P64

100 12 6
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
*Serlmerh-md*

🅿️ *...64*

                .......Duk wannan bidiri kuwa da akayi ba'a kawowa Zaitoon yarinyar ta ba dan Anty Madeena cewa tayi sai sun gama bincike tukunna.

Dole Zaitoon ta ke 'dan ya'ke bata bayyana damuwar ta sosai kan rashin Mufeen kusa da ita sai dai in sun ke6e da Marwa ta kan 'dan jajanta tayi tayi da Marwa suje gidan Anty ko gano yarinyar ne ma tayi amma Marwa sam taki, amma Ammi tuni ta gano damuwar da take faman 6oyewa.

Ayyukan da suka sha kanta ne a 6angaren Amrah ya sanya ko zama bata fiya yi sosai ba balle su tattauna da Ammi.

'Bangaren babu kowa sai ita ka'dai, Rayyan office Amrah kuwa na 'daki da jaririn ta,
wankin kayan yaron da ta tattaro bayan sun bushe ta ninke ta shigo da shi 6angaren Amran sai dai kafin shigar ta ta fara jiyo tashin hayaniya, idan kunnuwan ta basu yi mata 'karya ba kuwa sautin muryar Sultan ne..." Har kin isa ki mumafurce ni Amrah, ta ya ma zaki haifi 'dan da kika san nawa ne bana Rayyan ba salon kowa yasan sirrina dake 6oye ko me..ki fayda min manufar ki kan hakan..."
Ya 'karasa tsawace.
Cikin kwantar da murya Amrah tace
" Toh kai ban da abinka Sulty taya zan san cikin naka ne ko nashi? tunda ba ke6e lokacin tarayya da ku duk biyun nayi ba, dan na fita da kai bani da hujjar da zan hana shi hakkin sa idan ya bu'kata, toh in hakane kuwa taya zan iya bambance lokacin da nasamu cikin da kuma mamallakin sa? kaga dan Allah ka daina min ihu aka, ka barni ma da damuwar da nake ciki, kullum cikin fargaba nake kwana nk kuma tashi tsorona in aka gano wannan dan bana Rayyan bane nasan na ka'de ne har ganye na aure na da kyar ne ya cigaba da wanzuwa dan.nasan halin Rayyan sannan Daddy na kashe ni zai yi...kai kuma fa, iyaka Rayyan yayi fushi da kaine kuma nasan zai sakko da zarar ka bashi ha'kuri kace masa sharrin shai'dan ne ko Ammi bana tunanin zata iya juya ma baya balle matar ka, yanzu waye kk ganin zai fi cutuwa tsakanin ni da kai? har gara kaima damuwar ka ka'dan ce wlh..bazaka ta6a fahimtar halin da nake ciki ba a yanzu..."
" Ke ba dogon sharhi nazo ji a wajen ki ba, nazo ne in shaida miki cewar ba fa zan iya 'kyale yaron nan ya cigaba da rayuwa ba, ina son abuna amma rufuwar sirrina ya fiye min komai...dole ne a salwantar da rayuwar sa indai kina son zaman lafia..."

Tsaye Amrah ta mi'ke tace"  wannan ne kuma baka isa ba Sultan...duk yadda nake jina cikin damuwa amma wallahi ina 'kaunar yaro na, shin ka tayani rainon cikin sa ne ko kuwa kaine kai min na'kudar haihuwar sa, kasan irin wahalar da nasha taya za'ai kace wani a salwantar da shi ka sani ko har abada babu me ganewa hk kawai ka raba ni da yarona a banza...a a wlh...wa ma ya sani ko shi kadai ne haihuwar da zanyi a dunia..."

" Zamu gani ai...".
Ya fa'da gami da juyawa.
Amrah tace " 'Dan Halak ka fasa..".

Zaitoon ma saurin juyawa tayi ta 6uya abayan pillar dinning zuciyar ta na harbawa.
Ban da salallami babu abinda take.
In dai abinda kunnuwan ta suka jiye mata dai- dai ne kenan Muhammad Arfan ba 'dan Rayyan bane na Sultan ne.

Amma abinda ta kasa fahimta shine shin Amrah da auren nata take ke6ewa da wani mijin ko kuwa ya lamari ya kene...Yah ilahi.

Ashe idanun ta ba 'karya sukai mata ba da suke hango kamannin Sultan tattare da jaririn.

Fata take abinda taji ya kasance mafarki ne ba gaskia ba...dan babu wanda zai ji wannan batu batare da girgiza ba.

Babu wanda yasan taji hatta Marwa kuwa, dan cikin ranta ta ri'ke shi tana fatan ya kasance ba gaskiya bane.

Tausayin Ammi take ji sosai, yadda take so da 'kaunar yaron nan, take kaffa- kaffa da shi ya zata ji duk ranar da ta san cewa ba jinin Rayyan 'din ta bane...tasan sai tafi kowa shiga tashin hankali.

Yah Rabb Rayyan fa, ya zaiji idan zamcen ya riske shi, tsananin tausayin su take ji matu'ka.

Anty Raihana ma fa sai shekaran jiya ta koma tun bayan haihuwa da tazo, kuma ta fahimci irin 'kauna da suke nuna wa yaron ko kuka sun tsani suji yana yi.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now