P96

188 17 16
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...96*

               ........" Kin kasance jigon mafarki na Zaitoon cikin kowani baccina da zanyi..muradi na, duk wani buri na rayuwa ta kece Zaitoon, tsarukan rayuwata duk da ke nake tsara shi, ban ta6a ji ko a hasashe cewar baza ki zam tawa ba shiyasa a kullum fatana shine ki kasance tare da ni ki zam mallaki na har 'karshen rayuwa ta, ki fahimce ni pls kinji kuma ki sassauta min halin da nk ciki ta hanyar mallaka min jikin ki ko da na rana guda ne Zaitoon kinji...dan...Allah..hakan ka'dai ne zai iya rage min ra'da'din 'kaunar ki da ke cin zucia ta ko wani lkc".
Ya 'karashe maganar a rarrabe sakamakon 'ko'karin dawo da fuskar sa saitin tata da yake yi.

Wannan karon wani 'karfi ne taji yazo mata tuno wani abu da tayi daga cikin zuciyar ta...zancen su da Amra..ta kuma tuno Arfan...ta riga tasan komai dake tsakanin su ta kuma jima da fahimtar manufar sa akanta.

Amma sam, ko cikin mafarki bata ta6a tunanin faruwar wannan 'kazamin al'amarin a tsakanin ta da shi ba.

Angije shi tayi da iya 'karfin ta, Allah sai ya 'kara bata sa'a ya 'dan ja baya ka'dan tamkar mara laka a jiki, duk da yake bata isa ta ha'de 'karfin ta da nashi ba amma bata san ina 'karfin jikin sa ya tafi a wannan lkcn ba da har ta samu nasarar ture shi.

Saurin juya mata baya yayi yana mai cusa hannu cikin gashin kansa yayin da 'daya hannun dake ri'ke da hular sa ya kama 'kugun sa da shi, tamkar wanda ya farko daga wani dogon nazarin da bai shirya shigan sa ba amma da alamu ya shiga damuwa ne 'yar ka'dan...Sosai idanun Zaituna ya rufe cike da 'dacin rai take shirin duban sa bayan ta kara ja da baya daga inda yake...kafin ta ankara da wanzuwar wani a wajen sai jin _Tasssss_ .....tayi, sau'kan wani lafiyayyen marin da ita kanta sai da ya sake hargitsa mata lissafi duk da cewa ba'a fuskar ta marin ya sau'ka ba.

Kafin tayi wani yun'kuri ko fahimtar takamamme abinda ke faruwa sai gani tayi ya sake sau'ke wata dun'kulalliyar naushi saman fuskar Sultan dake yi masa duban firgici, take kuwa jini ya fara zuba ta baki da hancin sa.

Sam ma bata lura da cewa da hannun sa mai ciwon ya kai naushin ba sai da ta isa kusa da shi a 'dari a kuma firgice tana me 'ko'karin ri'ke hannun sa da ya sake dun'kulewa da niyyar kai wani naushin sai kuwa ya hanka'de ta baya..'dan 'karamin ihu ta sanya me cike da zogin buguwa da tayi da bango...sai dai hakan bai hana ta shiga tunanin yaushe hannun san yy lafiyar da har ya iya kai duka da shi har haka ba.

Madadin ta tsaya bibiyar zafin buguwan da tayi sai ta tsaya yi masa kallon mamaki.

Shi kam Rayyan shaf ma mancewa yy da batun ciwon hannu, ashe wargi ma waje yake samu..6acin rai ko firgici babu irin abinda baya iya haifarwa na daga sabbin yanayi.

Ganin yana neman yin kisa ne yasa Zaitoon dawowa hayyacin ta take ta saki wani ihu da 'karfi tana mai 'kiran sunan sa da kalmar ban hakuri amma ko gezau, tamkar kurma, tamkar namijin zakin da yunwa ta riga ta ciyo shi baya jin 'kira sam, baya jin ban hakuri balle ya sarara ga abinda yk niyyar aikatawa...bugun Sultan yake tamkar Allah ne ya aiko shi.

Ihun nata bb inda be ratsa cikin gidan ba hatta da su Ammi sai da suka jiyo ta amma shi tamkar itace, tamkar bai san tana yi ba.

Da gudu su Ammi suka yo 6angaren nasa batare da tsayawa kokonton daga inda ihun ke fitowa ko kuma ma'kasudin fitan sa ba.

Kuka sosai Zaitoon take yi ganin yadda Rayyan ke ta jibgar 'dan uwan sa tamkar ya mance matsayin da yake da shi agare shi, jini ke fita ta hanci da bakin Sultan kuma duk ya 6ata masa fuska da jikin rigar sa amma hakan bai sa Rayyan ya sarara masa ba.

Tuno Ammi yasa ta juya da gudu tayi hanyar waje dan neman agaji daga gareta nan suka yi karo da ita batare ma da dukkan su sun kula da tahowar juna ba.

'Kasa Zaitoon ta fa'di bisa gwiwoyin ra sakamakon ha'duwar bazata da suka yi.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now