P108

93 7 6
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...108*

               ........Da kukan nata ya ishe sa ne...a zuciye yaja wani uban birki tsakiyan titi..." Rayyan lafia?...Ya akayi?"
Anty Madina ta jefa masa tambaya cike da mamaki tana mai waigen baya.

Bai bi takan maganar ta ba..sai ma duban Zaitoon da yayi.
" I swear idan na sake ganin digon hawayen ki bazaki 'karasa shiga cikin garin nan ba zamu koma...haba da Allah"!
ya 'karashe maganar a zafafe.

Sai a lokacin ne ma duk suka ankara da cewan tana kuka.
Anty Madina da 'yar uwan Ammi ne suka fara yi mata nasiha cikin natsuwa, ita Anty Madeena dayake duk tasan meke faruwa, ita kuma 'yar uwan Ammi tunanin ta ko kukan rabuwa da Marwa ne.
Nasiha duk suka hadu sukai mata bayan yaja motar a fizge, shiru kawai tayi ta sunkuyar da kanta.

Wani tangamenen gida aka kai Marwa da fa'dar irin tsari da girman sa ma 6ata lokaci ne.
Amma su Anty da kansu sun yaba sosai tun ma ranar da suka kawo kaya.
Sun kuma samu tarba mai kyau daga Hajiyar Adam, domin gidan ta aka fara kai Marwa kafin gidan mijinta.
Kuka kawai Hajia Talatu ta sanya, lokuta da dama idan ta tuna abinda ta yiwa Zaitoon ko ita ka'dai ce cikin 'daki sai taji kunya ta kamata.
Sai gashi ashe ma Shaheed din Zaitoon tsoka da jini suke ta yadda babu wanda ya isa shiga tsakanin su sai wanda ya ha'da.

'Karin abin kunya ma yau gashi  dalilin ita Zaitoon din Adam ya samu kamilalliyar matar aure 'yar gidan mutunci da nagarta.
Hakika kowani dan Adam nada tashi kalar tasirin cikin rayuwar kowa.
Matukar mutum ya shigo cikin ka rayuwar ka toh ka mutunta shi, domin Allah shi kadai ne yasan manufar shigo da shi cikin taka rayuwar.

Anyi addu'a sosai da fatan samun zaman lpy ga juna sannan aka mika amarya gidan mijin ta.

Gida kam tabarakalla komai yayi...hadda abinda bai yi bama yayi sbd kyau da tsaruwar sa.

Sauran abubuwan da ba'a kammala gyara mata bane washe gari aka tashi da aikin su nan ma Anty Madeena tayi kane kane ta hana Zaitoon yin komai.

Taso taje taga maman Abdul amma Rayyan yaki bata dama acewar sa babu inda zataje dan yasan aikin kuka kawai zata je tasha abanza.
Kafin la'asar suka fara niyyan komawa.
Domin Rayyan ne zai koma da su, ya kuma fara azazzalan su akan su fito su wuce.

Marwa kuka, Zaitoon kuka, Anty Madeena har haushi suka bata tamkar ta doke su hk taji.. tun tana ban baki da rarrashi har ta fara masifa.
Dama tun agida wajen yiwa Marwa nasiha tafara masifa ganin yadda Marwa ke kuka 'karshe ba ama kammala da ita ba ta fito.

Sanin halin Rayyan da tayi yasa tun ma kafin ta isa wajen Mota ta rage kukan sai dai Marwa kam babu ma alamun zata tsagaita.

Rayyan sau 'daya ya kalli Marwa bai 'karaba sbd wani mugun tausayin ta daya fizge shi.
Abinda yayi niyyan fada mata ma kasawa yayi.
Sai dai kukan nata ya mugun tsaya masa arai sosai.
Shi dai ga Ubangiji ya dam'ka ta, amanar ta ya bawa Allah sannan Adam, yasan duk abinda zai same ta sai in Allah yaso, so babu wani mahalukin da zai iya cutar masa da yar uwa face da yardar ubangiji...dan haka yana mata fatan dacewa, yana mata fatan alkhairi, fatan zaman lpy da kwanciyar hankali, fatan wannan auren ya kasance mata yanki na jin dadin rayuwar ta ya kuma sada ta da aljannar sa ma'daukakiya.

Tunda suka 'dauki hanya babu wanda yace komai acikin su.
Hatta da Anty Madeena ma shiru ba ta furta komai ba, Zaitoon ajiyan zuciya kawai take saukewa, yayin da Anty Madeena ke sauke gauron numfashi.

Zaitoon kam tasan ba 'karamin kewar Marwa zatayi ba, domin tun ranar da Allah ya ha'da fuskokin su basu sake rayuwa a mabanbantan waje ba har sai da ta tafi garin su sannan...a koda yaushe suna tare da juna...suyi shawara tare, suyi sirrin su tare, suyi fada su kuma yi dadi.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 03 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now