
A fusace yace "Ke har na kaiki taurin kaine? Waima ina ruwanki danine? Dan giya, mara tarbiyya, zan lalata miki dan uwa, me kike nema a gurina, dauke Abincin ki bazan ciba, kintaba gayamin idan na mutu bakida Asara to meye naki na damuwa da banci Abinci ba?" yasa hannu ya dauke Abincin ya dora akan drower na kusa da gadon sannan yace
"Dama a duniya daga daddy se Jawwad ne suke sona se yan uwan daddy, nan duniya idan na mutu ba wanda yakeda Asara, sesu"

kura masa ido tayi yana mara lafiya da masifa, yace "Meye kuma kike kwalalamin idanuwa haka, kidena kallona" yai kwanciyar sa.

Kawai Jalila ta mike ta fice daga dakin, Ajiyar zuciya Jalal yayi dayaga ta fita ya dakko Abincin data zuba ya ci ya aje sauran.

Jalila na fita tasamu guri ta zauna a waje ta dakko wayarta tafara chatting tana daga kai ta hango Ilham da mahaifiyarta a harabar Asibitin kallo daya tayiwa Saudat tagane itace mahaifiyar Ilham.
da sauri Jalila ta tashi ta koma dakin Jalal, tana zuwa taga yaci Abincin yana kashingide ya lumshe ido, yana jin motsinta ya bude ido.
"Ke meya dawo dake, ko dama bakida zuciya?" cikin tsiwa tace
"dama ina naga zuciya, tunda kaima bakada ita"
Dan zare ido yayi, ashe halin nata yana nan
Ta fara hada kan kwanuka, Ilham ce da Mamanta suka shigo da sallama yanajin muryarsu yai Sauri ya rufe idonsa. Kai kace bacci yake, Tunda Ilham taga Jalila a gurin Jalal ta hade rai kaman taga kashi
Jalila ta maze tace "Sannunku da zuwa" yawwa maman Ilham ta amsamata, tabasu guri suka zauna Ilham se harar Jalila take, ita kam Jalila data kalli Ilham seta mata murmushi Maman Ilham tace "Yame jiki?"
"da sauki Mama"
"naga alamar kaman yana bacci ne ko?"
Jalila ta waiga ta kalleshi yawani rufe ido kaman gaske amma idonsa biyu, se Jalila ta kudurce wani abu a ranta dan haka Jalila tace "
eh likita yamasa Allurai yasamu bacci, likita yace baze farka ba se bayan Awa biyar, yanzu besan me ake ba"
Maman Ilham ta kalli Jalila tace
" Sedai bangane wannan ba, bakowa a gurinsa seke? ko itama a dangin baban nasa take?"
Ilham tai farat tace "Inafa," yar shishshigi yar wahala dai, me hana ruwa gudu, me cusa kanta inda Allah be kaita ba" Jalila tace
"haba Ilham, wani ma se yazata banida kirki, menamiki haka ina laifin kice, Sauro me hana giwa bacci, Raina kama kaga Gayya" Jalila ta karasa maganar tana murmushi tace

"Mama bari in saka wayata a caji, in karbo muku ruwa a waje" Jalila ta mike ta dau wayarta ta dan daddana sannan tasaka ta a caji ta fita.

Ba'a wani dade ba, Jalila ta turo kofa ta shigo da ruwan roba ta ajiye musu ko sha basuyi ba suka tashi sukace tafiya zasuyi.

Tai musu sallama suka mata banza Ilham nata gaya mata bakaken maganganu bata damu ba suna fita taje ta dauki wayarta ta bude, maganganun dasukayi tsaf tayi recording dinsa tai Saving tajuya ta hada kan kwanukan da Jalal yaci Abinci, bude idonsa yayi yana kallon ta tana dagowa suka hada ido
"Akwai matsala ne?" Jalila ta tambayeshi
"Wani Apple kika hanani ci kika musanya ranar da mukayi baƙi?" tambayar tazo mata a bazata, ta dan tabe baki sannan tace
"Apple kuma ni ban san zancen ba"
"Karya kikeyi" Hade rai tayi sosai
"Eh kasan na saba" tacigaba da abunda take, ko ina yasan wannan maganar oho masa.
ta mike tsaye taji ya janyo ta da karfi kan gadon, take jikinta ya hau rawa ta tsorata sosai ta ware ido tana kallon sa
"Ina tambayar ki kina rainamin hankali wani Apple kika hanani ci, kuma meyasa?"
"ni nace maka ban san zancen ba, ka tambayi wanda suka gayamaka mana, ni kacikani" kara karfin rikon yayi taji kaman ze karya ta, sannan yace

"ke bana son karya, for the last time ki gayamin" kawai ta fashe da kuka, mamakine yakama shi, in wani ya shigo se a zata wani abun yayi mata, dan haka a hankali ya sake ta ta mike da sauri ta koma waje, tana fita ta dakko wayarta kunna maganganun Ilham da mamanta.
Kawai taji maganar Ilham tana cewa
"Umma wannan itace munafukar da nake gaya miki duk lokacin danayi wani yunkuri zanyi wani aiki akansa itake lalatawa, na dade da gane take takenta sonshi take, amma taki yadda tana rainamin hankali, tasamun Ido ta hanani sakewa, duk lokacin danayi Yunkurin wani abu idonta na kaina, seta wargaza gashi ta hadani dawata tsinanniyar karuwa wai budurwar Jalal ce, hatsabibancin yarinyar nan ya wuce tunaninki, harda wani alwashin indai tana Raye seta rusa shirina akan Jalal" mamanta tace
"Ke sokuwar inace? Kika kasa gayamin tuntuni mu dau mataki akan shegiya"
"Umma har gurin Malam na kaita amma yace baze iya komai akanta ba, dakike ganinta ita ta musanya Apple din dana sawa maganin ranar da 'yan Maiduguri suka zo, makira tsinanniya" umma ta girgigiza kai tace
"Tab aikuwa da sake, dole muyi wani abu karta bata mana aikinmu, amma Khadija kuwa tazo taga halin dayake ciki?" Ilham tace
"Ai ingayamiki baya son ganin ta, kinga abunda ya dinga yi kuwa sekace ya haukace, dakinsa na nan kaman kantin mahaukaciya ya fasa komai a dakin, sangartacce ubansa na dawowa za'a canza masa komai" suka cigaba da maganganun su a zatonsu duk Jalal bacci yake besan mesuke ba, ita kuwa Jalila tana sane tayi haka.

Shiru Jalila tayi tana tunani "Kenan Jalal yaji duk maganganun da sukayi shine yake tambayata? Kafin kuga bayana zanga naku"

Jawwad ta hango ya taho da leda a hannunsa, yana zuwa inda take yace "Am sorry na tafi nabarki ko? Na dade bansamu maganin bane, bari inzo in maida kw gida nasan kin gaji"
"To Yaya sannu da zuwa"
"Yawwa babyn Yaya" yai mata murmushi ya wuce, yakai minti goma sha biyar sannan ya fito ya dauki Jalila suka tafi gida.

Suna zuwa gida gaban Jawwad yafara faduwa, sakamakon tarar da Maama a harabar gidan da sukayi a tsaye da alamu a zuciye take, Jalila ta fito daga mota, Maama ta dinga jefamata wani irin mugun kallo, Jalila ta basar tace "Maama sannu da gida" tafada tana kokarin wucewa cikin gida
"Dakata algunguma" ta dakatar da Jalila, Jalila ta tsaya ta sunkuyar da kai, Jawwad yafito ya rufe mota yakaraso gurin Maama yace "Maama, meyafaru ne?"
"Ubanka ne yafaru, daga gidan ubanwa kuke? Da kuka fita tun farar safiya se yanzu kuke dawowa?" Jawwad ya dan girgigiza kai yace "Kiyi Hakuri, ta rakani gurin Jalal ne, muna Asibiti tun dazu"
"Yimin shiru makaryaci banza da na wofi, kai ko kunya bakaji ka dingamin karya, Asibitinne se yanzu zaku dawo, tafara janka gantali ko, wallahi ka biye mata kafara aikata wani abu dayasaba da al'adunmu se ranka yabaci, tun yaushe Nake maka magana akan Naja, fafur kaki kaje ko inda take, tunda abun naka hakane Naja ta dawo gidan nan, kuma koba kaso seka Aure ta" ta juya ta kalli Jalila tace
"Kekuma ko mayyace sekin kyalemin dana, akan me ke baki da zuciya ne? Wallahi kifita daga idona, shegiya mayya" ba Jalila ba hatta Jawwad seda ya dago Ido suka kalli Maama a tare, Jalila ta juya ta shige cikin gida ta barsu a gurin, tana shiga palour ta fara kicibis da yaya mairo da Naja, a ranta tace

"Ashe wannan ibilishiyar matar ce tazo shiyasa yau akemun saukalen Rashin mutunci, tun daga harabar gida ai shikenan"
Aibata gama zancen zucin ba ta tsinto muryar Yaya mairo tana fadin
"Ga shedaniyar nan makira, wallahi kozaki mutu gidan nan ma se ya gagareki zama, kuma seya Auri Naja, dan bazamu Aura masa Arniya ba, wadda uwatta ta gudu tazabi barbadanci ta battaba, Nutsatsiya zamu aura masa yar musulmi"

Jalila ta tsaya ta waiga taga daga ita se su a palourn Maama tana waje tana cigaba da saukewa Jawwad kwandon jaraba, Jalila tace

"To ayi mugani mana, karewar nutsatsiya masallaci Zaku Aura masa, sannan kika kuma zagarmin uwa wallahi sena kira taki uwar na zaga dan uwa bata fi Uwa ba" Naja ta mike a fusace tace
"Ke dan uwarki uwatawa zaki zaga?"
Jalila tace
"badai uwata ba, wannan tsohuwar banzar kika zaga, kinbiyata ladar haihuwarki datayi, kuma Na zageta ita wacece? Ko fin tawa uwar tayi? Kuma wallahi takuma zagarmin uwa sena fasa mata kai da wannan flask din" Jalila ta nuna tea flask din da takaiwa Jalal Abinci a ciki, hangame baki Yaya mairo tayi Jalila tace

"Yanzu nasan ciwon kaina, ina zubarda hawayena ne a inda yakamata, nadena asararsu akan maganganun ku, iyakaci duk tsufan mace ta zagarmin uwa sena rama wallahi, Sannan ke Naja naji ance kindawo gidan nan da zama, kinyi kwantai ana cusa masa ragowa yana baya so amma saboda ansan baki da mamora, se cusaki akeyi to kinkawo kanki, bacin ran da uwarki ta dinga kunsamin tsawon shekaru sena ramasu akanki wallahi, kuma kafin inbar gidan nan sena tabattar da kin barshi tukuna"

Jalila ta juya tai wucewarta daki yayinda Naja da yaya mairo suka rasa abun cewa, Naja tai karfin halin cewa

"Lallai yarinyar nan rashin mutuncin ta yakara yawa, amma karki damu, ni zan saita mata zama namiki alkawarin setabar gidan nan da kafarta, kuma sena Auri Jawwad, kiyi hakuri zan ramamiki"

Naja na rufe bakinta, sega Maama sun shigo ta sako Jawwad a gaba tanata masa masifa shikam ya sunkuyar da kansa kasa har suka shigo cikin palourn
Nan Maama da yayarta, Yaya mairo suka saka Jawwad agaba da fada, shikam yayi shiru yakasa cewa komai babban abunda yake kona masa rai be wuce yadda suke cin mutuncin Ummi ba, matar da basuda tabaccin tana raye ko bata raye, seda sukayi suka gama sannan ya mike ya bar palourn, Yaya mairo tacigaba da zuga Maama tana kara cusa mata tsanar Jalila a ranta.

Yaya mairo ta tafi tabar Naja a gidan, koda Nana ta dawo gida ta tarar da Naja a gidan ba karamin haushi taji ba, dan sam Allah be hada jininta dasu ba.
Jalila takira Hanan a waya, tagayamata abunda ke faruwa, Naja ta dawo gidan da zama ita ake so Jawwad ya aure.

A fusace Hanan tace "Kan bala'i, wallahi ba'a isa ba"
cikin mamaki Jalila tace "Kamar yaya kenan?"
"kamar yadda nagaya miki, ai wannan fadan banaki bane Jalila nawane, ai muna nan zuwa Kanon very soon, ina baze yuwu ba, ai gara in barmiki Jawwad da ina gani ya Auri wannan yarinyar, gentle man like Jawwad, be dace da Auran ballagaza kaman wannan yarinyar ba dukda kasancewar ta yar uwassa"

Hanan ta dinga masifa karshema ta kashe wayarta. Mamaki duk yakama Jalila dama dagaske Har yanzu Hanan bata hakura da Jawwad ba? Haka Jalila taita tunani.

Washegari aka sallamo Jalal daga Asibiti ba laifi jikinsa yaji sauki sedai rashin kwarin jiki, Jawwad ne ya dawo dashi daga Asibiti, Dakin Jalal sam yayi kaca2 da kwalabe da abubuwa dan haka suka wuce dakin Jawwad.

Jalal ya kula da yanayin Jawwad kaman ransa a bace yake, dukda Jalal dinma nasa ran ba dadi amma yace
"Jawwad meyake damunka ne? Saura kacemin bakomai dan fuskarka ta nuna"
Jawwad yace "Jalal duk na rasa me ya kamata inyi" nan ya kwashe komai ya gayawa Jalal"
Jalal yace "Bazaka Auri wata Naja ba"
"Wallahi Jalal nima bana sonta amma Maama ta dage na rasa ya zanyi"
"Karka damu zamu samu mafita amma wannan yarinyar ba matar Aure bace, dan sam baku dace ba" Jalal yaita kokarin kwantar wa Jawwad hankali yayin da shikuma gefe guda tasa damuwar nakuma sassakar zuciyarsa, musamman idan ya tuna maganganun dayaji Ilham tanayi da mamanta akansa.

A ranar da yamma daddynsa ya dawo, bagan magariba Jawwad yaiwa Jalal rakiya zuwa gidansu, har palourn daddy sedai daddy beji dadin yadda ya tarar Jalal yai rashin lafiya be Sani ba, Jawwad yace

"Ai yaji sauki daddy ya warke, bekamata kana can mu tayar maka da hankali ba gashi yaji sauki" daddy yace
"Hakane ya jikin naka?"
Jalal yai ajiyar zuciya sannan yace "Naji sauki" Mummy ce ta shigo palourn da cup din tea a hannunta, tazo ta samu guri kusada daddy ta zauna sannan tace
"Ya jikin naka?"
Banza yayi yaki kulata, sema dauke kai da yayi, Jawwad yace
"Jalal Mummy namaka magana fa" wani uban tsaki yakuma yi ya dauke kai, daddy yace
"Haba Son Mum cefa, at least kagaya mata how you feel zataji dadi" mikewa Jalal yayi ya nufi hanyar fita Jawwad yabishi yana cewa "wai Jalal wani irin mutum ne kai? Baka kyauta ba meyasa kake hakane, mahaifiyarka cefa?" tsayawa yayi ya kalli Jawwad yace
"Ta haifeni ne kawai, amma bata amsa sunan uwata ba, ka gayamin ya dace abunda taiwa dangin mahaifina? shikenan ni haka zan kasance bawanda ze dinga rabata, ba soyayyar uwa, ba dangi ba abokai, haka zan kare Rayuwata, kai kadai ne ka iya jure halin mahaifiyata kae taredani har zuwa wannan lokaci, Jawwad yaushe zan samu sassauci akan kaddarorin Rayuwata why me? Mahaifiyata amma kullum itake kokarin rusani itafa ta haifeni, bata tausayamin kodan irin Rayuwar dana shiga saboda ita? Kowa ya gujeni nazama abun kyama, Amma shikenan nasan matakin dazan dauka"
yana zuwa nan a zancensa kawai ya juya ya fice da Sauri, Jawwad ya mike ze bishi daddy yace "
Son kyaleshi, inka bishi maybe ya sauke maka yabata maka Rai karkaje inda yake a yanzu, zoka zauna nan ina so zamuyi magana da kai, Jawwad ya dawo ya zauna, Daddy ya kalli Mummy yace" Khadija dan kina mahaifiyar Jalal, dole kicire girman kai ki nemi Afuwarsa dan tabbas kin cutar dashi.
Mummy tace "Nifa ina mamakin cewa dakuke nice sila, wace uwace zata sa hannu danta ya lalace, menayi dayazama nice silar lalacewar sa, Jalal ne ya kamata yanemi yafiyata batamin randa yakeyi"
Ta mike a fusace tabar palourn, Jalal kam yana fita yacikaro da Ilham a harabar gidan yabita da wani mugun kallo na tsantsar tsana, seda tasha jinin jikinta, yasa kai ya fice a fusace.

Jalila na kan step din palour taga Jalal ya shigo gidan ya nufi part din Jawwad, se hada hanya yake kaman baya ganin gabansa sosai, daga inda take ta hango kaman da hawaye a idonsa, da Sauri ya ƙarasa part din Jawwad ya tura kofa ya shiga aiko itama da sauri ta sakko tabi bayansa.
Amma tana zuwa kofar dakin seta tsaya tafara tunani "to idan naje mezan ce masa? Inkuma ya makeni fa?" juyowa tayi zata koma, kawai taji kaman Jalal yana fidda numfashi da Sauri.

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
What's app only 07063065680.

Continue Reading

You'll Also Like

250K 20.3K 61
"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin w...
35.4K 847 90
Continuation of Modesto story who happens to intercourse with friends,mature,classmates,strangers and even family...
214K 10.8K 90
Being flat broke is hard. To overcome these hardships sometimes take extreme measures, such as choosing to become a manager for the worst team in Blu...
1.2M 37.1K 100
Matar shi ce ta farko bata san haihuwa, idan ta samu ciki sai ta zubar, as ending yake yin auren sirri da mai aikin gidan