P8

81 9 2
                                    

💕 *BINTEE* 💕
      *(' Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️ *...8*

        Sai da ta taso wajen aikin a hanyar ta na zuwa gida ne maganganun Bbn Abdul suka fara dawo mata 'daya bayan 'daya, sai a lokacin kuma ta fara jin tashin hankali na shigan ta na gaske.
Da yace zasu karasa maganar a ina kenan yake nufi?.
Kuma da wani lokaci?.

Lokaci guda Bbn Abdul yasa taji zaman gidan nasu gaba daya ya fice mata aka, kudin shekara ta biya amma bata jin zata iya cike shekaran a gidan matukar Bbn Abdul bazai bar shiga sabgar ta ba.

  Da komawar ta gida ta shiga lalu6o 'yan kudaden da take tarawa a hankali, wasu daga cikin kudin hakkin ta ne na wajen aikin yayin da wasu Adam ke bata lokaci zuwa lokaci, ko da ta irga sai taga sun kai kimanin Naira dubu goma sha shida cif.

Tunani ta fara na inda zata samu daki koda kudin rabin shekara ne ta biya a hnkl sai ta bada sauran daga baya.
Toh a ina zata samu? Ta tambayi kanta.
Ko de Adam zata yiwa magana ya bincika mata.

Sai dai fa shima Adam din yanzu haduwar su ta kan dan yi wahala sakamakon aikin matsa mai da ya samu a wata Filling Station.

Karshe da ta kewaya kuma dai kan Adam din tunanin ta ya tsaya, dole sai shi zata yiwa maganar tunda shi kadai ne me iya zama ya saurari kukan ta.

Murmushi tayi kayatacce lokacin da take gyara musu shimfida bisa sabuwar katifar su da dududu bata wuce sati uku da siyan ta ba.

Mufee dake a goye a bayan ta wacce tuni tai bacci ta kwanto ta shimfidar da ita bisa katifar.
Dan yanzu tana 'dan barin ta kwanta ba'a jikin ta ba saboda samuwar katifar Mufeedan ce ma bata saba da kwanciya ita kadai ba dole ko da tayi bacci sai ta farka cikin dare in dai ba'a jikin Zaitun tayi bacci ba dole dai karshe akan cikin zata dora ta su karasa baccin.

A hankali ta fara tariyo yadda aka yi kafin siyan katifar wani lokaci da ciwon mura yai wa Mufee kamun karfi...abin ya damu Zaitun sosai dan hatta itama a lokacin lafiyar bata ishe ta ba amma na Mufeedan yafi tsaya mata a rai fiye da komai.

Ko da Adam yake tambayar ta garin yaya duk suka kamu lokaci guda haka ai bata ma san lokacin da tace" Ina ga sanyin siminti ne fa Yah Adam Allah kar kaga yadda kullun dare atishawa ke hana ta sakewa a hakan ma saman ciki na nake kwantar da ita da kullun"
" Babu gado ne ko irin katifa haka..?"
Da kai ta bashi amsa gami da fadin" a a tabarma ce kawai shiyasa.."
Adam bai sake yin magana akan hakan ba bayan kwana biyu kawai taga katifa ya kawo.
Da ta rasa bakin yi mai godiya sai kawai ta fara hawaye" Dan Allah Yah Adam ka daina wahal da kanka saboda mu..ni fa ban fada dan wani dalili ba a lokacin rikicewa nayi..dan Allah ka koma da shi sai inga kamar bana maka adalci duba da yadda na dora maka nawin abubuwa da dama da ba hakki ne akan ka ba..."
" Zaitun kenan.."
Ya fada yana me zuba hannayen sa cikin aljihun wandon jumpan da ke jikin sa.
"..in ban yi muku ba toh ma wa zan yiwa?...daga Hajiya ta sai ku kadai gare ni fa a yanzu, ba dole in kula da duk wata damuwar ku ba in dai ina da damar hakan..."
"Yah Adam..."
" Ni dai kinga tafiya ta idan kin ga dama ki kyasta ashana ki 'kona ko kuma ki qi kwanciya akai saboda ni ne na kawo.."
Daga haka yayi gaba abin sa bai ko sake waigowa ba.
" Wannan bawan Allah akwai tausayi, Ubangiji Allah ya saka maka da mafificin alkhairi ya kuma kara arziki"
Addu'ar da kullun take yiwa Adam din kenan ko gaban sa ko a bayan idanun sa ne.

Tunowa da tayi a safiyar yau din kamar da 6acin rai suka rabu ya sanya ta kara jin zafin Bbn Abdul har cikin zuciyar ta.
In dama ta gode Allah har dare yayi sukai shirin bacci bata ji ko duriyar sa ba.

Har ta fara karanto musu Addu'an bacci sai kuma taji fitsarin da tasan matukar bata yi shi ba sai ya tada ita cikin dare.

Dole ta tashi ta fita fitsarin wanda a lokacin gari yayi duhu sosai kuma babu wuta an dauke.
 
Bbn Abdul da shigowar sa gidan kenan wajen karfe goma saura har zai gitta dakin Zaitun sai kuma yaga kamar bude yake hakan yasa batare da tunanin komai ba kawai ya afka dakin duk da takalmin sa bai cire ba gudun kar Hajja ko Mmn Abdul su gani, zuciyar sa cike fal da farin ciki da tunanin bacci ne ya dauke Zaitun har ta manta bata rufe kofar tata ba.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now