P91

105 17 9
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...91*

               .......Wani tu'kukin takaici ne yaji ya ziyarce zuciyar shi a lkc guda..da irr-iren wadan nan mutanen kewaye da su ma ta ya ze iya barin Zaituna zama da yarinyar nan...?
ya tambayi kansa.

Da gangan sai ya'ki matsawa daga bakin 'kofar har suka gama gaisawa da shi..." Masu jegon na ciki?"
'Daya daga cikin matan ta tambaya cike da azar6a6i.

" A a bacci suke yi".
Shine amsar da ya basu da yana mai banka musu wata muguwar harara da 'kasa-'kasa.

" Aww to amma ai za'a iya ganin 'diyar ko?"
" Bata da ishasshiyar lafiya an kuma hana jagwalgwala ta".
Amsar da ya basu kenan a tsare ya kuma kawar da kansa gefe sam bayi da niyyan matsawa daga 'kofar.

Haka badan sun so ba suka yi waje suna mita 'kasa 'kasa wai irin wannan abin, dan ma 'yar gaba da fatiha ce, ake wani 'da'd'daurewa ana 'kafafa, waye uban sai Allah?"

Shi kam kasa barin gidan yayi saboda takaici...ya 'dauki a 'kalla tsawon mintina sama da talatin tsaye a wurin kafin ya fara yun'kurin sanya takalman sa..ni kam tuntuni bacci yy gaba da ni, baccin da ban samu yin sa da kyau tsakanin kwanakin ba..musamman ma daren jiya da zazzafan ciwon da kai ya taso ni gaba.

Har ya kusa barin gidan sai Abban mu ya fito daga 'dakin sa, nan ya zauna bisa kujerar sa da yake zama irin ta dattawa...yayin da Hamma ya isa ya tsugunna gaban sa daga 'kasa kan 'kafafuwan sa...
" Abbah barka da yamma, fatan ansha ruwa lpy ..?"
" Kira min Zaituna".
Abbahn mu ya fa'da batare da ya bi ta kan gaisuwar Hamman ba.

Hamma Bukar ne yaje ya tashe ni daga baccin da nake muka fito tare da shi..jiri sosai nake yake shirin  'diba na saboda zafin ciwon kai 'din da nake son takurani.

Amma ganin inda Hamma ya tunkara wato wajen Abban mu da ko alamun fara'a babu saman fuskar sa yasa take na nemi ciwon na rasa har na isa gaban sa nima nayi zaman dirshan zucia ta na harbawa da 'karfin da bana jin na ta6a fuskantar irinta.

Lokacin da kunnuwa na suka jiye min kalamin mahaifi na agare ni ba ciwon kai ba natsuwa ta ma gaba 'daya rasa ta nayi na fara rarraba idanu.

Addu'a nk Allah yasa ba dai-dai kunnuwa na suka jiye min ba, Allah yasa ba Abbah na bane ya furta.

Amma duk yadda naso 'karya sautin muryar ban samu canji ko guda ba..abin nan dai da najin shi yace..wanda tashin farko na fahimci cewa yana tafiya ne bisa ra'ayin matar sa Iyani.

" Mahaifiyar ku tace bazata zauna da shege a gida ba, dan haka kafin yamma bana so in dawo in same ki cikin gidana..ki tattara ki san inda zaki saka wannan abin kunyar da kk kwaso ko kuma ki kaiwa ubanta ya ri'ke abinsa tunda na tabbata kinsan waye ubanta, ni ke ka'dai na haifa ban kuma haifi shege ba balle in raini na wasu, dan haka baza'a tayar min da hankalin gida ina zaman zama na ba..".

Hamma Bukar shiru yayi yana tunanin ta inda zai 6ullowa lamarin.
Ni kuwa kuka ne kawai ya 'kwace min bayan tabbatar da cewa mahaifi na da gaske yake...ina girgiza kaina nake fa'din" Abban mu wallahi ni bani na haifi yarinyar ba, kuma ina zan ga ubanta balle in sanshi har in bashi 'diyar shi, Abbah uwar ce fa kawai muka ha'du da ita kuma bata yi min bayani cikakke kan asalin su ba, dan Allah Abbah kayi min rai kar ka kore ni da 'yar yarinyar nan, idan ka kore ni ina zan saka rayuwa ta..wallahi Abbah ka tambayi Hamma Bukar kaji.. shi ya sani ba nice na haifi yarinyar nan ba Abbah..dan Allah kayi ha'kuri..."
Na 'karashe ina mai komawa bisa gwiwoyi na.

Kafin Abbah ko Hamma 'dayan su yayi magana sai ji muka yi Iyami na tafa hannuwa tana fa'din
"...wallahi Zaituna bazaki zauna min agida da ''diyar shege ba, ban gaji hakan ba dan haka bazan zauna gida 'daya da mai shi a gur6ata min zuri'ah ba, kina nan kullum 'kunsun-'kunsun cikin hijabi ashe na munafurci ne sai ga sakamakon hijabin ya bayyana 'karara...kima san yadda zakiyi tun wuri da shegen abin nan matu'kar kina son zama agidan nan sa6anin hakan kuwa wallahi terere zan cigaba da yi miki kowa sai yaji me kika aikata da kuma sakamakon da kk samo, kema da kanki kin san sauran kin kuma san iya fin hakan ma..."

BINTEEE ( 'Yata ce)Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ